Min menu

Pages

An samu matsala a Daren farkon wannan auren domin ango yaga ta kansa

An samu matsala a Daren farkon wannan auren domin ango yaga ta kansa

 


Ina nan a tsaye har saida na daina hango danjar motar tasa sannan na shiga gida, kasancewar dakina a bakin kofa yake sai kawai na shiga ban tsaya bata lokaci ba na cire sabin kayan nawa na ajiye a gefe guda dan kar karin gugar nasu ya baci dan kuwa dasu nake sa ran komawa gun husna gobe...

Bayan na saka tsofin kayana sai kawai nai tsalle na hau kan tsohuwar katifata kura ta turnike kamar ana sukuwar dawakai nanfa gadon bayana ya sage saboda buguwar da nayi a jikin busheshshiyar katifar tawa bansan lokacin da nayi kara gamida mikewa tsayeba...

Na dade a tsaye bayana a sankare kamar wanda aka dakeni da sanda sannan na samu bayan nawa yadan dawo saiti...

Na dan karasa inda katifar take na hau cikin sanda dan gudun abinda taimin dazu na jingina da bango ina tunani da nazarin yadda soyayyata zata kasance da husna a haka har bacci ya zagayo ya daukeni...

Zafin ranar gamida haskenta suka doki fuskata nai sauri na tashi daga nannauyan baccin da nake naga ashema gari ya waye har rana ta fito, abin yayi matukar bani mamaki saboda wannan makarar da nayi dan kuwa ni iya sanina nasan na kai shekara uku ban makara irin yauba..

Nai sauri na mike daga kwancen da nake sannan naje nai alwala nai sallah...

Bayan la'asar tayi munyi sallah naje nai wanka na shirya tsaf nasa kayana sannan na kama hanyar zuwa gidansu gimbiyata husna...

Na dade ina tafiya da kafafuna sannan na samu na karasa kofar gidan ai kuwa tun kafin na tsaya naga itama ta fito kamar tasan cewa na iso...

Da tattausan murmushinta ta tareni sannan taimin umarni damu karasa cikin gidan nasu...

Banyi mata musuba ta shige gaba na bita a baya har muka karasa cikin farfajiyar gidan, cikin gidan an kawatashi da kayayyaki na alatu da jin dadin rayuwa ga shuke shuke masu matukar kyau da daukar hankali furenninsu sai kamshi suke...

Karkashin wata bishiyar zaitun nan ne inda husna ta tanada mana ma'ana nanne inda za muyi shirar da ita a wannan yammacin...

Bayan ta nunamin wata kujerar roba da take girke a gun su biyu suna fuskantar juna sai kuma dan wani tebir da aka ajiye a tsakiyar kujerun ma'ana sune suka raba tsakanin kujerun...

Ban jira komaiba na karasa na zauna itama tazo ta zauna a daya kujerar muka fuskanci juna nida ita babu wanda yace da wani kala, saida muka dauki lokaci muna kallon kallo nida ita sannan husnan ta katse shirun namu da murmushinta mai daukar hankali sannan ta fara yimin magana da yar siririyar muryarta mai kamar ana busa sarewa tace dani...

Yaya Abdul ashe dama zaka zo?

Murmushi kawai nayi sannan na dubeta har cikin idanunta nace haba husna menene zai hanani zuwa gareki in har ina raye?

Gaskiya naji dadin zuwanka sosai dan wallahi jiya kusan kasa bacci nayi saboda kewa da kuma tunaninka harma so nake gari yai saurin wayewa na kiraka na danji muryarka sai kuma na tuna ashe baka da waya husna ta sake cewa dani tana wasa da yatsun hannunta...

Murmushi kawai nayi sannan nace karki damu husna ai gashi nazo gareki dan kuwa nima kaina saida tunaninki ya dinga kaiwa da komowa a cikin zuciya naji babu wacce nake kaunar sake gani kamar ke kunnuwana kuma muryarki kawai suke bukatar suji nima nai mata wannan furucin...

Na gode kwarai yaya Abdul dina gashi kuma mun tsaya sai zuba muke ko ruwan sha ban kawo maka ba na barka da yunwa gamida kishirwa husna ta fada tana kokarin mikewa tsaye daga kan kujerar da take...

Husna kenan aini babu wata yunwar da nakeji a halin yanzu tunda ina tare dake haka kuma zan iya shafe tsawon wasu kwanaki ba tare da naci ko kuma nasha wani abuba idan har kina kusana dan kuwa sautin muryarki shi kadai yakan gusarmin da yunwar da nakeji haka kuma ganin wannan kyakkyawar fuskar taki mai annuri yakan kawarmin da kishirwar da nakeji nace da ita...

Lumshe idanunta kawai tayi sannan ta bude ta dubeni tace yaya abdul kalamanka suna matukar birgeni ina jin dadinsu sosai da sosai dan haka jirani ina zuwa tana maganar ta kada kanta ta nufi cikin gidan nasu..

Nai shiru ina tunanin wannan hali na mutuncin da husna taimin na dubi girman gidan gamida tsarin da yake dashi na kuma tuna yadda tsarin namu gidan yake na kasa ne haka kuma ya tsufa dan kujejjen rufinsa duk yayi baki saboda yawan shekarunda ya shafe, muna matukar shan wahala musamman idan lokacin damuna ne dan kuwa idan har ana ruwa to kusan a tsaye muke kwana saboda fashewar da rufin dakunan gidan namu ke dashi na girgiza kai na tuno cewa wai idan zanyi aure dole sai dai a bani daya daga cikin tsofin dakunan dake cikin gidan na tare da amaryar tawa...

Anya kuwa husna zata amince ita da take zaune a cikin wannan katafaren gidan?

Na tambayi kaina lokaci guda ina tunanin girman matsayinta

Mezai hana ta amince idan har tana kaunar taka wata zuciyar ta fadamin...

Gaskiya akwai abin mamaki idan har husna zata iya zama a gidanmu dan kuwa ko kusa baiyi tsari da irin gidajen da yayan manyan masu kudi suke zaman aure a cikiba sauda dama nakanga babu wani da yake auren yar gidan mai kudi sai yayan masu kudi ko kuma yayan sarakuna da kuma manyan yan siyasa...

Haka kuma sau tari yayan talakawa sunfi auran ruwansu ma'ana yan uwansu talakawa..

Ban gama tunaninda nakeba sanadin zazzakar muryar husna da takemin magana..

Firgigit nai saurin daga kaina na dubeta sannan wani dan fatalwan murmushi ya subuce daga fatar bakina...

Yaya Abdul dina tunanin me kake haka? Husna ta tambayeni tana kallona...

Tunani kuma husna? Na maida mata da tambayar da tayi a gareni...

Eh tunani mana abdul, dan Allah tunanin me kake? Ta sake tambayata.,

Husna tunanin yadda rayuwarmu zata kasance gaba nakeyi  musamman idan na tuna yadda zamu rabu dake nai mata karya a karo na farko, wanda ni kaina nasan ta gane hakan...

Kuramin ido tayi kamar wacce zata gano abinda ke damuna sai kuma lokaci guda tayi murmushi ta zauna a kujerar da ta tashi dazu...

Ta dade idanunta suna kaina ni kuma na kasa cewa kala tun daga maganar da na fada mata tun dazu, yaya Abdul waye ya fada maka zamu rabu haka kuma wa zai rabamu da kai? Lokaci guda ta jeromin wadannan tambayoyin nata har guda biyu...

Husna a hakikanin gaskiya ke baki kasance daga cikin irin matannan da suka taso cikin wahala da talauciba haka kuma ina tunanin rana a tsaka bazaki iya samun kanki a cikin irin wannan halin ki jure ba na sake cewa da ita..

Eh abdul maganar da ka fada ta farko gaskiya ne cewar na taso cikin jin dadi to amma waye ya fada maka bazan iya jure zaman talauci ba? Husna ta sake tambayata...

A gaskiya husna ina tunanin bazaki iya zama a gidan mu ba dan kuwa gaskiya a yadda naga gidanku yadda kika taso cikin jin dadi bani tunanin zaki iya zama a gidanmu mu talakawa..

Karka damu abdul in dai nice bana tunanin akwai yanayin da bazan iya jurewa ba indai akanka ne dan haka rike wannan ta mikomin wani abu a cikin leda..

Nai sauri na dubeta nace husna menene a ciki haka da kikamin kyautarsa?

Waya na saya maka abdul dan kawai muke magana dakai idan bama tare dan na dinga jin daddadar muryar nan taka haka kuma naji a wanne hali kake ciki dan wallahi ko kusa banso kayi nesa dani, dan sai naji kamar wani abune zai sameka idan bama tare ko kuma  watace zatamin kwacenka hakan tasa dazu da rana naje na sayo maka ita husna ta sake cewa dani...

Hannuna yana rawa na karba lokaci guda na bude kwalin wata hadaddiyar waya na gani irin wacce ake yayi irin wadda duk wani maiji da kansa zaiso ace irin wayar yake rikewa tun daga kan manyan samari har zuwa manyan yan mata haka kuma yayan manyan masu kudi ko kuma masu mulki...

Na bude baki da niyyar nayi godiya a gareta amma tun kafin nace komai tai saurin rufemin bakina da hannunta sannan tace haba yaya abdul ai bai dace kamin godiya ba danna sayama waya kuma naga idan banyiwa masoyina abin kaunata abuba wa kuma zanyima dan haka kome nayi a gareka ko kadan bana bukatar sai kamin godiya husna tace dani...

Shiru nayi ina kallonta harta gama maganar da takemin sannan nayi murmushi nace husna kenan, ai ya zame dole a gareni nayi godiya sakamakon irin kaunar da kike nunawa a gareni wanda hakan yakesa ni kuma zuciyata take kasa nutsuwa idan harba godiyarnan nayi a garekiba domin husna...na kasa karasa maganar saboda tsananin dadin da yake kai kawo a cikin zuciyata...

To abdul nima na gode husna tace dani tana kallon can wani bangare mai tarin shuke shuke dake cikin gidan...

To husna nikam zan wuce dan haka sai goben idan na dawo ko kuma idan munyi waya dake dan haka bari na fada miki number tawa saiki ajiye dan kuwa dama na fada miki inada layi wanda nake amfani dashi da kafin bukata ta tasomin na sayar da wayar...

To yaya abdul fadamin number husna tace dani lokacinda ta zaro tata wayar abin yayi matukar birgeni dan kuwa itama tata wayar iri daya ce da wacce ta sayamin..

Uhm nai murmushi sannan na fara da bata number tawa kamar haka 08060763027...

To shikenan zan kiraka da an jima dan haka karbi wannan kasa kati danka kira sauran yan uwa da kuma abokanka husna ta fada lokacinda ta mikomin daurin kudi yan dubu dubu...

Ji nayi gabana ya fadi kirjina ya buga da karfi lokacin da naga wannan daurin kudin dan kuwa nidai tunda nake ban taba kawo cewa zan mallaki kudin da zai kai yawan wadannan ba har zuwa lokaci mai tsawo na dubeta sannan na dubi kudin dake hannunta na girgiza kai nace haba haba husna gaskiya bazan karbi wadannan kudaden nakiba dan kuwa idan har maganar gaskiya za ayi to nine ya dace ace na baki bawai kece zaki baniba...

Wani lokacin kana bani mamaki yaya abdul da har kake wani mamaki idan nayi maka abu na sani idan kaima kana da halin yin hakan ai zakamin abinda yafi wannan ma dan haka ka karba idan harba so kake ka batamin raina ba husna ta fada wannan karon kam bata rai tayi tana kallona...

Nai saurin karbar kudin sannan nace husna na karba dan haka daina bata rai dan kuwa ko kadan banso naga kin damu...

Murmushi kawai tayi sannan tace yauwa abdul dina har kasa naji dadi a cikin raina...

To shikenan husna nizan wuce saina jiki idan munyi waya nace da ita...

To yayana husna ta fada lokacin da ta takemin baya ta rakoni har kofar da zata fitar dani daga cikin gidan nasu sannan mukayi bankwana da ita na kama hanyar da zata kaini gida zuciyata cike da murna gamida farin cikin abinda husna tamin da haka harna karasa kofar gidanmu..

Ina zuwa na fita da gudu na shiga zauren gidanmu idanuna a rufe saboda murna karon da naji nayi da mutum ne yasa nai saurin bude idanuna mubarak na gani a tsaye nai saurin dubansa nai dariya sannan nace wallahi kado ta sayamin waya mai matukar kyau...

Waye ta saya maka wayar ne da zaka zo har kana hankadeni...

Wa kake tunanin zata sayamin waya idan ba sarauniyar mataba? Ai kaima kasan wannan aikin sai tauraruwar taurari mai hankali tarbiya tunani gamida sanin daraja da girman mutane mai yawan taimako...

Abdul kenan, ni sai fadamin halayen mace kakeyi kuma kaki fadamin sunanta ai yana da kyau ka fadamin sunanta danna gane mubarak ya sake fada...

Husna mana ai kaima kasan itace zatamin irin wannan kyautar na fada ina kallonsa...

Ban jira ya sakemin magana ba kawai na wuce cikin gida..

Haka mukaci gaba da soyayya da husna har tsawon wata biyar ya zamana kowa a gidansu yasanni haka nima kowa ya santa a gidanmu hakan kuwa ya biyo bayan gwagwarmayar da husna tasha akan sai an barta munyi aure saboda jajircewar da sauran yan gidansu sukayi akan bazata auri talaka irina ba daga karshe sai kuma komai ya zama tarishi ya zamana sun amince akan ta aureni...

Munyi matukar farin ciki lokacin da aka yanke ranar aurena da husna abbanta ya bamu wani hadadden gida wanda zamu zauna nida gimbiyata husna...

Haka mukaci gaba da zama cikin farin ciki har ranar daurin aurena da husna tazo..

Ba laifi ansha biki sosai da sosai an cashe duk kan abokaina sun ziyarci auren nawa tun daga kan maza har zuwa mata...

Bayan dare yayi abokaina su sadauki da mubarak da sauran abokaina guda uku sukamin rakiya zuwa dakin bayan yan sauran maganganun da abokaina sukayi mana nida gimbiyar tawa amatsayin nasiha sai kuma sukacemin zasu tafi...

To shikenan bari nayi muku rakiya koda bakin kofane nace dasu...

Haba yaya abdul ai ba'a raka abokai tunda kaima kaga rakoka sukayi dan haka ka barsu su tafi amarya husna tace...

To amarsu ta ango mu yau saiya rakamu waje tukunna ko an fada miki guduwa za muyi dashine sadauki ya fada yana dariya...

Karki damu gimbiyata yanzu zan dawo nace da ita lokacin da na takewa abokan nawa baya mukayi waje...

To yaya abdul a dawo lafiya husna tace dani..

Tunda na rakasu bakin kofar mukai bankwana dasu sai kawai na nufo ciki dakin da amaryata take cikin farin ciki da zuwan wannan daren mai suna DAREN FARKO...

Kaina ne ya sara da karfi lokacinda na shiga cikin dakin numfashina ya fara sarkewa idanuna ya fara lumshewa wani jiri ya fara daukata naji na tafi luu zan fadi nai sauri na dafa bangon dakin da hannuna sakamakon ganinta da nayi a kasa mala mala cikin jini...

Lokaci guda idanuna suka zaro lokacinda naga irin mummunan yankan ragon da akai mata kanta yana kallon rufin dakin gashin dake kanta ya baje duk jini ya batashi...

Sannan kuma naga wukar da aka yankata da ita a yashe a kusa da ita sai sheki da walwali take...

Jikina na rawa na samu na tashi daga zaunen da nake gamida fige katuwar rigar tawa wacce ta jike sharkaf da gumi kamar wanda yayi aikin karfi, sannan na karasa gunda take kwance na durkusa na kalleta naga ko alamar motsi batayi..

nan take hawaye ya fara kwaranya a cikin idanuna...

Waya kasheki husna?

Nace da karfi, haba husna ya zakimin haka ya zaki tafi ki barni, yaune fa DAREN FARKO na aurenmu ni dake...

Ya za ayi ki mutu ki barni? Ya zakimin haka husna? Ki sani auren soyayya mukai ni dake yau kuma kika tare a gidana kuma yau shine DAREN FARKO na amarcin mu..

Lokaci guda naji wani sassanyan hawaye ya fara kwaranya daga cikin idanuna nasa hannu na dauki wukar da aka yanka husna da ita na dagata sama na fara jujjuyata a hannuna ina kuka...

Yaya Abdul a dawo lafiya, naji kalamanta na karshe suna kai kawo a cikin kaina

wayyo husnata dan Allah ki taimakamin ki tashi ki sanar dani waya kasheki nima wallahi nayi alkawarin saina rama miki na fada da karfi nai saurin daukar wayata na kira sadauki...

Sadauki kazo gidana yanzu akwai matsala dan wallahi an yanka husna...

Banma gama maganar da zanyiba sanadin daukewar da wayata tayi...

Nai shiru ina kallon husnan da take kwance cikin jini na tuna kamar ba ita bace husnan da aka kawomin ita amatsayin sabuwar amaryata amma wai itace a kwance bata motsi an yankata kamar wani rago...

Lokaci guda hawaye yaci gaba da kwarara a cikin idanuna na karasa gabanta na dukursa na kamo kanta da wukar a hannuna na fara jijjigata...

Budewar da naji kofar tayi da karfi ne yasa nai saurin juyawa da sauri su uku na gani da bakaken kaya sai kuma sadauki da yake take musu baya...

Abdul waya kasheta..? Kar dai kacemin kaine ka kasheta..? Haka kuma a garinya ka kasheta? Me tayi maka ka kasheta lokaci guda naji sadauki ya jeromin wadannan tambayoyin...

Lokaci guda na saki wukar da fadi kasa gaba daya hannuna yayi kaca kaca da jini na dubesu su sadauki da kuma sauran yan sandan da suke tsaye tun shigowarsu ba suce komai ba sannan nace wallahi sadauki bani na kasheta ba..

You are under arrest! Naji yan sandan sun fada lokacinda suke kokarin sakamin ankwar a hannuna...

Nai sauri na kawar da hannuna sannan na dubesu bakina na rawa nace wallahi bani na kasheta ba yama za ayi na kasheta yau fa ta tare a gidana itace sabuwar amaryata da aka daura aurena da ita yaunefa DAREN FARKO

Zakai bayani dan samari a gaban kuliya zaka fadi wanda ya kasheta da kanka suka sake fada lokaci guda kuma suka garkamamin ankwar a hannuna...

Na daga kaina na dubi yan sandan gaba daya hankalina ya gama tashi da wanne zanji da bakin cikin kashe matata husna zanji ko kuwa da doramin alhakin kisan zanji, wallahi yallabai bani na kasheta ba yayama za ayi na kasheta na sake cewa dasu...

To idan ba kaine ka kasheta ba waya kasheta yan sandan suka kuma tambayata a lokaci guda...

Wallahi bansan wanda ya kasheta ba na basu amsa...

Kaga malam karka raina mana hankali ko kaga munyi kama da irin mutanen da zaka raina ne wani bakin dan sanda mai katon kai gamida jajaren idanu da kuma buzu buzun gashin baki wanda suka taru suka kara fito da tsananin muninsa yamin magana...

Yahuza tsaya anan ka jire gawar kafin muje mu dawo ka tabbatar ko kadan baka taba kayannan ba mu kuma zamu je da wannan police station daga can zamu biya mu dauko likitan da zai gwada dan gano ko hannun waye yai kisan a jikin wukar daya daga cikin dan sandan ya fada..

Ok sir yahuza yace lokacin da ya sarawa dan sandan da yayi masa maganar sannan ya kame...

Lokaci guda suka sani gaba kamar sa cinyeni danye sukai waje dani suna zuwa suka debeni gamida watsani cikin motar tasu kamar wani kayan wanki, kayina ya bugo da kasan motar nai kara saboda tsananin zafin da naji...

Suka fisgi motar tasu da karfi suka bar unguwar, gaba daya babu alamar jama'a ko ina yayi tsit saboda daren da yayi, banda kukan tayar motar da yakebi ta saman kwaltar babu abinda za kaji...

Ku sauko dashi ku sashi a dakin horo ina so kafin muje yanzu na dawo ya fada muku wanda ya kasheta dan sandan dake cikin motar ya baiwa sauran kwalawan dake tsaye a bakin station din umarni...

Ban zata ba ban nufa ba saiji nayi sun jawo dani da karfi daga kan motar na fado kasa sannan suka kwasheni sukai cikin dakin horon dani...

Dakin dan tsukakkene mai matsakaicin tsawo ko kusa baka isa ka mike tsaye a cikiba, su biyu ne naga sun shigo dakin da wasu sanduna kamar zasu daki wani naman jeji da su...


Zaka fada mana wanda ya kasheta ko kuwa saika fara yabawa aya zakinta wani daga cikinsu mai suffar yan kokuwa shine yai wannan maganar...


Wallahi nima bansan wanda ya kasheta ba...nai shiru tun kafin nakai karshen maganar sanadin kulaken da naji sun fara sauka a kaina kamar ruwan sama...


Ban isa yin wani kwakwkwaran motsiba sai naji sun rufani da duka haka sukaci gaba da kadamin wadannan kulaken tun ina iya karewa da hannuna harma na kasa daga karshe  kuma sai na daina jin abinda yake faruwa saboda suman da nayi...


Bayan sun tabbatar da na suma ne sannan suka barni suka koma suka tsaya a waje suna jiran na farfado su sake rufeni da duka da wadannan kulaken dake hannuwan nasu...


Saida na dauki lokaci mai tsawo sannan na farfado daga dogon suman da nayi a lokacinda su kuma kwalawan yan sandan suka dawo cikin, wannan karon harda wani wanda ga dukkan alamu shine babbansu.


Saida na kare masa kallo sannan na fara tuno abinda ya faru dani dazu, sannan na sake tuno shine dan sandan daya basu umarnin su dakeni har sai nayi bayanin waye ya kashe matata husna..


Sir har yanzu bai fada mana wanda ya kasheta ba sannan kuma har yanzu yaki ya amsa laifinsa ya amince da cewar shine yai kisan, daya daga cikin kwalawan dan sandan yace da mutumin da ya basu umarnin sannan lokaci guda ya kame..


Ku dauko shi mu koma gidan domin yanzu haka muna tare da likitan da zai mana aikin duba hoton yatsun yace dasu lokaci guda ya juya ya fice daga cikin dakin..


Ko tausayina babu wanda yaji a cikinsu, haka suka cakumoni sukayi waje dani sannan suka watsani a bayan motar kowa yai tsalle ya hau..


Kamar jira yake drivern ya fusgi motar da karfi sannan ya dorata akan titi, daya daga cikin kwalawan yai saurin kankame karfen jikin motar domin bai gama hawa ba drivern yaja motar...


Nai saurin mikewa tsaye daga cikin motar sannan na tafi da gudu domin na fita daga motar nasan inda dare yayimin...


Zaka iya guduwa daga nan har birnin sin idan har zaka iya hakan din sai dai ko kadan karka zargemu dan albarushin bindigarmu ya samu matsugunni a wannan dan kyakkyawan kan naka yan sandan suka ce dani lokacinda suka nunoni da bakin bindigoginsu...


Nai turus na tsaya na kasa tafiya danna sani zasu iya aikata komai idan na gudu haka kuma kowa zai yadda cewa nine na kasheta idan harna gudu to amma idan na tsaya komai zai zo da sauki duk dama dai ba lalle bane su mutane su yadda akan cewa bani na kashe husna ba...


Ka fasa guduwar kenan? Suka tambayeni suna dariya...


Shiru dai nayi bance dasu komai ba...


Ai bamu sanka da tsoroba kaida ka aikata kisan kai kuma meye naka na tsorata dan munce ga fili nan kaita gudu daga nan har birnin sin yan sandan suka kuma cewa dani lokacin da muka karyo kwanar da zata shigar damu layin da gidan yake...


Tun kafin mu karaso kofar gidan na hango motoci guda biyu dayar na sani ta mahaifin husna ce haka kuma dayar ma ko tantama banayi ta adama ce wato kawar husna waya fada musu halin da ake ciki? Na tambayi kaina ban samu damar samo amsar ba sanadin birkin da naji an taka hakan shine ya bani tabbacin munzo kofar gidan...


Gabaki dayan su suka fito daga cikin motar daga su har likitan sannan biyu daga cikin yan sandan suka sauko dani suka sani a tsakiya suka tura keyata muka nufi cikin gidan hannuna yana garkame da ankwa...


Su wajen biyar na gani a tsatstsaye sun kewa ye gawar da sadauki sai adama kawar husna sai kuma mahaifanta uwa da uba da kuma dan sandan da aka bari jiron gawar husnan yana nan a kame baya ko motsi...


Wallahi bazan yarda ba sai an biyani yata maman husna ta fara fada lokacin da muka shigo...


Kiyi hakuri hajiya za'a gano wanda ya kashe yarki insha Allahu nan da dan lokaci dan yanzu hakama muna tare da likitan da zai gwada wukar da akai wannan aikin da ita domin ganin zanen hannun kona waye shugaban yan sandan yace da ita lokaci guda ya dubi likitan ya bashi umarni daya fara aikin nasa...


Bayan dan lokacin da likitan ya dauka yana yin gwaje gwaje akan wukar yana rubutawa sai kuma ya dawo inda nake ya kama hannuna yaci gaba da dubawa..


A bisa binciken da nayi na gano babu wani zanen hannu wanda ya taba wukar nan face na mutun daya dana duba sai naga zanen hannun yayi dai dai dana wannan mutumin ya nunani da hannunsa...


Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un naji kusan gaba dayansu sun fada..


Dama wallahi yace saiya dau mataki akan husna koda ace ya aureta, dan haka kuma saika kasheta abdul dama kasheta kakeso kayi shi isa ka aureta naji adama ta fada lokaci guda kuma ta fara kuka...


Au dama yace saiya kasheta ne tun farko amma adama baki fada mana ba har muka aura masa ita to wallahi bazan taba yarda ba dole na makashi a kotu domin a hukunta shi ya kuma fadi dalilinsa na kashemin yata mahaifin husna ya fada...


                  *       *         *        *

kotun ta cika iya cika ko ina ka duba zaka iske mutane ne a zazzaune kowa yayi shiru dan saurarar shari'ar da za ayi..


Mai gabatarwa ya tashi bayan yayi gaisuwa gurin alkali sai kuma ya fara da cewa yau litinin sha shida ga watan goma sha daya shekara ta dubu biyu da goma sha tara, wannan kotu mai alfarma zata fara sauraron kara mai lamba goma sha hudu a sakin layi na biyu wato karar da alhaji isma'ila ya shigar akan kisan gillar da akaiwa yarsa husna a ranar data tare a gidan ta amatsayin amarya, lokaci guda saiya mikawa alkalin takardun dake hannunsa ya koma ya zauna...


Bayan yan nazari da alkalin yayi ga takardun nadan wani lokaci sai kuma ya fara magana da cewa ko lauyan wanda yake kara yana da bayanin da zaiyi..


Eh akwai mai girma mai sharia, sunana bar. Haruna shehu kani, nine lauyan bangaren da suka shigar da kara...


Bar. Haruna ko kanada abin cewa alkalin ya tambaya..


Ba wani abin ja bane game da wannan shariar domin kowa daga cikin mutane suna da tabbacin cewa wanda ake zargi shine ya aikata wannan kisan haka kuma zamu iya gabatar da saidu masu yawa wadanda suke nuni da cewa eh lalle shine yai kisan...


Zaka fada idan bukatar hakan ta taso alkalin yace lokaci guda kuma ya kara da cewa ko lauyan wanda ake kara yana da abin fada...


Eh akwai yamai girma mai sharia naji  muryar mace ta ratso cikin kotun nai sauri na daga kaina domin ganin mai maganar ba kowa na ganiba sai safiya s musa wata makociyar mu abin yayi matukar dauremin kai da naga itace lauyan da zata kareni ba komai bane ya bani mamaki ba face nasan safiya bata dade da kammala karatun da take ba na lauya dan ko aikima bata fara ba kuma wai ita ce wadda zata kareni...


Sunana safiyya s musa nice lauyan da zan kare wadda ake kara...


Malama safiyya ko kina da abinda zakice a game da wanda ake kara alkalin ya tambaya..


Eh akwai tace lokaci guda ta tashi daga inda take zaune ta karaso guna inda nake a tsaye...


Malam ko zaka iya fadawa kotu sunanka da kuma sana'arda kake? Ta tambayeni...


Sunana Abdulrahim yusuf haka kuma bana sana'ar komai face saida ruwa na bata amsa...


To malam abdul kana nufin cewa da wannan yar sana'ar ruwan naka kenen kake samun abinda kake ci har kuma kayi aure ko?


Eh da wannan sana'ar da nake ci nasha harma na ciyar da namu gidan to amma yanzu duk alhaji ne ya daukemin nauyinsu harta da gidan da zamu zauna ma'ana mahaifin husna nace da ita...


Idan na fahimceka kana nufin cewa alhajinne ya baka gida tare da yarsa ka aura kenan haka kuma ya dauki nauyinku harma dana mahaifanka...


Eh hakane na bata amsa..


Ya mai girma mai sharia ina so kotu mai alfarma tai duba da idon basira taga cewa yaya za'ai mutumin da akaiwa dukkan alfarmomin nan akan yana tare da abu daya to tayaya zaiso wannan abin wanda yake karuwa daga karkashinsa yai nesa dashi? Kaga abinda bazai taba iyuwa bane kenan dan haka nakega bazai kashe matarsa ba domin koba komai itace bangon daya dogara a jikinta ta dalilinta yake samun ci da kuma sha...


Kotu ta duba duk wasu maganganu da bangarori biyu suka kawo dan haka ta daga karar nan zuwa ashirin da biyu ga wannan watan haka kuma za aci gaba da tsare wanda ake zargi har zuwa ranar zama na gaba alkalin ya fada lokaci guda ya buga gudumar dake kusa dashi...


Kwanci tashi har kwanakin suka zo yauma kotun a cike take kamar wancen lokacin zuciyata sai famar bugawa take dan nasan ayau za'a gama shariar kuma ayau nima za'a yankemin hukuncin kisa duk da nasan ba nine na kasheta ba...


Ba wani dogon bayani zanyiba yau dan kuwa an sani wanda ya ake zargi shine yai kisan saidai zan kawo hujjoji wanda zasu tabbatar da hakan barr. Haruna yace lokaci guda ya fara gabato da hujjojinsa tun daga kan hoton hannuna da ya fito a jikin wukar sannan ya gabato da adama amatsayin shaidarsa ta gaba ta kuma bada amsa da cewa nace saina dau mataki akan husna koda na aureta ne tun farkon haduwata dasu a auren sadauki...


To lauyan wadda yake kara ko yanada tasa shaidar da zai gabatar alkalin ya kuma tambaya...


Eh ina da saida ya mai girma safiyya ta fada lokaci guda ta tashi tsaye..


Hujjar da zan kawo itace wanda take gaba da dukkanin hujjojin da wadannan suka kawo kuma ita ce wadda zata bada tabbacin ba abdul bane yai wannan kisan safiyya ta fada

 Barr. Zaki iya kawowa hujjar alkali yace..

Duk kan wasu hujjoji suna wayar marigayiya husna domin naga text message har biyu wanda aka rubuta mata dayan an nuna cewa ne ta zauna cikin shiri domin idan ta kuskura ta fadawa wani za'a kasheta dayan kuma cewa yayi fadar wannan sirrin ga wani daidai yake da saida ranta to da muka duba sunan mai number sai mukaga an rubuta DAN FULANI hakan tasa na sake shiga cikin wayar anan kuma na tadda recording guda biyu na maganar da tayi da wani...


Dayan sunyi maganane akan cewa shi abokin abdulrahim saurayinta ne kuma sunansa dan fulani dan haka shima yana sonta kuma zai aureta harma yace mata ta rabu da abdul ma'ana saurayin nata kenan...


To ta nuna bazata amince dashiba harma daga karshe suka fara cacar baki tace saita fadawa abdul ma'ana zata sanar dashi cewa akwai wani a abokansa mai suna dan fulani daya ce yana sonta zai aureta to dan fulanin da yaga cewa idan harta fadi haka zaiji kunya agun abokinsa saiya fara lallashinta yana bata baki akan cewa tayi hakuri karta fadawa saurayin nata halin da ake ciki to saita nuna cewa a'a itafa gaskiya saita fada kuma bazata fada bama sai ranar darensu na farko, to da yaji haka sai kuma ya fara yi mata gargadi da cewa idan har ta kuskura ta fada to kuwa zata yabawa aya zakinta..


A dayan kuma cigaba yayi daga waccan maganar da sukayi ya kara da cewa bazata kwana a duniyaba idan harta fada dan kuwa shine zai zamo ajalinta a daren farko..


Lokacin da barr.  Safiya tazo nan a zancenta sai sai kawai ta zaro wayar husnan ta kunna recording din a gaban kowa aka saurara sannan ta fito da rubutaccen sakon ta nunawa alkali...


Bayan alkali ya karanta sai yai umarni akan a tafi a nemo dan fulani aduk inda yake tun kafin su yan aikan su fita sai gashi ya shigo kamar an jefoshi dan fulani ne tun kafin ayi wata maganar nai nuni da hannuna inda yake nace gashinan shine dan fulanin...


Baiyi wani motsiba koya nuna zai gudu sai kawai yace eh nine dan fulani kuma nasan za'a nemeni shi yasa na kawo kaina nine na aikata laifin ba abdulrahim da kuke zargiba kuma amin duk wani hukunci da akaga ya dace dani akan haka...


Kammalawa


na dubi dan fulani sannan na dubi dukkan jama'ar dake kotun na sunkuyar da kaina sannan nace dan fulani dama wannan shine abotar da take tsakanina dakai dama zaka iya yimin haka ashe dama.. Na kasa magana sakamakon bakina da naji yana sarkewa sai a lokacin na tuna maganarda husna take cewa zata fadamin amma sai a ran daren farko na aurena da ita ashe dama wannan maganar zata sanar dani...


A lokacin aka kama dan fulani ni kuma aka wankeni daga laifin da ake zargina dashi nayi matukar godiya ga barrister safiya saboda jajircewarda tayi a kaina daga nan aka sallameni na koma gida dan fulani kuma aka yankemar hukuncin kisa...

Karshe

Ina mika sakon godiyata zuwa gareku masoyana da kuke sadaukar da lokacinku wajen karanta labaraina. NA GODE

Naku ABDULRAHEEM YUSUF BULANGU.

08060763027

Comments