Min menu

Pages

Hankalin malaman kano ya kwanta gaskiya ta fito akan BATUN mukabala

  Hankalin malaman kano ya kwanta gaskiya ta fito akan BATUN mukabala



Bayan yada jita-jita da akayi tayi dangane da mukabalar da gwamnatin jahar Kano tace zata shirya tsakanin sheikh Abduljabbar da malamai akan zarginsa da akayi wajen ciwa addinin musulunci dunduniya a karatuttukansa.


A baya gwamnatin kano ta shirya wani kwamati Wanda zasu tsara yanda za'a gabatar da mukabalar, to sai kuma kafin wannan kwamati suce wani abu kafafen sada zuminta suka dauki yamudidin cewa malaman da aka shirya makabalar dasu ne suka zulle. 


Ana cikin haka kuma aka sami labarin BBC Hausa sun rawaito cewa kwamatin sun mika sakamakon yadda za'a gudanar da wannan mukabala zuwa ga gwamnan jahar kano, harma suka ce haryanzu ba'a fitar da ranar mukabalar ba Wanda hakan yana karyata batun da ake tayi a kafafen yada zumuntar.


Kwamishinan harkokin addini Muhammad Tahir Adam Wanda akafi sani da baba impossible yace cikin rahotan mukabalar da suka gabatar yace sun bukaci gwamnan jahar kano daya hado manyam malaman kasar nan da ake dasu na kowane bangaren kama daga Kadiriyya,Tijjaniyya, da Izala tare kuma da wakilci daga sarkin musulmi

Malamin dai a kwanakin baya gwamnatin kano ta dakatar dashi daga yin wa'azi tare da rufe makarantarsa dayake koyar da karatu akan zarginsa da wa'azi Wanda keda alaka da tada fitina, malamin mutane da dama sunsha zarginsa yanayin karatuttuka Wanda bayayiwa yawancin musulmai dadi. Bayan rufe makarantarsa da hana shi wa'azi da akayi yace ba'a masa adalci ba idan ba'a bashi dama ya kare kansa ba, ya zargi gwamnati da kokarin tauye masa hakki, haka kuma Malamin yace dakatar dashi daga yin wa'azi ba komai bane face bashi dama da akayi ya sami lokaci yayi ta rubutu irin Wanda bazaiwa malamai masu ja da maganganunsa dadi ba, inda a cikin maganarsa yake cewa: inawa maluman nan bakin albishir dasu saurareni zanyi ta fitar rubututtukan da bazai musu dadi ba har sai sun rasa inda zasu saka Kansu. 

A bayan wannan ne dai gwamnatin kano ta fitar da cewa zata fitar da lokacin da zata hada mukabala tsakanin Abduljabbar da malamai dabam dabam daga ko wane bangare domin tabbatar wa da malamin kuskurensa ta fuskar ilimi.

Kungiyar izala wanda ta dade tana gogawa da malamin sunyi matukar farin ciki da wannan hukunci da gwamnatin kano ta zartar saboda sun dade dama suna zargin malamin dayin batanci ga sahabbai masu daraja a cikin wa'azin dayake gudanarwa. A yanzu dai haka an baiwa malamai dama dasu je su shirya domin wannan mukabala.

Comments