Min menu

Pages

Awanni arba'in da hudu na baku ku karbo garin marte daga hannun yan boko haram inji shugaban sojojin Attahiru

 Awanni arba'in da hudu na baku ku karbo garin marte daga hannun yan boko haram inji shugaban sojojin Attahiru.Attahiru shugaban sojojin kasa ya baiwa rundunar operation lafiya dole umarni akan su karbo garin marte da yan boko haram suka kwace cikin awowi arba'in da hudu.


Yan boko haram din sun kwace garin na Marte ne tun ranar juma'a wanda har yanzu yake a hannunsu.


Sannan kuma shugaban sojojin ya umarci sojojin dasu tabbatar an samu zaman lafiya a garin kuma tsaro ya samu sauran garuruwan da suke makota da garin.


Shugaban sojin attahiru shine shugaban sojojin da aka nada yan kwanaki kadan bayan an sallami sauran.


Kuma yayi alkawarin zai tsaya kaida fata ganin sunyi yaki bakin kokarinsu da duk masu tada hankalin al'umma dake fadin kasar.

Comments