Min menu

Pages

Dalilin da yasa film din izzar so yafi kowanne film masoya

 Dalilin da yasa film din izzar so yafi kowanne film masoyaShin me yasa film din izzar so yafi dukkan fina finan wannan lokacin?


           FARKON SHIRIN

Tun bayan bayyanar wani kayataccen Shirin film mai dogon zango wato izzar so mutane da dama suke ta tofa albarkacin bakinsu akansa suna nuna jin dadinsu.

          KADAN DAGA CIKIN LABARIN

A farko an nuna wata yar gidan wani mai kudi ce take rike da kamfanin mahaifinta hakan yasa taki sakin fuska ga duk mutanen dake karkashin kamfanin ya zamana bata son raini ita kullum saidai a girmamata saboda tana ji da izzar kamfanin na mahaifinta ne kuma itace babba a ciki..


Ana haka sai wani sabon ma'aikacin ya bayyana mai gaskiya da rukon amana wato Umar Hashim, wanda shi yace sam bazai juri wannan izzar da take nunawa ba.

Tun daga nan sai takun saka ya shiga tsakaninsa da ita take ta neman hanyar da zata wulakantashi ta tozartashi amma Allah bai bata nasara ba saboda yawan addu'ar da yake yi idan zai gabatar da komai nasa.


ABUBUWA GUDA BIYU DA SUKA SA SHIRIN YA ZAMA NA DABAN SUNE

1.yadda ya ga matawalle ta dunga kirkirar masifu domin lawan Ahmed ya sami matsala amma bai samu ba ita kuma taki hakura.

2.yadda lawan Ahmed yakeiya kalubalantar shugabar kamfanin cikin izza tare da nuna gaskiyarsa.

ABINDA SHIRIN KE NUNAWA

Karshe dai izzar so yana nuni da cewa duk abinda mutum zaiyi ya kasance mai gaskiya sannan yana addu'a Allah zai kareshi a komai yake na rayuwa.

Izzar so ya samu yabo mai kyau wurin

jama'a domin cewa ake babu wani film da aka taba yi daya kaishi..

Lawan ahmad shine ya dauki nauyin shirin nura mustapha waye ya rubuta labarin kuma ya bada umarni..Comments