Min menu

Pages

Baza mu biya kudin fansar daliban makarantar kagara ba inji gwamnatin tarayya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tace bazata biya kudin fansar daliban makarantar kagara ba.



An sami labarin gwamnatin tarayyar Najeriya tace bazata biya kudin fansa ba domin ceton daliban makarantar kwalejin kimiyya ta  kagàra dake jihar Neja da aka sace.


Wannan bayani ya fita ta bakin Ministan Buhari Lai Muhammad inda yace kada wadanda sukayi garkuwa da daliban makarantar kagara suyi tunanin samun kudin fansa daga gwamnati, ya kara da cewa masu aikata laifin nayin amfani da tunanin mutane ne kawai domin su rinka samun kudade.


A bayanin da lai Muhammad yayi yace zasu bi dukkanin hanyoyin da suka dace domin ceto daliban amma bada kudin fansa ba, ya kuma bayyana cewa ko a lokacin da aka sace daliban kankara a jihar katsina dana dapchi a jihar yobe babu wani kudin fansa da gwamnati ta bayar domin ceto su daga hannun masu laifin.


Dayake cigaba da bayaninsa yace yan fashi da gangan sukafi kama mata da kananan yara domin su janyo hakalin duniya a biya musu bukatunsu cikin gaggawa ya bayyana hakan a matsayin amfani da ilimin sanin halin mutane.


A kwanan nan ne dai aka sami wasu yan fashin daji suka shiga makarantar kwalejin kimiyya ta kagara a jihar Neja suka sace dalibai sukayi garkuwa dasu. Wannan abu ya jawo cece kuce da dama daga bangarorin dabam dabam na kasar nan ganin cewa kwana-kwanan nan aka sauya jagororin tsaro na soji baki daya a Najeriya tare da fatan ganin cewa sauyin ya kawo canji mai amfani, amma kuma maimakon haka mutane dayawa suna ganin a bangaren tsaron jiya iyau maimakon sauyi sai matsalar da ake ciki take ci gaba da faruwa. 


Al'amari na sace mutane a karbi kudin fansa a Najeriya ya zama ruwan dare ana tayinsa babu kakkautawa, hakan kuma ya zama wata muguwar barazana ta fuskar tsaro da kwanciyar hankalin al'umma.

Comments