Min menu

Pages

 Daren farko 3Nai saurin juyawa na kalli kofar gidan naja da baya da sauri na kalli ango sadaukin sannan nai masa nuni da inda jajayen yan matan suke nace wacce ce husnan a cikinsu?


Ita ce ta bangaren dama amaryar kuma tana tsakiya sai kuma adama wacce take bangaren hagu sadauki ya fadamin...


Kai amma wallahi adamar ma ta hadu mubarak ya fada lokacinda ya kurawa gunda suke idanu yana kallonsu...


Me kake nufi data hadu mubarak kodai kana nufin kace kaima budurwar zakayi yau kamar yadda Abdul ma yace zaiyi? Dan fulani yace..


Salamu alaikum manyan abokan ango mukaji wata zazzakar murya tayi magana lokaci guda kuma sai daddadan kamshin turaresu ya game gun da kamshi...


Amin w.salam manyan kawayen amarya muma muka ce dasu lokacin da kowa ya bude murafen motocin su...


Amarya da kawayenta guda uku husna da adama suka shiga motar farko ma'ana wacce zan tuka kenan sai kuma sauran suka shiga motocin abokan angon...


Na tada motar sannan naja da baya na dorata akan hanyar da zata kaimu gidan angon, a lokacin nasa wakar da na yiwa angon sadauki da sahibar tasa khadija wakar tayi bala'in yin dadi domin kuwa wakace da nayi musu irin ta soyayya a cikin wakar na lissafo sunan abokan amarya haka kuma na lissafa sunan abokan angon...


Kai waye yai wakar nan kuwa husna ta katse shirun namu da tambaya..


Ango sadauki yai saurin juyowa ya kalli mata ukun dake zaune a kujerun baya na cikin motar sannan yace wa kike tunanin zaiyi wannan wakar idan ba ni ango ba..


Suka saka dariya dukansu sannan suka ce lalle kuwa ka fadawa wasu da basu san muryarka ba kace kaine ka rera amma kam ba muba dan kuwa nidai na sani baka isa rera wakaba husnan ta sake fada ta sigar tsokana..


Nidai shiru nayi kawai ina jinsu naci gaba da tukina ban tanka musuba a shirar da suke...


Kudai wallahi ga mawakin nan yana sauraronku ango sadaukin ya fada gamida dafa kafaduna...


A'a nifa ba nine nayi wakar nanba karma yai wani tsaraku, yace nine dan kuwa in kuka lura sosai kuka saurari muryar mawakin zaku yadda dani dan kuwa ko kusa batai kama da tawaba na fada a karo na farko dana saka bakina a zancen da suke...


To kuma ina ruwan mutane koma kaine kayi ko kuma ce maka mukayi dole sai munji wanda yayi wakar? Husnan tace lokacin data bata rai a cikin motar...


Nai saurin juyowa na dubeta sannan nai saurin mayar da kaina kan hanya raina ya gama baci dajin maganar da kawar amarya husna ta fadamin...


Ke husna ba'a haka, bai dace ki fadi wannan maganarba dan kuwa ni wallahi wannan wakar tayimin musamman ma sunanki da sunan amarya da kuma sunana da naji mawakin ya fada kamar yadda muke a yanzu adama ta fada a daya bangaren...


To ai wannan ku kadai ya shafa ni bai dameni ba ni yanzuma idan da damar a cire sunana a cikin wannan wakar to kuwa da ba bala'in jin dadi zanyiba haka kuma zan bada ko nawa ne wallahi husna ta sake fada...


Ba karamin baci raina yayiba zuciyata ta fara tafarfasa kamar zata kone nasa hannuna a hankali na danna gunda ake amfani dashi dan kashe kidan nanfa sautin kidan ya daina tashi cikin motar yai tsit kamar ba wasu masu rai a ciki...


Sai hakuri fa malam haka halin husna yake idan bata ga dama ba sai a hankali dan Allah kayi hakuri adama ta katse shirun da maganarta..


Karki damu ba komai nace da ita lokacin guda naji kaina ya fara ciwo naji motar tana barazanar kwacewa a hannuna, nai sauri na riketa sannan na kara mata wuta ba abinda zuciyata take sai tunane tunanen maganganun da wannan kawar amaryar ta fadamin...


Innalillahi wa inna ilaihirraji'un shine abinda naji gaba dayansu suna fada a tsorace nai saurin dawowa daga tunanin da nake lokacinda motar da muke ciki kuma tayi gefen titi zata gangara nai sauri na dawo da ita bata samu nasarar gangarawa damuba..


Meya hakan Abdul, wanne irin banzan tunani kake kana gani zaka halakamu a wannan ranar? Ango sadaukin yai saurin fada idanunsa a zare saboda tsananin tsorata..


Nai sauri na juyo da kaina gunda su husna kawar amarya take naga ta dora hannunta aka duk da nima na tsorata amma saida naji wani dadi...


To kuyi hakuri tunda dai gashi Allah ya kiyaye ba abinda ya faru kawai dai tsautsayine ya gifta nace dasu..


Malam tsaya da tukin nan haka bani kawai naja motar tunda naga kai so kake ka kashemu dani da sabuwar amaryar tawa tun bata tare a gidan nawa ba ango sadaukin yace dani...


Murmushi kawai nayi gamida taka birki , nan take ango sadaukin ya dawo gunda nake ya karbi motar daga hannuna ni kuma na koma bangaren mai zaman banza na zauna...


Ba muyi wata doguwar tafiya ba muka karaso gurin da muka ware dan nuna farin ciki da kuma murnar auren da sadauki yayi...


Muna zuwa kowa daga cikin abokan angon suka tsatstsayar da motocinsu sannan kowa ya shiga cikin gun..


An kawata gurin sosai ya tsaru iya tsaruwa, kyawawan shuke shuken dake gun sun dada fito da gurin kamshin furanninsu sai tashi yake ko ina, an jera kujeru reras gwanin ban sha'awa da...


Nan fa kowa ya samu gurin zama ya zauna, ango sadauki suka zauna gu daya shida amaryarsa khadija, mubarak ma ya karasa gunda adama take zaune ya zauna a kusa da ita...


Na samu guri na zauna nesa kadan da inda husna take dan gudun wulakancinta zuciyata sai tafarfasa take ni kadai kamar wani bakin kumurcin maciji, duk lokacinda nakai dubana inda husna take to kuwa a lokacin zata hada rai koda ace dariya take to kuwa zata daina..


Abin yana matukar kona min rai idan har tamin haka to amma ya zanyi dole na hakura tunda tun farko dana fara jin muryarta ta kwanta min arai..


Bayan an gabatowa da kowa abinci da abin sha sai kuma dan fulani ya tashi ya fara bayani gamida nuna farin cikinsa na samun karuwa da abokin mu sadauki yayi, bayan ya gama sai kuma ya zaro takarda daga cikin aljihunsa ya fara bayani da cewa..


Yanzu zamu fara kiran babban abokin ango da kuma babbar kawar amarya, yana zuwa nan a zancensa sai kawai yace muna so Abdulraheem yusuf daga gurin ango ya fito sai kuma husna daga bangaren amarya...


Gabana ne na faraji ya yanke ya fadi sai kuma zuciyata ta fara kwakwkwaran bugu kamar zata fasa kirjina ta fito waje saboda fargaba sakamakon jin sunan husna da nayi amatsayin wacce aka hadamu tare...


Hakanan na tashi kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, nai duba da bangaren da husnan take naga ta taso tana murmushi hannunta rike da lemon robar...


Abin yayi matukar bani mamaki da naga tana murmushi a haka harta karaso inda nake ta tsaya, na bude bakina zan fara magana tun kafin maganar tawa ta fito nai saurin rufe bakina sakamakon sassanyan ruwan lemon daya sauka a fuskata...


Na dubi jama'ar dake wajen abokaina da kuma abokan amarya naga adama ta dora hannunta akanta da cikin mamaki da irin 

abinda taga kawarta tayimin, na kuma maida dubana gaban rigata wanda ya jike sharkaf da ruwan lemon sannan na dubi husna naga ta dauke kanta daga gareni kamar wacce ba itace tamin wannan irin wulakancinba...


Murmushi kawai nayi sannan na koma gurin zamana na zauna nama fasa maganar...


Murmushi kawai husna tayi lokacinda taga na koma na zauna sannan ta bude zazzakar muryarta ta fara magana ba abinda ya dameta kamar ma ba ita bace ta jikeni da ruwan lemon ta fara da cewa duk wata godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai mamallakina kuma mamallakin kawata khadija da kuma ango sadauki, haka kuma shine ya mallaki manyan abokan ango irinsu mubarak dan fulani harma da dan matashin saurayin can dake zaune wato Abdulraheem tana maganar tana nuni da hannunta inda nake tana murmushi

Zanci gaba

Comments