Min menu

Pages

Babu tantama Abduljabar yaji haushin hukuncin Ganduje

  Tantama babu Abduljabar yaji haushin Ganduje Sheikh Abduljabbar ya matukar ji haushin gwamnatin jihar kano bisa dakatar dashi da tayi tare da rufe masallacin sa.


A wata shira mai tsawon minti hudu da akayi da Malamin nan na Kadiriyya Abduljabbar a sashen Hausa na BBC malamin yace gwamnatin kano da kanta tasan zalunci ne abin da akeyi masa.


A cikin zancensa ya kuma cewa ya kamata jama'a su karkade katinan zabensu saura shekara biyu a sauya gwamnatin da zatayi adalci a kano azzalumai su kuma zasu dandana kudarsu, alokaci guda kuma malamin ya zargi gwamnatin kanon da hada baki da wasu malumai magautansa domin a bata masa suna wajen ciro magana ta sakanni kalilan cikin wa'azinsa na awa biyu su kafa Hujja dasu.


Bayan Wannan a cikin shirar tasa yace duk wani malami dayake tunanin abin dayake fada ba gaskiya bane ya tareshi suyi mukabala.


Malamin dai a kwanan nan gwamnatin kano ta dakatar dashi daga yin wa'azi tare da rufe makarantarsa dayake koyar da karatu akan zarginsa da wa'azi wanda keda alaka da tada fitina.


 Malamin mutane da dama sunsha zarginsa yanayin karatuttuka Wanda bayayiwa yawancin musulmai dadi. 


Bayan rufe makarantarsa da hana shi wa'azi da akayi yace ba'a masa adalci ba idan ba'a bashi dama ya kare kansa ba, ya zargi gwamnati da kokarin tauye masa hakki, haka kuma malamin yace dakatar dashi daga yin wa'azi ba komai bane face bashi dama da akayi ya sami lokaci yayi ta rubutu irin wanda bazaiwa malamai masu ja da maganganunsa dadi ba.


Inda a cikin maganarsa yake cewa: inawa maluman nan bakin albishir dasu saurareni zanyi ta fitar rubututtukan da bazai musu dadi ba har sai sun rasa inda zasu saka Kansu. 


A yanzu dai haka gwamnatin kano ta fitar da lokacin da zata hada mukabala tsakanin Abduljabbar da malamai dabam dabam daga ko wane bangare domin tabbatar wa da malamin kuskurensa ta fuskar ilimi.


Kungiyar izala wanda ta dade tana gogawa da malamin sunyi matukar farin ciki da wannan hukunci da gwamnatin kano ta zartar saboda sun dade dama suna zargin malamin dayin batanci ga sahabbai masu daraja a cikin wa'azin dayake gudanarwa


 A yanzu dai haka an baiwa malamai dama dasu je su shirya domin wannan mukabala.

Comments