Min menu

Pages

Daren farko 4

Labarin amarya husna da aka kashe


raina yai bala'in baci da naga wannan sabon salon wulakancin data fara a kaina, lokaci guda soyayyarta da nakeji ta fara rikidewa daga karshe ta koma kiyayya naji hankalina bazai taba kwantawa ba raina bazai taba yin fariba har saina rama irin wannan wulakancin da tamin dole saina fara nuna mata cewa itafa karamar yarinya ce a bangaren iya rashin mutunci...


lokaci guda na tashi daga inda nake nai waje nabar gurin da ake taron...


Ganin hakan da nayi yasa adama tare da mubarak da suke zaune guri daya sukayi saurin tashi daga inda suke suka takemin baya...


Hakuri za kayi malam Abdul da irin halin husna dole sai kana mata uzuri dan wallahi haka take yanzu ba karamin aikinta bane tace duk a wasa ne kawai gwadaka takeso tayi adama tace dani tana kallona...


Mubarak dake tsaye yai saurin duban adama da alamun maki karara a fuskarsa sannan yace gwadawa fa kika ce adama?


Eh kwarai kuwa gwadawa dan kuwa ni nasan halin kawata husna sai tayiwa mutum wani abu da zai bata masa rai daga karshe kuma tazo tace wasa takeyi masa adaman ta sake fada tana wasa da yan yatsun hannunta...


Na dubi adaman lokaci guda nayi wani fatalwan murmushi mai dauke da mugun nufi sannan nace ai kuwa zata san wasa dan kuwa sai na dauki mummunan mataki a kanta saina nuna mata nidin Abdulraheem ne nace dasu ina kallonsu...


Gaskiya wannan kam bai dace a kirashi da sunan wasaba dan kuwa ba haka ake yinsa ba mubarak ya fada..


Gaskiya dai kam husna bata kyautaba amma dan Allah abdul kayi hakuri kuma inaso kiyayyarda kake mata ka juyata ta koma soyayya adama ta sake fada...


Shikenan adama, amma ina so na tabbatar miki da cewa kome husna ta zama a gareni to kuwa nine nan na fada miki saina rama abinda tayimin koda kuwa matata ta zama nima nace da ita...


Murmushi kawai adama tayi sannan tace dama zuwa mukayi mu baka hakuri kafin ita husnan tazo dan kuwa nina sani  zata zo itama dan haka mu zamu koma...


Tana fadar haka sai kawai ta dubi mubarak tai masa murmushi mai dauke da tsantsar soda kauna sannan ta juya domin ta koma haka mubarak murmushi kawai yai a gareni sannan ya take ma adama baya..


Ai kuwa basuyi wata doguwar tafiba sai gasu sun tsaya sakamakon haduwa da sukayi da husnan akan hanya...


Bansan me dame husnan ta fada musuba sai kawai naga sun juyo gaba dayansu sun nufo inda nake a tsaye a jikin motar...


Bata rai kawai nayi na tsaya ina sauraron zuwansu gareni zuciyata cike da bakin cikin abinda husna taimin..


Mene kuma na bata rai jarumin maza? Naji zazzakar muryar husna tana fada lokacin da suka karaso gareni...


Ko kulatama banyi ba saima kawai na sake dauke kaina daga gareta na koma kallon wani bangare na daban...


Dama abdul zuwa nayi na baka hakuri a bisa abinda na aikata a gareka, husna tace sannan taci gaba da bayaninta da cewa ada abdul na dauka hakan dana aikata ba kuskure bane a gareka amma sai daga baya na gane bai kamata nai maka haka a cikin taron nasan nayi kuskure amma kayi hakuri...


Hakan data fada ya dada batamin rai na tuna irin wulakancin da yarinyar nan taimin tun a cikin mota har zuwa lokacin data kwararamin ruwan lemon a fuskata a gaban mutane lokaci guda zuciyata ta turnike da bakin ciki na daga hannuna na shareta da mari tun karfina har saida taje kasa...


Kai abdul meye hakan ai bai kamata dan kare ya cijeka kaima kace saika bishi ka rama ba, bai dace dan husna taima haka kaima kace saika ramaba koba komai ai kaine gaba da ita dan kuwa kaika fita hankali tunda kai na mijine mubarak ya fada da fada fada...


Murmushi kawai nayi gamida shafa fuskata kamar ni aka mara na kalli adama da take tsaye naga tana kallona cikin mamaki duk abinda muke batai magana ba watakila mamakin ganin na mari kawarta husna take...


Na sake maida dubana inda husna take har yanzu tana kasa wanwar hannunta yana dafe akan fuskarta tayi shiru tana kallon kasa..


Nasan nayi maka laifi abdul amma kuma kayi hakuri dan kuwa ni banyi tunanin har ranka zaiyi kololuwar baci haka ba husna ta fada kanta yana kasa..


Abdul kayi hakuri tun tazo da kanta ta nemi afuwa kuwa insha Allahu ya wuce bazama ta sake yima wani abu da zai bata maka raiba na dauka maka wannan alkawarin adama ta saka baki a karo na farko a maganar tamu...


Maganar da adama ta fadamin tasa na sauko daga dokin zuciyar da na hau naji lokaci guda farin ciki ya mamaye cikin zuciyata musamman idan na tuna cewa nima na rama abinda tamin, amma sai kawai na sake bata raina na nuna ban huceba..


Nai nuni da hannuna inda husnan take sannan nace wannan shine karo na farko kuma shine somin tabi a cikin jerin abubuwan rashin mutuncin dana tanada miki dan saikin gane cewa kin taboni saina koya miki hankali na nuna miki ke karamar yarinya ce a cikin jerin marasa mutunci ni kaina maganar da nake fada yau saida ta bani mamaki domin ban taba tunanin zanyi fada irin na wannan ranar ba..


Gaskiya yau kam nasan an bata ran abokina dan kuwa tunda nake ban taba ganin abdul yayi fada irin wannan ba hakan shine yasa nasan gaskiya ranka ya baci to amma tunda ta nemi afuwa a gareka ina ganin kai mata afuwa kawai dan kuwa ta riga ta gane kuskurenta mubarak ya kuma fada...


Nasan ka tsaneni abdul tsana kuma mai yawa saidai ina dada neman afuwarka akan kai hakuri ka yafemin domin wallahi bazan taba gafartawa kaina ba idan har bakamin afuwa ba husna ta fada lokaci guda kuma ta fashe da kuka kamar wata karamar yarinya hawaye ya fara sartu a idanunta yana bin takan yar kyakkyawar fuskarta...


Ni ko kusa ban tsaneki ba dan kuwa banga abinda kikamin har yakai na tsaneki dinba kawai dai na fara rama irin abinda kikamin ne domin kiji koda dadi na fada lokaci guda...


Abdul kenan ai yanzu kan ya dace ka hakura tunda gata da kanta a durkushe a gabanka tana roko da kuma neman afuwa adama ta sake fada...


Na dubi adama sannan na dubi husna da take zaune kanta yana kallon kasa, na taka na karasa inda take nace tashi tsaye husna...


Tai saurin mikewa muka kurawa juna ido nida ita babu wanda ya kawar da kansa har yanzu hawayene yake kwarara daga cikin idanunta, nai saurin zuwa kusa da ita sannan nasa hannuna a cikin aljihu gamida zaro wani dan karamin kyalle na fara goge mata hawayen dake idanunta...


Duk da kasancewar tayi kuka amma saida tai murmushi wanda ya baiyana kyawawan fararen hakoranta sakamakon goge mata hawayen da nayi ko tantama banayi nasan taji dadi har cikin ranta...


Karki damu husna komai ya wuce sai kuma a kiyaye gaba nace da ita...


Kai gaskiya naji dadi wallahi da kuka sasanta kanku domin wallahi kun dace da juna yanzu dai fatana abokin fada zai koma abokin mutunci koma abokin rayuwa na dindindin mubarak ya fada yana murmushi...


Mubarak kenan ai ni nafi kowa ma jin dadi da abdul da husna da suka shirya kaga sai su zama manyan masoya maimakon da da suke matsayin manyan makiya ga junansu adama tace tana kallona...


Gaskiya na gode abdul da afuwar da kamin kuma naji dadi insha Allahu na daina yiwa mutane irin wannan wasan husna ta kuma fada...


To yanzu ina mai taya abokina abdul murnar samun budurwa domin kuwa ya dace ace kunso junanku mubarak ya fada..


Mubarak kenan waye ya fada maka husna zata soni? Ai kaima sanin kanka ne ajin husna yafi nawa ko kusa bankai husna ta soniba nace da mubakar..


Kamar yaya kace baka kai husna ta soka ba abdul adama ta tambaya..


Eh mana saboda nasan husna koba tambaya ta fito ne daga gidan manyan mutane masu hannu da shuni haka kuma gata kyakkyawa kamar balarabiya ga ido hanci gamida dan madaidaicin baki kinga kuwa ai baza ta so talaka irina ba na fada ta sigar tsokana...


Eh gaskiya ba karya kayiba abdul husna yar manyan mutane ce to amma saidai ina so ka gane cewa kudi ko kadan ba shine matsalar husna ba idan harta amince tana sonka to kuwa babu bazata jura ba adama ta sake fada...


Shikenan dai na gane abdul baiso ya budi bakinsa yace yana sona ne amma idan ba haka ba ai shi so ba ruwansa da dukiya kyau ko kuma asali husna ta fada a karo na farko tun lokacinda muka fara shirar tamu...


Ba haka bane husna nace da ita a takaice...


To abdul menene idan ba haka bane husna ta sake tambayata..


Murmushi kawai nayi ban tanka mata ba a maganar da take...


To shikenan abdul ni ina sonka tunda kai baka iya fada husna tace...


Kina sona kuma husna? Na tambayeta ina mamakin abin da ta fada min...


Eh abdul ina sonka kuma har cikin zuciyata kaunarka nake zan aureka husna ta sake fada lokaci guda ta zubamin kyawawan fararen idanunta...


Harna budi baki zanyi magana mubarak yai sauri yasa hannunsa ya rufemin baki sannan ya dubi husna yace shikenan husna mun gode da kaunar da kika nuna a garemu kuma insha Allahu shima abdul din ya amince dake...


Mubarak kenan ai ba shine ya fadi da kansa ba cewar ya amince dani amatsayin masoyiyarsa kaga kuwa aini gani zanyi kamar bai aminta daniba husna ta fada..


Dubanta kawai mubarak yayi sannan yace husna ina so ki gane cewa nida abdul abokaine na gani na fada wanda abotarmu ta karade ko ina hakan tasa nasan abinda yakeso kuma shima yasan duk abinda nake so, bari kiji na takaice miki husna tun daga lokacinda muka je daukar khadija amarya lokacin da yayi magana dake a wayar sadauki ai koshi saida ya yaba miki kuma tun a lokacin yace kin kwanta masa arai kinga kuwa ai dole nace dake ya amince..


Ba abinda husna tace sai kawai ta maida dubanta inda nake sannan ta bude baki da niyyar taimin magana...


Karki damu husna hakane duk maganar da mubarak ya fada miki gaskiya ne dan kuwa tun lokacinda na fara sauraron zazzakar muryarki naji kin kwantamin a rai naji ina kaunarki saidai kuma lokacin da kika fara yimin wannan abin da kika kirashi da suna wasa ne na fara tsorata da lamarinki...


Uhm to naji dadi yayana abdul daka amincemin da bukatata a gareka dan haka sai muyi saurin komawa inda ake taron husna ta fada...


Babu wanda yai mata musu a cikin mu a game da maganar da take sai kawai muka juya muka nufi inda ake taron muna tafiya muna dan shira a tsakanin mu muna dariya kamar ba mune muke ta famar fada dazu ba


muna karasawa wajen muka samu guri muka zauna abin yayi matukar baiwa mutanen dake wajen mamaki hatta khadija da angonta sadauki abin ya basu mamaki nanfa gurin ya kauqe da hewa gamida tafi...


Bayan an gama komai sai kawai muka dauki amarya da kawayenta muka wuce kai tsaye zuwa gidan ango sadauki inda amarya kadija zata tare...


Baya gabatar da komai da ya kamata abokan ango suyi sai kawai kowa ya fara watsewa a lokacin ne nace da husna tazo ta hau motar na kaita gidansu in yaso shi kuma dan fulani sai ya hau ta mubarak, haka kuwa akayi husna ta hau gamida yimin kwatancen inda unguwarsu take da haka har muka karasa bakin kofar wani dankareren gida na gani na fada, hurna taimin umarnin na tsaya a kofar gidan banyi mata musuba kawai na taka birki na tsaya...


Yaya abdul na gode nizan shiga dan haka bani wayarka nasa maka numberta husna ta fada tana murmushi gamida watsamin kyawawan fararen idanunta


kirjina ne kawai naji ya fara bugawa da karfi na dubeta har cikin idanunta sannan nace husna bani da waya wallahi dan a gaskiya kudi ne bani hakan yasa na saidata na cika na sayi wadannan kayan dake jikina ina maganar ina mata nuni da kayan dake jikin nawa...


Baka da waya kuma abdul? Husna ta sake fada da alamar mamaki karara a fuskarta...


Uhm murmushi kawai nayi sannan nace kwarai kuwa husna bani da waya barima kiji na fada miki gaskiya ko wannan motar da kika ganni da ita ba tawa bace ta wani abokina ce muhammad dan fulani, na karbi aron tane musamman dan zuwa daukar amarya...


Hm abdul karka damu ai arziki nufi ne na Allah kaima wata rana idan da rabonka sai kaga ka samu husna ta fada har yanzu dai idanunta suna kaina taki kawar dasu..


Murmushi kawai nayi bance da ita komaiba...


Abdul nizan wuce dan haka yaushe zaka dawo gareni...


Kece zaki fada ai husna danni duk lokacin da kika ce nazo zan iya dawowa gareki dan kuwa kunnuwana basu gajiya dajin wadannan zakakan wadannan kalaman naki haka kuma idanuwana basa gajiya da ganin wannan kyakkyawar surar taki nace da ita ina murmushi...


Wannan maganar dana fada ba karamin faranta ran husna yayiba ta dubeni tayi dariya wanda ya tona asirin kyawawan jerarrun fararan hakoranta dimple din dake boye cikin kumatunta ya baiyana a fili sannan tace kaisheka sahibul kalam gaskiya naji dadin wadannan kalaman naka dan haka idan har bazaka damuba kuma ban takura makaba zanso ka dawo gobe...


Babu batun takura a anan gimbiya husna Allah ya kaimu goben ni kuma nayi miki alkawarin zuwa...


Haka mukayi sallama nida husna kowa zuciyarsa a cike da farin ciki gamida annashuwa..


Naja motar nabar kofar gidan ina tafe ina tunane tunanen haduwata da husna na tuna kamar ba ita ce muke fada da ita ba dan lokaci kankani daya wuce amma gashi yanzu ta zamto masoyiya ta hakika a gareni, lalle rayuwa babu ta yadda bata juyawa...


A  haka harna karaso kofar gidan mu tun kafin na bude na fito daga cikin motar na hango dan fulani kamar an cilloshi yana zuwa ko sallama baiyi a gareniba ya hau jaraba da cewa...


Haba malam ya zakamin haka kawai zakaje ka zauna tun dazu ina jiranka zaka zo kaban motata nima ai akwai inda zanje da ita...


Yi hakuri mai arzikin mota nace dashi ina murmushi saboda na riga nasan halinsa abu kadan idan akai masa zai hau mutum da masifa...


Eh naji ni mai arzikin motar ne amma ai duk da haka naima rana tunda na baka kakai wannan yarinyar data zubama ruwan lemon a fuskarka dan fulani ya fada yana huci kamar wani kumurcin maciji...


Kwantar da hankalinka abokina gobe zaka rakani gunta dan kuwa tace naje zance..


Dan fulani ya bata rai da yaji nace za muje gun husna zance ya dubeni yace gunwa za muje zancen ina fata ba yarinyar nan marar tarbiya data zubama ruwan lemo bace?nai sauri na dubeshi da alamun mamaki sannan nace meya faru idan itance?


Babu abinda ya faru kawai dai cema zanyi bazanje gareta ba...


Me yasa baka zuwa gareta dan fulani? Na tambayeshi da alamar mamaki...


Aini yarinyar ta gama sanemin wallahi dan tun daga lokacin data watsama ruwan lemon nan naji na tsaneta kuma kai dinma dan baka da zuciya ne shine yasa harka koma inda take harma kakemin ikirarin kun fara soyayya da ita dan fulanin ya kuma fada...


Murmushi kawai nayi sannan nace gaskiya kanada saurin zuciya abokina kodan kai dan fulani ne shi yasa kake haka...


Kaga malam bani makullin motata in wuce nina gaji da wadannan banzayen maganganun naka marasa tushe...


Banyi masa musuba na mika masa dan makullin motar na koma gefe na tsaya ina kallonsa ya tada motar sannan ya bata wuta lokaci guda yasa mata giya ya fisgeta baiko dubi inda nakeba ballantana har yaga hannun da nake ta famar daga masa...

Akwai ci gaba yana zuwa

Comments