Min menu

Pages

   Daren farko 2Ranar wata asabat da yammaci ranar da aka daura auren sadauki da kadija, bayan mun dawo daga wajen daurin aure sai kuma kai tsaye muka wuce gidan angon dan mu fara shirye-shiryen zuwa daukar amarya...


Motocin abokan angon guda talatinne da muka tanada dan zuwa daukar amaryar kusan kowacce mota akwai salon kidan da yake tashi a cikinta...


Kowa daga cikin abokan angon yayi ado na kece raini wanda yake tunanin da wannan adon shima zai yanki sauran mata musamman abokan amarya...


Nima ina daya daga cikin jerin wadanda sukayi irin wannan wankan na kece rainin saidai kuma zakusha mamaki ta hanyar da nabi harna tara kudinda na sayi wadannan kayan dake jikina domin na dade ina taru kafin na samu isashshen kudin da zan saya...


Haka kuma na dade ina tanadi dan jiran wannan ranar dan kuwa na dauki alwashin komai ruwa da iska kuma ko ana ha maza ha mata nima sai nayi budurwa a wannan ranar hakan yasa na nacewa abokina dan fulani akan yaban motarsa shi kuma ya shiga ta mubarak suje daukar amaryar tare...


Haka nan dan fulani ya hakura yaban makullin motar tasa shi kuma ya koma motar mubarak ya zauna..


Kasancewar nine babban aboki a gurin ango SADAUKI sai shima angon yazo ya zauna a daya bangaren na gaban motar domin muje mu dauko masa gimbiyarsa khadija..

Bayan mun danyi wasu shirye shirye sai kawai muka dunguma mu duka muka nufi gidan su amarya...


Ba wata doguwar tafiya mukayiba muka karasa kofar gidan nasu khadija, a cike kofar gidan take da yan mata yara da manya kusan kowa a cikinsu yayi ado na gani na fada...


Kayan dake jikinsu gaba daya iri daya ne face daga kan yan matan har zuwa kananan yara kayan yayi bala'in yi musu kyau..


Muna karasawa muka tsayar da motocin a kofar gidan sannan gaba dayan mu muka fito daga cikin motocin namu muka tsatstsaya a lokacinda ango sadaukin kuma yaci gaba da zamansa a cikin motar yaki fitowa...


Na juyo na dubi sadaukin nace haba malam ya munzo kofar gidan kuma zaka tsaya kaki futowa...


Ango sadaukin ya dubeni yayi dariya sannan yace eh naji dai aini na zama babban mutum tunda nayi aure na fika matsayi ko a yanzu...


Na dubeshi nayi dariya sannan nace naji angogu dan kuwa kaiba ango bane tunda har yanzu ba'a kaima matar taka gidaba nima nace dashi...


To yanzu mun dunga tsayawa anan kenan baza  ku kira mana ita kuce gamu munzoba ko saimun shiga gidan mun fito dasu mubarak da dan fulanine suka fadi wannan maganar a tare lokacinda suka karaso inda muke  


Na dubi ango sannan na dubi su mubarak da dan fulani nace dasu wallahi nima maganarda nake tayi masa kenan yanzu, gashinan kuma ya sani a gaba sai wasu maganganu yakemin yana dariya..


Angon ya dubemu sannan yace to yanzu ya kukeso nayi kenan?


Malam ka kira babbar kawar amarya kace mata gashinan munzo su muke jira kaga sasan munanan a waje nace da sadaukin..


Lah rufamin asiri ni na kira husna so kake ta dameni da surutu kenan ta hanani sakat ango sadauki ya fada


to yanzu ya kake so muyi ko so kake muyi ta zama anan su basuma san mun karasoba na fada...


Gaskiya nikam bazan kira husna ba tazo ta dameni sai dai idan na baka numberta ka kirata kace mata gamu munzo muna jiransu a kofar gida sadaukin ya kuma fada yana kallona..


Cikin bacin rai na dubi ango sadaukin sannan nace dashi ina wayar da zan kiratan ko ka sayamin waya da har zakace na kirata nace dashi..


Yi hakuri sarkin talauci ashe fa kai yar wayarma baka da ita yanzu ko sadaukin ya fada lokaci guda suka sa dariya suda sauran abokan namu..

To bari na kirata da tawa wayar saina baka in yaso kai sai kuyi maganar da husnan ina nufin kawar amaryar sadaukin ya fada lokaci guda kuma ya dauko wayar tasa da take a ajiye a gaban motar..


Yauwa yanzu kayi magana ta sauraro abokina, kirata kawai ka bani na tsarata nace da sadaukin lokaci guda mukasa dariya harda tafawa...


Gashi ta shiga sai kamata maganar idan ta dauka sai dai kasan salon maganar da zakai mata domin yarinyar yar gadarace saima ta gadama zata ci gaba dama magana idan har taji bani bane dan kuwa yarinyar tana takama da kasancewarta yar masu kudi sadaukin ya sake fada...


Nai saurim amsar wayar a hannun sadaukin na kara a kunnena, kana magana da husna isma'il naji wata hadaddiyar murya ta ratso ta cikin salular ta doki kunnena...


Kirjina naji ya buga da karfi sannan na bude baki zanyi magana a lokacin naji bakina ya fara sarkewa hakan tasa nai shiru...


Hello ango mijin amarya ya kai shiru naji muryar ta sake fada ta cikin salular dake hannuna..


Nai sauri na dawo daga suman tsayen da nayi sannan nace ba ango sadaukin bane babban abokin angon ne ma'ana Abdulraheem yus...


Nai saurin tsuke bakina tun kafin na karasa maganar da zan fada sanadin jin muryarta ta fara surutu da cewa to kuma malam tun dazu muna zaman jiranku amma kun sharemu ko kuma so kuke ku bata mana rai mu hana amaryar tarewa...


A'a ayi hakuri babbar kawa mu bamu isa mu bata muku raiba a irin wannan lokacin dan kuwa bamu so kuyi fushi damu, na fada lokaci guda...


To idan kuwa hakane kuyi sauri kuzo ku dauki amaryarku husna isma'il ta sake fada ta cikin wayar...


Kwantar da hankalinki sha ruwan sanyi babbar kawa na fada ta sigar tsokana a tunanina zaisa ta danyi shiru a maganarda take amma akasin haka sai kawai naji ta dauki wani sabon salon fadan tace kaga malam fadamin dalilin kiranka gareni ko kuma na ajiye wayarka dan kuwa na fara gajiya da wannan zancen naka...


Yi hakuri babbar kawa dama ba komai yasa na kiraki ba sai dan kawai na fada mikine cewar mun rigada mun iso kofar gidan dan kuwa ku kadai muke jirama a yanzu haka nace da ita...


To ai saika fadamin tun wuri baka tsaya kana wani batamin lokaci ba dan kuwa bakasan abinda nakeba na bari husnan ta sake fada cikin bacin rai sannan tace ku jiramu gamunan zuwa, tana fadar haka sai kawai ta kashe wayar bata jira taji abinda zan sake cewa ba...


Su ango sadaukin da suke gun suka bushe da dariya sakamakon shirar tamu da sukaji...


Kai amma yarinyar nan ta iya wulakanci kaji irin maganarda takeyi dan fulani ya fada yana dariya...


Dama dai ta hadu itama kamar yadda naji muryarta take idan itama haka take to aradu za aga kyakkyawa mubarak ya tsoma baki a maganar tamu...


Har naji yarinyar ta kwantamin a raina wallahi na fada ina kallon abokan nawa da kuma ango sadauki..


Ai kuwa tafi karfinka abdul dan kuwa yarinyar yar manyan mutane ce masu ji da naira kai kuma kaga yadda kake baka da komai sadauki ya fadamin..


Uhm karka damu abokina shi so babu ruwansa da matsayi dukiya mulki ko kuma wani abu na daban, nidai idan na samu ta amince dani to kuwa tayimin komai nace da sadaukin lokaci guda...


Abokina kenan, ni gani nake matan yanzu babu wani abinda suke bukata a gun namiji kamar kudi duk kuwa da cewar nasan halin husna kudin mutane basa rufe mata ido saboda itama tasowa tayi ta ganta cikin kudi, to sai dai gani nake ba lalle bane taso talaka irinka ba dan kuwa yarinyar bata saba da wahala ba, sadauki ya fadamin lokacin da ya fito daga cikin motar gamida dafa kafadata...


Karka damu abokina nidai nasan ba wata damuwa bace idan har ta amince dani komai zai zama normal daga karshe nace da abokin nawa ango sadaukin...


Har mubarak ya bude baki zaiyi magana yai shiru sakamakon gudar da mukaji ta taso daga kofar gidan ta nufo inda muke tsaye...


Nai saurin juyawa na kalli kofar gidan naja da baya da sauri na kalli ango sadaukin sannan nai masa nuni da inda jajayen yan matan suke nace wacce ce husnan a cikinsu


zanci gaba

Comments