Min menu

Pages

Ko gaskiya ne za a daina haska film din labarina a tashar arewa24

Ko gaskiya ne za a daina haska film din labarina a tashar arewa24Tun a wancan satin ko kuma makon jiya aka kammala nuna karshen zango na uku na shirin Labari na da ake haskawa a tashar Arewa24, wanda aka dinga jiran ci gaba da haska zango na gaba na shirin daya mamaye zukatan masu kallo.


An saba haska shirin duk ranar Litinin, to sai dai ana zargin cewar an sami matsala a tsakanin mahukunta tashar Arewa24 din da mamallaka shirin Labarina, mai dogon zango, har ake ganin ta iya yiwuwa ma a sauya tashar haska shirin zuwa wata tashar a maimakon tashar Arewa24 da aka saba haskawa.

             Wani sirri

Lallai dole akwai wani boyayen lamari da ya faru kan dakatar da dora sabon shirin ranar Litinin, din  tare da fitarwar dena haska shirin a ƙuraren lokaci.

                  Wasu hujjoji

Hujjojin suna da tarin yawa, Mashiryin shirin da sauran masu ruwa da tsaki ciki harda mai rubutun ƙagaggen labarin Ibrahim Birniwa, basu bayyana zaa tafi hutu daga haska shirin ba sai jiya Litinin kuma ya rage saura Minti bai fi 20 a fara haska shirin ba suka sanar da cewar baza a ci gaba da haska shirin ba a jiya.

           Sanarwa daga daraktan shirin

Har ila yau sanarwa da Aminu Saira, ya fita ta bayyana cewar baza a ci gaba da haskawar ba kuma babu tabbataccen lokacin da suka bayyana na lokacin ci gaba da haska shirin sai dai sun cewa idan lokaci yayi zasu bayyana tashar da zaa ci gaba da haska shirin da kuma lokacin fara haska shi.

                      Maganar mutane

Ana zargin an sami dan rashin jituwa tsakanin tashar Arewa24 da masu ruwa da tsaki kan shirin Labarina, mai dogon zango wanda hakan ya saka dole aka dakatar da haska sabo, aka dauko tsohon tun daga farko aka saka saboda cece-kucen mutane.


Har ila yau wasu masu nazari sun zargi cewar kamar masu tashar AREWA24  sun fi amfana da tagomashin shirin a maimakon masu daukar shirin, hakan ya saka zaa koma kallon shirin a YouTube kawai a maimakon a Talabijin.


        Tashar da za ana dora Shirin

Tashar saira movie itace tashar da ake tunanin za ana dora shirin domin yanzu anan suka fara dora tallar wani bangaren na shirin
Comments