Min menu

Pages

Birthday din RararaDauda kahutu rarara yayi bikin zagayowar ranar haihuwarsa jiya inda taron ya samu bakuncin mutane masu matukar yawa ciki kuwa harda taurarin da suke fitowa a cikin fina finan hausa sannan harda manyan jagorori ma'ana masu bada umarni da kuma masu daukar nauyi na fina finan hausa.

Mutanen da suka halarci bikin.Daga nesa zaka hango irinsu Abubakar bashir mai shadda da sauran mutanen masana'antar na kannywood cikin farin ciki da annashuwa suna taya abokin nasu kuma ubangidan wasu da yawa daga cikinsu murna na zuwan ranar haihuwar tasa.

   Waye Dauda kahutu rarara
Kowa dai yasan dauda kahutu rarara indai dan nigeria ne kuma dan arewa saboda sunan da yayi a wajen wakokin siyasa dana biki harma dana sarauta saidai yafi bewa wakar siyasar karfi fiye da sauran wakokin nasa nesa ba kusa ba.

Dauda kahutu rarara mawakine da ya jima tauraruwarsa na haskawa saboda kwarewar da yayi wajen iya tsara baituka da wasa duk wani da yake yiwa waka musamman shugaban kasar nijeria muhammad Buhari da sauran wasu manyan mutanen..

       Alakarsa da abokan aikinsa

Sannan dauda kahutu rarara mutum ne mai kyautata alakarsa da sauran abokan harkarsa da suke aiki tare domin ko kwanaki yayi kyautar motoci masu yawa ga wasu daga cikinsu yayinda a yan kwanakin nan ya sake gwangwaje wasu da sabin kyautuna na motocin inda har tijjani asase shima ya samu tasa.
Saidai har yanzu yan Nigeria na zaman jiran ya sake musu wakarsu da suke ikirarin sun tura masa kudi domin yayi musu kamar yadda mawakin ya fito ya nuna cewa zaiyi wakar ta baba Buhari ga talakawa saidai bazai rerata ba sai har kowa ya tura masa dubu daya dalilin da yasa yace haka kuwa saidan maganganun da ake tayi cewar farin jinin shugaban da yake wakewa ya ragu, shi kuma dan ya nuna musu cewar har yanzu farin jinin shugaban yana nan shine yace su tura masa wannan kudin.

Har yanzu dai babu wani mai masaniyar yaushe mawakin zai saki wakar tasa.

Comments