Min menu

Pages

MUhimman APPS GUDA 5 DA SUKAI FUCE

MUHIMMAN APPS GUDA 5 DA SUKAI FUCE A WANNAN LOKACIN


Assalamu alaikum ƴan uwa barkanmu da wannan lokaci, sannan kuma barkanmu da sake saduwa a wannan sabon bidiyon.

A cigaba da kawo maku muhimman Apps da wannan Shafi yake a yau munzo da bayanin wasu Apps har guda (5)  wanda ya kamata ace kowa ya sansu domin yawancinsu sababbi ne.

DALILIN KAWO WANNAN APPS ƊIN (5)

Duba da yanda ake samun cigaba a harkar technology a duniya, mukaga ya kamata ace muna kawo muku dukkan wasu Applications na waya da suka hau kan Google Playstore domin amfaninku da kuma samun sauƙi yayin aiki da wayoyinmu na hannu.

BAYANIN APP NA FARKO (Standby)


STANDBY Manhaja ce da ze baka damar ka canza fuskar wayarka izuwa kaloli dabam dabam wanda ze saka kadinga kewar wayar taka a duk lokacin da ka tuna da ita, ta yanda zakaga ya saita maka komai, wanda suka haɗa da Agogon wayarka, kwanan wata, dai dai sauran wasu abubuwan.

BAYANIN APP NA BIYU (VOLUME Booster 2023)


Kawai bayan ka sauke App ɗinka kana dannawa fuska ta farko da ze nuna maka ze tambayeka umarni seka danna " While using" daga sama akwai wata alama da aka rubuta " Enable" nan ma zaka danna, sekazo ƙasa inda aka rubuta " Volume" anan ne zaka ƙaro duk adadin sautin da kake so ka saka. A cikin wannan App ɗin akwai wasu abubuwan, kawai dai mu munkawo muhimmai ne.

BAYANIN APP NA UKU ( My link manager)
Shima wannan App ne me saukin amfani, kamar yadda fikirarsa take kawai idan kana wani abun ko kuma bakada lokacin kallan wani bidiyon ko kana wani aikin, ze baka dama ka dawo ka aje kowani irin Link daga baya idan ka gama aikin da kake seka danna ka kalli abinda kake so.

Kawai kana danna cikin App ɗin zakaga wata alama ta + daga ƙasa a gefe, seka danna wannan alamar, Kai tsaye ze baka zaɓuka guda uku seka zaɓi na tsakiyar, to dama ka ruga kayi Copy na link ɗinka anan kana Paste zakaga wata alama daga ƙasa seka danna Add shikenan ze adana maka. Da zaran ka buƙaci kallan abunka zaka zo ka danna seka ga ya buɗe maka kai tsaye. Shima wannan App ɗi  akwai wasu abubuwa da ya kamata ka duba domin ze amfaneka sosai.

BAYANIN APP NA HUƊU ( PASSPORT PHOTO)
Wannan Manhaja ce me matukar muhimmanci da ya kamata ace mun saka a wayoyinmu. Saboda sau da yawa yayin da ka tashi cike wani gurbin na neman karatu ko aiki ko wani abun ana neman bayananka, wanda muhimmin abunda akafi nema shine Hotonka na Passport. A don haka wannan App ze baka dama ka zaɓi kalar hoton ƙasar da kake so kai Passport ɗinta.

Bayan ka sauke App ɗinka kawai zaka danna cikinsa anan ne ze tambaye ka " Allow " seka danna, bayan ka danna ze baka fuskae alamar ƙaramin hoto, daga sama gefen hannunka ma hagu zakaga Alamar tutar ƙasashe, anan ne kana dannawa zaka zaɓi ƙasar da kake so yai maka irin Passport ɗinta. bayan ka zaɓa seka dawo ka danna wannan fuskar me alamar hoto, shine zai kaikia Gallery wato inda hotunan ka suke, anan me zakai Select na hoton da kake so ya maida maka shi Passport, daga ƙasa gefen hannunka na dama zakaga alamar Good kana dannawa, ya gama maka seka danna kan aikin da kai, seka ga Save ko share izuwa kafar sada zumunta. Idan kuma save ne zaka ganshi a cikin hotunan wayarka kana dubawa.

BAYANIN APP NA 5 ( Tap translate screen)
Kana shiga cikin App ɗinka fuskar farko zakaga wani jan rubutu yana Off seka maidashi On. Sannan daga ƙasa zaka zaɓi daga wannan yaren izuwa yaren da kake so a fassara maka. To kana futa zakaga wata alama me zagaye akan screen na wayarka to aduk lokacin da kake son fassara kawai zakka danna sau biyu seka jaaa abun, nan take zakaga ya fassara maka. Idan kuma kanasan kashe App ɗi  zaka koma cikinsa ne ka danna Off a wannan alamar da akai rubutu kalar Ja.

JERIN APPS ƊIN

STANDBY Danna NAN

VOLUME BOOSTER DANNA NAN

MY LINK MANAGER DANNA NAN

PASSPORT PHOTO DANNA NAN

TAP TRANSLATE SCREEN DANNA NAN

wasalam anan bayanin namu yazo karshe.

Mun gode.


Comments