Min menu

Pages

Yanzu sojoji suka kwace gonar shekau dake cikin dajin sambisa

 Yanzu sojoji suka kwace gonar shekau dake cikin dajin sambisa.A yaune jami'an tsaro ko kuma nace sojojin Najeriya suka samu damar kwace wata gona dake cikin dajin sambisa wacce mallaki ce ga shugaban boko haram.


Tun ba yau ba sojojin suke cikin dajin na sambisa suna neman shugaban yan boko haram din.


To saidai rohoton da muke samu yanzu yanzun nan ance sojojin sunyi nasarar dira a gonar tasa saidai basu same shi ba.

Amma dai mutane na nata cewa duk wannan ma cikin nasara take ga sojojin domin suna tsammata musu wata rana zasu iya kama shugaban yan boko haram din a cewar mutanen.


Tun jimawa dai yan boko haram din suka addabi al'umma wanda hakan yasa mutane da dama dake yankunan da abin ya shafa suke yin shijira su koma wasu garuruwa.


Hakan yasa gwamnati ta bada umarnin sojoji su shiga su yake su, su tabbatar zaman lafiya ya samu.


To saidai har yanzu basu samu damar kamo shugaban yan boko haram din ba.

Comments