Min menu

Pages

Menene makomar Sakamakon mukabalar kano?



Bayan tsawon lokaci da aka dauka ana jiran ranar da za'ayi mukabala tsakanin shehun malamin darikar kadiriyyar nan Sheik Abduljabbar Nasiru kabara da malaman jahar kano domin karyata shi tare dayi masa yar kure akan irin wa'azuzzukan dayake Wanda malaman suka kira da ciwa addini dunduniya tare da bata sahabbai.

A jiya ne dai kowa yake saka ran wannan mukabala amma shiru kake ji ko me yasa?

Bayan diga alamar tambaya akan sakamakon wannan mukabala, an sami wani gidan rediyo ta kafar yada zumunta mai suna Qibla FM yana bayyana zumudinsa na jiran lokacin wannan mukabala domin a zubar da ita a faifayi tsakanin malamin da malaman da suke ganin ya kaucewa hanya. Amma maimakon haka sai suka kare da samun labarin nokewar wadannan malamai akan dalilan da basu da asali bayan kuma da dama daga cikinsu ansha ji suna cewa irin wannan rana sukeso tazo a zubar da ita a kasa.

Abduljabbar a wata shira da yayi yace shi ya riga daya shirya tsaf yana jiran ranar ne, to amma sai abu ya sauya maimakon mukabalar sai janyewa, to hakan mai yake nufi idan har ba'a gabatar da wannan mukabala ba?

Abu na farko dai shine duniya zata dauka cewa Abduljabbar shine akan gaskiya, idan kuma hakane to ya zama wajibi ga dukkan musulmai a jihar kano su koma kan tafarkin koyarwarsa tunda ba'a sami mai ja dashi ba.

Har yanzu dai ba'aji wani furuci ba ta bangaren gwamnati dangane da wannan al'amari shin zata cirewa Abduljabbar ne takumkumin data saka masa ko kuma wani matakin zata dauka. Sannan ta bangaren malamin wane mataki zai dauka akan wannnan al'amari.

Malamin dai a kwanakin baya gwamnatin kano ta dakatar dashi daga yin wa'azi tare da rufe makarantarsa dayake koyar da karatu akan zarginsa da wa'azi Wanda keda alaka da tada fitina, malamin mutane da dama sunsha zarginsa yanayin karatuttuka Wanda bayayiwa yawancin musulmai dadi. Bayan rufe makarantarsa da hana shi wa'azi da akayi yace ba'a masa adalci ba idan ba'a bashi dama ya kare kansa ba, ya zargi gwamnati da kokarin tauye masa hakki, haka kuma Malamin yace dakatar dashi daga yin wa'azi ba komai bane face bashi dama da akayi ya sami lokaci yayi ta rubutu irin Wanda bazaiwa malamai masu ja da maganganunsa dadi ba, inda a cikin maganarsa yake cewa: inawa maluman nan bakin albishir dasu saurareni zanyi ta fitar rubututtukan da bazai musu dadi ba har sai sun rasa inda zasu saka Kansu. 


A bayan wannan ne dai gwamnatin kano ta fitar da lokacin da zata hada mukabala tsakanin Abduljabbar da malamai dabam dabam daga ko wane bangare domin tabbatar wa da malamin kuskurensa ta fuskar ilimi.

Kungiyar izala wanda ta dade tana gogawa da malamin sunyi matukar farin ciki da wannan hukunci da gwamnatin kano ta zartar saboda sun dade dama suna zargin malamin dayin batanci ga sahabbai masu daraja a cikin wa'azin dayake gudanarwa.

 

A yanzu dai haka an baiwa malamai dama dasu je su shirya domin wannan mukabala.

Comments