Min menu

Pages

Kungiyar Izalah tayi saurin amincewa da muqabular da aka shirya a kano tsakanin malamai

 Kungiyar Izalah tayi saurin amincewa da muqabular da aka shirya a kano tsakanin malamaiShugaban kungiyar Malam Abdullahi Bala lau ne ya sanar da hakan a wani zama da yayi a jihar kaduna yayin tattaunarsu da manema labarai.

Ya kara da cewa hakika mun nuna matukar goyon bayan mu game da wannan dokar da gwamnatin kano ta fitar domin dakile wannan fitinar da Abduljabar yake haddasawa, sannan malamin ya yaba wannan muqabular da aka shirya a tsakanin Abduljabar din da malaman Kano.

Sannan malamin ya yaba tare da jinjinawa gwamnatin kano bisa wannan matakin data dauka domin zai kawo karshen yaduwar irin wannan abubuwan da suke faruwa na cin zarafin musulunci.

Har yace irin wannnan matakin ita gwamnatin jihar Neja ta dau lokacin da wani ya fito yana maganganu marasa kyau akan sahabban manzon Allah inda aka dauki matakin daya dace akansa.

Duniyar labari


Comments