Min menu

Pages

   Daren farko 1      Kashi na farko


Kaina ne ya sara da karfi numfashina ya fara sarkewa idanuna ya fara lumshewa wani jiri ya fara daukata naji na tafi luu zan fadi nai sauri na dafa bangon dakin da hannuna sakamakon ganinta da nayi a kasa mala mala cikin jini...


Lokaci guda idanuna suka zaro lokacinda naga irin mummunan yankan ragon da akai mata kanta yana kallon rufin dakin gashin dake kanta ya baje duk jini ya batashi...


sannan kuma naga wukar da aka yankata da ita a yashe a kusa da ita sai sheki da walwali take...


Jikina na rawa na samu na tashi daga zaunen da nake gamida fige katuwar rigar tawa wacce ta jike sharkaf da gumi kamar wanda yayi aikin karfi, sannan  na karasa gunda take kwance na durkusa na kalleta naga ko alamar motsi batayi...


nan take hawaye ya fara kwaranya a cikin idanuna...


Waya kasheki husna? 


Nace da karfi, haba husna ya zakimin haka ya zaki tafi ki barni, yaune fa DAREN FARKO na aurenmu ni dake...


Ya za ayi ki mutu ki barni? Ya zakimin haka husna? Ki sani auren soyayya mukai ni dake yau kuma kika tare a gidana kuma yau shine DAREN FARKO na amarcin mu..


Lokaci guda naji wani sassanyan hawaye ya fara kwaranya daga cikin idanuna nasa hannu na dauki wukar da aka yanka husna da ita na dagata sama na fara jujjuyata a hannuna ina kuka...


Yaya Abdul a dawo lafiya, naji kalamanta na karshe suna kai kawo a cikin kaina


Lokaci guda tunanina ya fara sauyawa yana komawa baya har zuwa farkon haduwata da husna wadda take kwance a gabana yanzu cikin jini kamar ba itace wadda muka rabu da ita yanzu ba lokacinda zan raka abokaina su sadauki zuwa waje... 


FARKON LABARIN


Bazan taba iya manta farkon haduwata da itaba kamar yadda bazan taba manta ranar auren abokina abubakar sadauki ba wanda shine ummul aba'isin haduwata da ita...


Ranar wata asabat da yammaci ranar da aka daura auren sadauki da kadija, bayan mun dawo daga wajen daurin aure sai kuma kai tsaye muka wuce gidan angon dan mu fara shirye-shiryen zuwa daukar amarya...

Zanci gaba

Comments