Min menu

Pages

Kuyi gaggawar hana kiristico kona masallatai sakon shugaban kungiyar izala Sheikh Bala Lau ga jami'an tsaro

 Kuyi gaggawar hana kiristoti kona masallatai sakon shugaban kungiyar izala Sheikh Bala Lau ga jami'an tsaroShugaban kungiyar Izala ta kasa sheikh Abdullahi Bala Lau yayi kira ga jami'an tsaro cewar suyi gaggawar hana kiristico kona dukiyoyin al'umma da kuma masallatan musulmai dake garin Billiri na jihar Gombe.


Malamin yace yace abin babu dadi kuma akwai takaici akan nada sabon sarki wanda bama akai ga fada ba ko kuma bayyanawa ba amma kiristoti su fito suna kona masallatai da dukiyoyinsu a garin Billiri.


Har malamin yace koda tarihi za abi sarautar billiri dama can a hannun musulmi take kuma suke juyata ba tare da zaluntar kiristico ba sai a shekarar dubu biyu da sha daya lokacin mulkin marigayi habu hashidu bayan mutuwar sarkin musulmi to a lokacin ne aka nada musu sarki kirista.


A wancan lokacin dole musulmi suka hakura, sai yanzu da ake hasashen za a nada musulmi shine za suzo suna tada hankali harda kone masallatai.


Sheik Abdullahi Bala lau yayi kira da gwamnatin jihar Gombe data dada bada kaimi wajen ganin an shawo kan wannan matsalar data kunno kai cikin garin na Billiri.


Sannan ya yabawa gwamnatin bisa maganar da tayi cewar zata zuba ido ganin an kamo mutanen da sukayi wannan aikin.

Daga karshe malamin yayi addu'ar zaman lafiya ga kasar dama duniya baki daya.

Comments