Min menu

Pages

Akwai iyuwar WhatsApp zai daina a wasu wayoyin cikin wannan shekarar.

Akwai iyuwar WhatsApp zai daina a wasu wayoyin cikin wannan shekarar.

 Cikin kwanakin nan muka samu labarin kamfanin Whatsapp zasu cire wasu wayoyin daga jerin masu Amfani da manhajar tasu.

       Menene WhatsApp

WhatsApp sun sanar da cewa mashahurin Application dinsu na sada zamunta ze dena aiki a cikin wasu wayoyi masu yawa a cikin shekarar nan da muka shigo 2021.

     Jerin wayoyin da zai daina aikin

 wayoyin da ze dena aiki a cikinsu sune wayoyin da suke aiki da tsohon operation system daga kan android har iPhone sannan kamfanin ya fadi sunan wayoyin da whatsapp ze dena aiki a kansu.

             Gasu kamar haka

Whatsapp ze dena aikine a wayoyin android daga kan 4.0.3 zuwa kasa da kuma wayoyin iphone da suke aiki da tsarin ios 9 zuwa kasa saboda whatsapp yayi bayani kan cewa ya kamata mutum ya mallaki wayoyin zamani saboda ya morewa dukka tsarukan da application din zezo dasu.

            Sanarwa daga kamfanin 
Kamfanin whatsapp sun bada sanarwa game da wanda suke amfani da wayar iphone ya kamata ayi update din wayoyin iphone4, iphone5, iphone5s, iphone6, iphone6s zuwa update na sama da 9.

                            

                             Misali

Kamfanin ya bada misali da kadan daga irin wayoyin android da zasu dena aiki da manhajar tasa masu Android 4.0.3 misalin lg optimus, htc desire 9, motorola droid razr 9.


Idan kana son duba version din wayarka

Zaka shiga setting>about>version anan za kaga wanne version kake dashi.

Comments