Min menu

Pages

Duk wani dan Nijar ya kamata yasan wannan (Yaren yan kasar Nijar)

Duk wani dan Nijar ya kamata yasan wannan (Yaren yan kasar Nijar)Shirin mu zagaya duniya da wannan gidan hake kawo muku yau ma munzo muku da wani mahimmin batu akan kasar Nijar, batun kuwa ba komai bane face mu sanar daku yare nawa ne a kasar Nijar.

Yaren kasar Nijar dukansu wanda bincike ya nuna su goma sha daya ne wanda yaren France kusan shine ya zama yaren da suke amfani dashi kasancewar kasar France ce ta reneta dan haka suka dauki yaren amatsayin official language nasu, kamar yadda takwararta Nigeria ta riki yaren Englishi saboda suma sun samu yancin kaine daga kasar England.

To saidai duk da haka akwai yaruka kala kala da kasar suke amfani dashi wajen maganganu da isar da sakon su har wajen guda goma sha daya (11)

- Hausa

- Arabic

- Buduma

- Fulfulde

- Kanuri

- Zarma & Songhai

- Tamashek

- Tassawaq

- Tebu

- Gurmanchema

Wadannan sune manyan yarukan da aka fi amfani dasu a kasar ta Nijar bayan yaren da yan kasar ke amfani dashi a matsayin yaren kasa wato France.

√ HAUSA :- Yaren Hausa shine yare mafi girma kuma mafi yawa wanda mutanen kasar suke amfani dashi domin shine ya dauki wajen kaso 55.4% √ SONGHAI :- Bincike ya nuna shine yare na biyu da yafi yawa kasar idan ka dauke yaren hausa domin shine ya dauki kaso 21%√ TAMASHEQ :- Yanada kaso 9.3% kuma duk da haka shine yake a cikin rukuni na uku a jerin yaren dake kasar.√ FULFULDE :- Yaren fulani shine na hudu a manyan yarukan dake kasar ta Nijar kuma yanada kaso 8.5%√ KANURI :- Kanuri shine yaren dake biye da fulfulde a yawa a kasar ta Nijar domin yanada kaso 4.7%√ ARABIC :- Yaren larabci shima na daga cikin manyan yaruka dake kasar Nijar din wanda yake da 0.4%√ GURMANCHEMA :- Shima kai daya suke tafiya da yaren larabci a kasar domin 0.4% ke dashi.√ TEBU :- yaren Tebu shine wanda baikai sauran ba amma dai kansu daya da larabci da kuma gurmanchema domin shima 0.4% ne dashi.Sauran yaren sune ke dauke da sauran kaso 0.1% din.

To saidai dole a samu wasu yarukan dake cikin kasar amma dai babu su a cikin lissafin da aka lissafa.


Domin kalla danna nan


Comments