Min menu

Pages

Game da shari'ar su Dangote. Wa kotun America tace da budurwar Dangote tayi kafin cikar kwana ashirin

Game da shari'ar su Dangote.


Wa kotun America tace da budurwar Dangote tayi kafin cikar kwana ashirin.Wata kotu dake America ta kira budurwar da ta bayyana photunanta da attajirin dan kasuwar nan wato Aliko Dangote data bayyana gaban kotun domin ta kare kanta bisa kazafi ko kuma bata suna da tayiwa dan kasuwar.

A bayar bayan nan wasu maganganu sukai ta yawo a kafafen yada zumunta inda wata budurwa ta fito tana yada wasu photuna wanda take tare da attajirin nan Dangote har take cewa shi saurayinta ne kuma take ikirarin sunyi da ita zaina bata miliyoyin kudi duk wata.

Ta fadi abubuwa masu abubuwa akan cewa itace silar faruwarsa, sannan inta dora photon tana tagging din wata kawarta wanda itama tace tsohuwar budurwar attajirin ce.

To saidai mutane da dama basu ji dadin wannan abinda matar ta aikata ba har hakan ya jawo maganganu masu yawa, wasu ma na ganin tayi haka ne kawai domin ta bata masa suna, dan haka suke cewa ya kamata a hukunta matar domin wasu gani suke photunan da matar ta dora ma kawai editing akayi domin ba nasa bane.
To shima dai dan kasuwar ba tsayawa yai ba saida ya garzaya kotu domin abi masa hakkinsa na bata sunan da tai masa a cewarsa.

To saidai dama tun farko budurwar tace tanada dukkan yarjejeniyar da sukai da mai kudin a rubuce a yadda ta wallafa a shafikanta na sada zumunta.

Aliko Dangote dai dan kasuwa ne wanda a yanzu yake jan ragamar wanda yafi kowanne mutum kudi a fadin kasarnan Nigeria dama Africa baki daya.

Comments