Min menu

Pages

    Bakin zalunci




Bulagul ansar gari ne dake can gabas da birnin misra, mutanen dake zaune cikin garin sun kasance musulmai wanda suka suka rike addinin musulunci da hannu bibbiyu. Wannan yasa suke zaune cikin kwanciyar hankali walwala gamida kaunar juna, a dukkan al'amuransu na rayuwa suna yinsu ne bisa koyarwa irinta addini kama daga kan yadda suke gabatar da rayuwarsu zamantakewarsu da dai sauran al'amura.

             Bangaren sana'a

Noma da kiyo sune mutanen wannan gari suka rika amatsayin hanyoyin dogaro dakai na yau da kullum wanda suke ci su kuma sha daga garesu, a wani fannin kuma mutanen wannan gari sun dauki farauta amatsayin babbar dabi'a da kuma ta zama tamkar al'ada kasancewar akwai manyan dajika da suke da fadi kuma suka yiwa garin na Bulagul ansar kawanya tako wane bangare hakan yasa duk wani matashi dake garin zaka sameshi yana farauta , kai ba matasa kadaiba hatta jaruman yan matan da suka yadda da kansu suma zaka samesu suna zuwa farauta tare da kamo manyan tsintsaye da kuma manyan dabbobi  masu hatsarin gaske, hakazalika wannan fanni ya zama tamkar wata hanyar debe kewa da mutanen wannan gari suke amfani da ita don haka tsarin yin farauta a garin bulagul ansar ya jawo samuwar zunzurutun matasa da yan mata gami da tsoffin jarumai  masu dakawa maza gumba a hannu wanda kuma suka ga jiya suka san yau.  Duk da kasancewar garin bulagul ansar ba wani katon gari bane amma yanada kasuwa mai matukar girman gaske da tayi ukun garin a girma da fadi wacce ake zuwa daga nahiya nahiya da kuma manyan kasashen duniya domin sayan kayan abinci da kuma safarar dabbobi domin albarkar da Allah yayiwa wannan dan karamin gari da abubuwan da suke nomawa na abinci da kuma kiwon dabbobi, ita dai wannnan  kasuwa tana cine duk bayan wata daya wanda a cikintamanyan fatake da suka tumbatsa a duniya ta fanni fatauci suke mata tsinke  ta ko'ina har tsawon kwana goma sannan kowa yake watse sai k wani watan. A tarihin wannan kasuwa ta garin balagul ansar ba'a taba samin wani bafatake da ya sayi kaya daga cikin wannan kasuwa ba sannan ya koma kasarsu ya sayar dasu kuma ya fadi ko kuma ace baici riba mai  yawan gaske ba.shi yasa attajirai da dama suka camfata kuma suke kiranta da suna kasuwar arziki.


         Wani abin birgewa

 Haka kuma wannan kasuwa ta arziki shahara da tumbatsar da tayi saida yasa sarakunan duniya da dama suka nuna sha'awarsu tasu mallake wannan gari na balagul ansar ya koma karkashin yankinsu amma sai abin yaci tura domin daga an sami wani babban sarki ya taso da zummar mallake wannan gari sai kananun sarakunan da basu da karfin mallakar wannan waje su kadai ta hanyar yaki saisu taru suyi caa a kansa su kalubalanceshi idan kuma yaki hakura sai su taru su murkusheshi ta karfin tsiya saboda suna jin tsoron garin ya koma karkashin wata kasa ko wani sarki ya toshe musu hanyoyin da suke samin abincin da suke saya da sauki sannan kuma haraji dole ya kara hauhawa domin samin kudin shiga sabanin  garin balagul ansar dake karbar haraji dan kadan daga hannunsu don haka kowane sarki ya hakura yana ji yana gani  ya kyale wannnan gari kai koda ma ace wani sarki yana da ra'ayin hakan baya taba yarda ya fitar da kwadayinsa a fili gudun kada sauran takwarorinsa sarakuna suyi amfani da wannan dama su yakeshi su rabashi da mulkinsa gaba daya wannan daliline sai yasa gari yakecin gashin kansa ba tare da ya kasance a karkashin mulkin wani sarki ko wata kasa ba. 


Zanci gaba sannan idan kuna son ganin cikakken bidiyon saiku shiga nan





Comments