Min menu

Pages

Wannan ce kawai hanyar da zaku bi in kuna yin Insme, Uwork da My bonus da Getapp

 Wannan ce kawai hanyar da zaku bi in kuna yin Insme, Uwork da My bonus da GetappWadannan duka wasu hanyoyi ne na samun kudi wanda suka baiyana a yan kwanakin nan wanda mutum zaisa kudinsa yana cirewa kadan kadan harya mayar da kudinsa sannan yaci riba, mutane da yawa sun karbi abin hannu bibbiyu domin sun saka kudaden su da yawa a ciki.

Insme shine wanda ya fara zuwa kuma cikin nasara sai mutane suka karbeshi hannu bibbiyu suka zuba kudi sosai a ciki domin kuwa suna samu.

Uwork shine yazo a bayan Insme, kuma tsarin nasu kusan kamar tare suke tafiya saidai akwai yan bambance bambance amma dai shima din kudinka zaka saka sannan kana cira kadan kadan har kudinka su dawo.

Getapp duk kamarsu daya da sauran hanyar samun kudi ce online amma mai abin mamaki domin yan kudi kalilan zaka saka ka samu mai yawa.

Dalilin da yasa aka bude wannan tsarin

Magana ta gaskiya ba komai bane yasa aka bude wadannan abubuwan ba saidai dan a yaudari mutane ne sannan a guje musu da kudi, domin kuwa babu wanda zaizo yace ka bashi dubu goma kai kuma zai baka dubu ashirin indai ba damfara zai maka ba, amma abin mamaki sai naga kowa sai shiga yake. Hatta yan wasan kwaikwayo sun sanar da irin wannan damfarar ta wani film dinsu mai suna garabasa duk domin su nusar da mutane cewar su guji yadda da wannan tsarin na yan damfara amma mutane basu yadda ba.

Sukai ta shiga harkar tare da tura kudade domin shiga harkar.

Hanyoyin da mutum zaibi idan ya shiga tsarin

Akwai hanyoyin da za kubi idan kun shiga tsarin, hanyoyin ba wasu bane face kuyi saurin cire kudinku da kuka tara a ciki wanda baku cire ba kamar na cikin wallet account dinku na Uwork da Getapp domin insme kam su sun riga sun gudu dan haka saboda tsoron kar suma sauran su gudu muku da kudi to shine kuyi gaggawar cire sauran abinda ya rage.

Sannan in mutum zai shiga ya daina zuba manyan kudade domin gudun irin wannan ranar.

Daga karshe mutane suna hankali tare da taka tsantsan wajen yin duk wasu harkokin kudi na online domin gujewa fadawa tarkon yaudara.

Akwai hanyoyin samun kudi wanda babu yaudara ko cuta a ciki shine kamar youtube channel da kuma website domin sune zakai aiki kuma ka samu kudi a koda yaushe.


Comments