Min menu

Pages

Jebun budurci da mata ke amfani dashi idan sun rasa na gaskiyar

Jebun budurci da mata ke amfani dashi idan sun rasa na gaskiyar
Yanzu munzo wani karni da samari ke ta fatan suga sun auri mace tana budurwa hakan yasa a daren farko har dubawa suke domin su tabbatar da hakan domin kawar da zargi, wannan abin ba karamin tayarwa da mata hankali yake ba musamman wadanda suka rasa budurcinsu tun a waje.

Ana haka ne sai wani abu ya bayyana wanda ake cewa fake hymen ma'ana jabun budurci.


Saidai ni kuma a kaina banso yin wannan post din ba saboda abu biyu.


1. Ina mai kunyar kalmomin dazanyi amfani dasu wajen yin wannan bayanin.


2. Ina mai taka tsantsan wajen bude sirrin masu sirri, amma sai naduba naga rashin baiyana wannan abu zai iya yin karan tsaye ga addininmu da aladun mu.


HYMEN a turance wata fatace datake gaban mata dab a cervix, a hausance tana daukan sunan BUDURCI, kuma rashinta shine rashin budurci.


Fatar bata da karfi sosai kuma ruwa kan iya wuce ta cikinta, tana dauke Da kananan hanyoyi na jini, shiyasa fashewa ko tsagewarta kansa jini ya fita.


Mafi akasari takan tsage idan wadannan abubuwa sun faru


1.idan an sadu da mace(copulation)

2. Wajen neman fitar da shaawa da wani abu mai karfi(vaginal insertion or mastubation)

3.Yawan tsalle ko hawa mashin, keke, doki ko jaki kasancewar maza kanyi amfani da fashewar

wannan fata da fitar jini wajen gwada budurcin ya mace, sai turawa sukai jabun wannan fata wadda ake kira fake hymen domin matan da suka rasa budurcinsu tun a waje kafin suyi aure.

Menene fake hymen ma'ana jabun budurci?

Ita wannan fake hymen din wato jebun budurci, robace da akayita da sinadare masu narkewa dazai dace da jikin

mutum(prosthetic in nature) yanda idan macen data rasa budurcinta tasa zai zauna daidai

agurbin nada, sannan dazarar tasadu da ango wanni jan sinadari zai fashe daga cikin FAKE HYMEN din mai kama da jini, toh dazarar ango yaga haka sai ya zaci matarsa budurwa ya aureta.


Matsalolin da fake hymen zai iya haifarwa

kasancewar bayan saduwa fake hymen zai iya fitowa, inkuma bai fitoba zai iya narkewa a cikin

gaban mace, shiyasa zai iya kawo matsalolin lafiya ga macen datayi amfani dashi.


Haka zalika jan ruwan da FAKE HYMEN din kefitarwa mai kama da jini, shima zai iya canza

kaidar tsaftar vagina mace, saboda cikinsa akwai (chemicals) dauke da kalarja""when ever we change nature, we create a problem"" dan haka fake hymen zai iya sa wadannan abubuwan:-

1. Zai canza yanayin sinadaran dake kiyaye  vagina da turance .

2. Zai iya kawo cancer of the vagina

3.zai iya toshe ma haifa

4. Zai canza tsarin hailar mace

5.zai iya kara recurrent vaginal discharge

6. Zai iya kawo infertility


Comments