Min menu

Pages

Ta mutu bayan aurenta da kwana hudu Innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun

 Ta mutu bayan aurenta da kwana hudu Innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun!Hakika mutuwar wannan amaryar ba karamin ishara bace garemu dama sauran musulmai baki daya.

Wannan amarya ce wadda duka kwananta hudu da yin aure amma yau ta mutu Allah ya karbi rayuwarta.

Anyi bikinta kwana hudu da suka wuce ita da mijinta, to amma dake kwana ya kare kuma dama Allah ya rubuta bazata jima da yin aure ba zata mutu gashi ta rasu ta bar mijinta da sauran danginta da abokanta.

Amaryar kanwa ce ga wani fitaccen jarumi  cikin masu shirya fina finan hausa. Dan haka muyi mata addu'a Allah ya gafarta mata yasa ta huta ya haskaka kabarinta, sannan ya baiwa mijinta da danginta hakurin jure wannan rashin, mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani.

Jan hankali garemu.

Ya yan'uwa hakika yanada kyau muna tuna mutuwa sannan muna tuna cewa koda yaushe zata iya zuwa ta dauke mu muna shirye ko kuma bama shirye muna cikin aikin lada ko kuma muna aikata wani aiki maras kyau dan haka mu yawaita tuba muna mu sanya tunanin cewa zamu iya barin duniya yanzu ko an jima.

Ku duba kuga wannan baiwar Allah data mutu a lokacin da take amarya tana tunanin ta shiga sabuwar rayuwa amma dake kwana ya kare Allah ya rubuta ta rasu dan haka muyi hankali da wannan duniyar mu daina aikata ayyuka marasa kyau mu tuba ga Allah.

Comments