Min menu

Pages

Mutane sai rige rigen ficewa suke daga WhatsApp saboda wasu dalilai.

Mutane sai rige rigen ficewa suke daga WhatsApp



Wani abin mamaki wai yau mutane ne da kansu ke ficewa daga WhatsApp, manhajar da mutane masu matukar yawa ke amfani da ita to saidai yanzu ga dukkan alamu mutane zasu fice kamar yadda suke yawan fada matukar kamfanin na WhatsApp ya bai dakatar da wannan tsarin da ya dauko ba..

Dalilin da yasa mutane ke yin WhatsApp

Mutane da dama suna yin WhatsApp ne ko kuma sun dauke shi wani guri da suke amfani domin tattaunawa da juna da kuma gaisuwa da abokan hulda yayinda mutane da dama ke amfani da manhajar wajen gabatar da kasuwancin su.

Waye mamallakin manhajar WhatsApp

Mai kamfanin Whatsapp shine mamallakin manhajar facebook dan haka yake ganin zai sake tsarin na WhatsApp din ya koma kamar facebook ta hanyar duk wani da yake so yayi amfani da manhajar to sai ya saka dukkan bayanansa na sirri kamar yadda facebook yake dashi sannan kuma in kayi abu kai tsaye za a nunawa mutane dukkan abinda kayi kamar yadda facebook yake.

Mutane sunji rashin dadi

To saidai abin bai yiwa mutane dadi ba domin a cewarsu domin sirri shine dalilin da yasa suke yin WhatsApp din domin duk abinda suke a ciki babu wani da yake gani sai su kadai ba kamar facebook ba.

Dokar da mai manhajar ya saka

Mai kamfanin Whatsapp din ya fitar da dokar ne wanda yace lalle sai kowa ya amince da ita sannan za a bashi damar yin amfani da manhajar in kuma mutum bai amince ba to shikenan bashi da damar da zaiyi amfani da manhajar wanda wannan dokar zata fara zuwa ne nan bada dadewa ba.

Mutane kuwa ganin haka yasa har sun fara kaura suna komawa telegram domin a cewarsu can babu bukatar sai sun saka wadannan bayanan sannan yafi dadi fiye da WhatsApp.

A yan kwanakin nan mai kamfanin telegram yace ya samu bakin mutane fiye da miliyan biyar wanda suka kulla alaka da manhajar tasa ta telegram sannan a shirye yake yayi musu dukkan abinda suke bukata.


Hakika manhajar telegram manhaja ce mai matukar dadi sannan dukkan abinda WhatsApp yake yi telegram ma yana yi sannan yafi WhatsApp nesa ba kusa ba domin duk girman abu zaka iya turawa ta ciki walau waka film dadai sauransu


Comments