Min menu

Pages

Takaitaccen Bayani akan Apps na Artificial intelligence

ZAKA IYA TAMBAYA KUMA KA SAMUN AMSAR KOMAI TA WANNAN APP ƊIN


Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu ƴan uwa barkanmu da wannan lokaci sannan kuma barkanmu da sake saduwa a wannan sabon darasin  wanda zamuyi bayanin wani muhimmin abu a Technology, wanda ya danganci Artificial intelligence a Turance.

MENENE ARTIFICIAL INTELLIGENCE?

Ma'anarsa a taƙaice shine wato kwaikwayon ɗabi'a( Wato abunda mutane suka ƙera da kansu bawai wanda Allah ya halitta ba).

Wato dukkan wani abu wanda ɗan Adam yakeyi sannan se a ƙirƙiro madadinsa wanda ze maye gurbin harka ya kwatanta wannan aikin na ɗan Adam wataran ma kaga ya fishi.

Amma sedai a gefe guda wasu daga cikin masana suna ganin cewa zuwa da sabon Technology ɗin na  Artificial ze iya kawo tsaiko wajan ayyukan da ɗan Adama yake samu, Saboda gudun mamayewar da Robot ze iya yi a manyan ayyukan da mutane suke samu a guraben aikin gwamnati harma da na Kamfanunuwa.

A gefe guda kuma wannan abun yana da amfani sosai wanda suka haɗa da temakawa ayyukan ofis dama har na gwamnati. A gefe guda kuma wasu lokutan sukan taimaka mana wajan maye gurbin wasu abubuwa da ɗan adama yake buƙata na su taimaka masa a yayin rasa wani sassa na jikinsa.

 BAYAYNIN ESKRITOR

shima wannan wani na'ui ne na bayanin wani Manhaja me aiki irin na Me kama da Artificial wanda ze taimakawa me aiki dashi wajan amsa dukkan wasu tambayoyi na Ilimi da ma harkokin rayuwa, musamman abubuwan da suka shafi harkokin Technology. 

YANDA AKE AIKI DA WANNAN APP ƊIN

Kawai kana buɗe wannan App ɗin bayan ka sauke shi a wayarka zaka danna cikinsa daga baya ze nuna maka wani waje da aka rubuta Continue, bayan ka danna ze kaika fuska ta gaba daga nan zakaga wani waje wanda kanar zakaga ance ka biya, kada ka danna nan kawai zakaje can sama daga gefen hannunka na dama zakaga wata alama ta Cancel (× ) seka danna, kai tsaye ze buɗe maka fuskar da ze baka dama kai rubutu ko kuma kai Searchin dukkan wani abu da kake buƙatar tambaya game da Fasahar zamani ko kuma wani abun da ya danganci tarihi ko kuma ilimi.

Anan kana rubutawa zaka danna Generate text kai tsaye bayan jira na minti guda zakaga ya kawo maka amsar dukkan abunda ka nema.

BAYANIN APP NA BIYU (DIGITAL TASBEEH)
Fikirar wannan manhaja a taƙaice itace a duku lokacin da kake buƙata zakai tasbihi ko kuma wani abu da ya shafi ƙirge gudan  kada ka manta zaka iya ɗakko ta sannan kai amfani da ita.

BAYANIN YANDA ZAKAI AIKI DA APP NA 2 

Bayan ka danna cikin App ɗinka, kawai ze bude maka wata fuska, daga ƙasa zakaga anrubta Continue nanma kana dannawa zakaga ya baka fusakar da zaka dinga danna TASBEEH ɗinka yana lisaafa maka tun daga  1 har zuwa adadin da kake so ka tsaya. Bayan ka tsaya zakaje kai save daga nan ka rubuta sunan kalar zikirin dakai misali " Subhanallah" kai guda 200 kawai zaka rubuta daga nan seka sakashi a jeri yanda idan kadawo zakaci gaba zaka fara daga inda ka tsaya ne a baya.

Idan kanasan sauke ESKRITOR  danna NAN.

idan kanasan sauke DIGITA TASBEEH  danna NAN.

Wannan shine takaitaccen bayanin wannan Apps ɗin da kuma ARTIFICIAL INTELLIGENCE sedai idan kana buƙatar ƙarin bayani zaka iya zuwa Sashin Google kai Searchin domin samun cikakken bayani.

Comments