Min menu

Pages

Cikin kwana daya Dangote yayi asarar dollars miliyan dari tara

Cikin kwana daya Dangote yayi asarar dollars miliyan dari tara 



Mai kudi Aliko Dangote ya rasa kimanin Naira biliyan 350,100,000,000 a makon jiya Ad -Attajirin da ya mallaki $18.4bn a farkon mako, ya kare da $17.5bn a cikin asusu.

Dangoten ya sauko a jerin Attajiran Duniya daga na 106, ya koma har na 114.

Shugaban kamfanin Dangote Industries Limited, Aliko Dangote, ya ga dukiyarsa ta sauka a ranar Juma’a, 8 ga watan Junairu, 2020.

 

Wata jarida tace hakan na zuwa ne bayan kasa da kamfanin Dangote ya yi a kasuwar zuba hannun jarin Najeriya watau NSE. 

 Bloomberg Billionaires Index wanda ta ke tattara alkaluman attajiran Duniya ta nuna Alhaji Aliko Dangote ya rasa Dala miliyan 900. 

Dangote wanda ya mallaki $18.4bn a ranar Alhamis, ya wayi gari ranar Juma’a da $17.5bn a asusunsa. 

 Dangote da sauran manyan Attajiran da suka fi kowa arziki a Afirka Da wannan canji da aka samu, Dangote wanda shi ne attajiri na 106 a kaf Duniya kafin yanzu, ya koma na 114 a sabon jerin da aka fitar. 

Bayan ya samu karin Dala miliyan 600 a farkon kwanakin 2021, Aliko Dangote ya gamu da wannan babbar asarar cikin sa’o’i 24. 

Abin da hamshakin Attajirin Nahiyar Afrikan ya rasa a wannan takaitaccen lokaci a darajar kudin Najeriya, ya haura Naira biliyan 350. 

A tsakiyar Disamban 2020, dukiyar Dangote ta yi wani tashi daga Dala biliyan 15.5 zuwa dala 17.8, sama da Naira tiriliyan shida kenan. 

Ya da ya iya shiga jerin Attajirai 500 na farko da ake da su a Duniya, na farko a fadin Afrika. 

An haifi Aliko Dangote ne a Kano sannan yanada kamfanoni da dama wasu na fulawa wasu na suga da dai sauransu.

Comments