Min menu

Pages

  Bakin zalunci 2



Garin shi kadaine gari na musulmai a kaf fadin lardin wannan yasa basa karkashin ikon wata kasa ko wani sarki na daga daulolin manyan sarakunan kafirai dake yankin ya zamana su kadai suke gabatar da komai na rayuwarsu ba tare da tunanin komai ba, duk da kasancewar garin kwaya daya tilo na musulmai hakan yasa suke yawan samun kawowar farmaki da sumame na daga wasu daga cikin manyan sarakunan dake yankin domin ganin sun dawo da garin bulagul ansar a karkashin ikonsu saboda albarkar kasar noma da kuma yalwar arzikin dake shimfide a garin, amma cikin ikon ubangiji har yanzu babu wani daga cikinsu daya samu nasarar yin hakan.

An kawata garin da manyan gine gine irinna  wannan zamanin, sannan ko ina ga furanni kala-kala da futulu masu haske gwanin ban sha'awa da dadin gani, ko ina ka duba a garin zakaga mutane ne suke ta gabatar da al'amuran gabansu cikin kwanciyar hankali babu abinda ya dame su, yayinda jefi jefi zakana ganin mutane cikin shigar yaki akan dokunansu wasu na fita daga garin wasu kuma na shigowa dauke da abubuwan da suka farauto wasu  tsintsaye ne marasa rai zaka gansu wani sashe na jikinsu ya fito daga jakar dake sakale a jikin mafarautan lokaci-lokaci kuma zakaga wasu suna janye da kananun dabbobi irinsu gada barewa wanda suka kamasu da ransu a farautar da suka fita..

Garin a zagaye yake da wata katanga mai matukar girma da tsayi hakan yasa  manyan kofofi  biyu  ne da garin, daya tana bangaren gabas yayinda dayar take bangaren yanma sai kuma yan kananan kofofi guda biyu dake bangaren kudu da arewa, mafi yawanci wannan kananan kofofin mutanen dake garinne sukafi yin amfani dasu wajen shige da ficensu na yau da kullum yayinda manyan kofofin kuma mutanen dake shigowa daga wasu biranen ne suka fiye amfani dasu musamman lokacinda kasuwar garin take ci. Hakan yasa ba'a fiye amfani dasu ba kusan kullum suna kulle kuma amfi basu tsaro domin a kalla zaka samu jarumai wajen guda dari suna gadin kowacce kofa.

Sarki HASANUL ANSAR shine sarkin dake sarautar garin bulagul ansar kuma yana gabatar da mulkinsa bisa adalci da kyautatawa wannan yasa mutanen dake garin suke matukar nuna  so da kauna a gareshi domin bashi da girman kai ko nuna isa sannan bai dauki duniya a bakin komai ba, domin sau tari abinci ma tare da fadawansa da suke tare a fada suke ci sannan idan dare yayi lokacin da kowa yake a gidansa yana hutawa shi kuma a lokacin yake daurawa dokinsa sirdi ya hau yana zagayawa layi layi saiya shafe wajen tsakiyar dare lokacin ya tabbata ba wata matsala sannan yake komawa cikin turakarsa ya kwanta, sannan in gari waye ya fito fada yakan tambayi mutane matsalolinsu a lokacin duk wanda yake da matsala ko damuwa yakan fada ba tare da damuwar komai ba, musamman aka ware rana ta rabon kayayyakin abinci ga mutane masu karamin karfi da kuma tsofaffi wadanda baza su iya fita su nema ba.

Gimbiya BAHIJJATU HASANUL ANSAR itace diya kwaya daya tilo da sarki yake da ita tun farkon aurensa kasancewar duka sauran yayan daya haifa  sun mutu tun suna kanana wasu ma babu rai ake haifarsu iya Bahijjatu ce kawai ta rage gashi har tsufa ya fara kamashi ba tare daya sake haihuwar wani da ko kuma wata ya ba hakan shine dalilinda yasa sarkin ya dauki son duniyarnan ya dora mata ya kasance daidai da kuda baya so ya tabata.

Gimbiya Bahijjatu macece mai tsananin kyau wanda kyan nata yafi karfin na zayyana muku shi domin a tarishi tun kafuwar garin bulagul ansar ba a taba haihuwar mace mai kyau da ta kama koda rabin kyawun gimbiya bahijjatu ba domin tun tana yarinya karama batafi shekara uku ba lokacinda sarki Hasanul ansar  ya fara fita da ita zuwa fada, manyan masu kudi gamida fadawan dake fadar suka fara kamun kafa ga sarki akan idanta girma suna so a bewa yayensu aurenta, domin wata rana har sa'insa aka danyi tsakanin wazirin garin da kuma mai rike da mukamin GADO DA MASU na birnin akan kowa ya nuna lalle saidai dansa ne zai aureta idan ta girma, da sarki Hasanul ansar yaga haka sai yace dasu shi bazai yiwa kowa a cikinsu alkawari ba saidai su bari idan ta girma ta zabi wanda take so da kanta..

Lokacinda gimbiya bahijjatu ta cika shekara goma sha takwas sai kyan nata ya dada karuwa fiye da kima domin mutum bai isa ya kalleta sau daya ba ba tare daya sake son ya kuma ganinta ba, duk lokacinda ta fito yawan shakatawa kuwa ko kuma ta shigo cikin kasuwa to ranar mutane barin komai suke su koma kallonta, daga karshe dai dole in tana so ta shiga kasuwa ko kuma taje wani guri a cikin birnin dole saita badda kama take samu ta fita..

Amma duk da haka labarin kyawunta ya game ilahirin garin dama sauran biranen dake can nesa da garinna bulagul ansar  hakan yasa samari da dama dake garin suka rika meko kokon baransu gareta na son ta amince musu amma ina ita a zuciyarta tanada wani kuduri wanda tace saita samu mai irin wannan abun tukun zata aura..

Al'adar gimbiya bahijjatu ne duk safiya bayan rana ta dan fara zafi takan fito daga cikin gidan sarautar ta haye wani ingarman dokinta sannan ta rufe fuskarta ta fita zuwa dajin dake zagaye da birnin na bulagul ansar domin ta iyo farauta, yauma kamar kullum bayan ta gama shiryawa sai kuma ta kama farin ingarman dokinta ta hau sannan ta rufe fuskarta ta nausa cikin jejin har tayi tafiya me nisa ba tare data tsaya ba, haka taci gaba da nausawa cikin jejin babu tsoron komai harta kawo gurinda wasu manyan duwatsu suke masu matukar girma, turus tayi ta tsaya lokacinda wani katon zaki ya biyo wata gada da gudu saida suka zo daidai kusan inda gimbiya bahijjatu take sannan gadar tai tsalle ta shige wani kogo dake jikin daya daga cikin dutsunan, nan fa zakin ya tsaya yana haki sannan ya juyo suka fara kallon kallo shida gimbiya bahijjatu. Ba a dau wasu dakiku masu yawa ba zakin yai ihu da gurnani sannan ya daka tsalle sama da niyyar ya gama da gimbiya bahijjatu ta farat daya..

Cikin tsananin zafin nama gimbiya bahijjatu ta daka wani wawan tsalle ta bar kan dokin da take kai sannan ta fara juyawa a sararin samaniya suka hadu da zakin a sama suka mangaji juna sannan suka fado kasa gaba dayansu, zakin ya sake gurnani yaja da baya sannan ya danno da gudu da niyyar ya danne gimbiya bahijjatu cikin sauri ta goce sannan ta daki zakin da kafofinta yaje ya dungura.

Gimbiya bahijjatu tai saurin jawo wata doguwar wuka dake daure a jikin damararta ta jefawa zakin tun karfinta, wukar ta tafi da gudu kamar kibiyar da aka harbo a cikin baka ta cake a jikin wuyansa, zakin yai kururuwa mai tsananin karfi saboda zafin shigar wukar da yaji dajin ya amsa kuwwa tsuntsayen dake saman bishiyoyin dake dajin suka tashi a guje, zakin ya sake kugi da gurnani mai matukar firgitarwa sannan ya danno da gudu jini na zuba a inda wukar ta soke shi, ya daka tsalle ya bangaje gimbiya bahijjatu, ta tafi taga taga zata fadi amma ta turje, zakin ya sake tasowa da gudu ya danne ta sannan yakai mata raruma da hakoransa da niyyar yaga makogoronta, cikin tsananin jarumta tasa hannunta ta rike bakin zakin bata bari ya kafa mata hakoranba suka fara birgima ita da zakin amma har yanzu babu wanda ya samu nasara a tsakaninsu da kyar gimbiya bahijjatu ta samu ta ture zakin daga kanta ya fadi can gefe sukai rige rigen tashi sannan kowannensu yaja baya suka tsaya sukai cirko cirko na dan lokaci zakin ya karci kasa da kafofinsa na gaba yai gunji da gurnani  dajin ya amsa kuwwa ya sake daka tsalle ya iyo kan gimbiya bahijjatu  kafin zakin ya isa ga inda take ne ba zato ba tsammani wani mashi yazo da tsananin gudu ya cake a cikin zakin har saida ya fito ta daya bangaren zakin ya kwala kara mai tsiwa a saman sannan ya fado kasa baiko shura ba..

Zanci gaba

Comments