Min menu

Pages

Akan rikicin Oyo Dr Pantami yace yayi magana da gwamna


 A matsayina na dan arewa kuma musulmi nayi magana da gwamnan Jihar Oyo inji malam pantami

Muna jajantawa yan’uwa da suke Jahar Oyo da sauran jihohin kudu, wadanda suka rasa rayukansu Allah ya jikansu, wadanda suka rasa dukiyoyi Allah ya mayarmusu da Alkhairi, wadanda suke cutardawu Allah ya kunyatar dasu. Muna rokon Allah “Alhayyu Al Qayyum” da yako masu Dauki.

Nayi kokarin Kiran Gwamnan jihar Oyo state ban samu damar magana dashiba, Amma na samu magana da Deputy Governor na Garin Oyo, na Nuna masa damuwa da duk kalar rashin jin dadi a matsayina na Dan Nigeria Kuma Dan Arewa Musulmi, ya fadamin matakai da ake dauka Kuma ya bani wasu muhimman information game da Rikicin

Na Kira Gomnan Lagos State (Sanwo Olu) dake shima nasan irin kokarin da yakeyi Akan irin wadannan abubuwa, na Fada masa irin takaicin da Yan Arewa suke ciki

Munyi Exchanging message da gomna Ikiti State akan Rikicin.

Na Kira abokin aikina wato Minister na Yan sanda yake fadamin irin mataki da suke dauka Akan abun, suna waya da Commiisoner of Police na Garin yana bibiyar halin da suke ciki. Kuma yace an kaimusu taimako na Gaggawa ga wadanda suke chan.

Gomnan Lagos State da nake gayamasa har yanxu abun Bai kare ba, na samu wasu Video clips daga wasu Yan uwa matasa yake cewa a tura masa Ya gani.

Shi Kuma Minister na Yan Sanda yace in akwai wasu location da suke da problem a bashi.

Na Kira shugaban Gomnonin Arewa wato Gomnan Plateau akan matsalar a matsayinsa na shugaban Gomnonin Arewa Kuma yan Arewa ake kaiwa hari, wajibine yayi magana akai. Hakuri yanada iyaka idan hakurin mutum ya kare babu dadi.

Wadanda muke shawari dasu akan abun irinsu Prof. Zulum tun jiya muke shawari dasu akan yanda za’a Kai doki da samo solution akan rikicin.

Bama bukatar sai an fito fili ana fadan irin kokarin da muke akan irin wadannan rikicin, yardar Allah muke nema. Allah Yana sheda idan irin wannan matsalar ya taso, Ina waya da akalla mutum 30 da abun ya shafa saboda magance matsalar

Doka ta Nigeria, kowani Dan kasa yana da damar ya zauna a inda yake so ya zauna, idan yayi laifi sai a kaishi kotu a hukuntashi

ubangiji Allah ya kawomana karshensa wannan fitina ya zaunar mana da kasar mu lpya,

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments