Min menu

Pages

Dalilin da yasa na saida yaron dana haifa dubu goma a ranar dana haife shi inji budurwar

 Dalilin da yasa na saida yaron dana haifa dubu goma a ranar dana haife shi inji budurwar.

Budurwa yar shekara 22 da biyu ta fadi dalilin da yasa ta saida danta data haifa naira dubu goma a ranar data haife shi ga wani pastor, a cikin garin babban birnin na jihar ta Ondo sannan ta fadi dalilin da yasa ta dauki wannan hukuncin ko kuma matakin na saida yaron nata.

Oladayo itace wanda jami'an yankin na amotekum suka kama da laifin saida danta da tayi.

Ba tare da fargabar komai ba tace hakika ita ta saida dan nata da kanta tunda tun ranar data samu cikinsa mahaifinsa ya tafi ya barta.

Taci gaba da cewa saida na yanke masa cibiya tunda na haifeshi a tunanina zai mutu amma bai mutu ba daga karshe kawai na yanke shawarar na saidashi, shine na kaiwa pastor ya bani dubu goma tunda bai mutu ba.

Kuma inada tabbacin pastor din zai bani dana koda wata rana cewar budurwar ga yan ametokum din da suka kamata.


Matar taci gaba da cewa hakika nice na saida dana domin koda na barshi bazan iya daukar nauyin ciyar dashi ba, hakan yasa nace da faston ya dauke shi yaje ni kuma ya ban dubu goma.

Pastor din daya sayi yaron sai yace, nidai ina zaune saiga dan uwan matar yazo gareni yace nazo gidansu wata ta haihu kuma na sani sabuwar haihuwa ana bukatar addu'a daga gare mu.

Tun lokacinda nai mata addu'a a kwanakin baya lokacin cikin nata bai girma sosai ba tun daga lokacin ban sake ganinta ba sai zuwan wannna dan uwan nata gare ni.

Lokacinda naje inda suke abin ya bani mamaki domin gani nayi duka rufin gurin da suke a yaye, daga karshe dai na karbi yaron na basu dubu goman ni kuma na wuce ofishin ametokum dashi..


Comments