Min menu

Pages

Makomar: Raya, Doku, Kane, Olise, Adams, Andre, Silva, Borges, Colwill, Williams, Bernardo, Dembele

Musayar yan wasa a yau ranar Laraba makomar: Raya, Doku, Kane, Olise, Adams, Andre, Silva, Borges, Colwill, Williams, Bernardo, Dembele, Mane 

Ga kanun labaran 

Arsenal ta amince da yarjejeniya da David Raya, cinikin Bayern Munich kan Kane bashi da tabbas, Bernardo a shirye yake ya koma Barcelona, PSG ta dau Dembele, City nada kwarin gwiwwar daukar Olise, Chelsea nason daukar Alvarez da Adams, Mane ya kammala komawa Al-Nasr

Ga cikakken labarin 

Arsenal ta amince da yarjejeniya da Brentford kan mai tsaron gida David Raya, mai shekaru 27, inda dan wasan na Spain ya kai fam miliyan 40. (Evening Standard)


Manchester City na zawarcin dan wasan Rennes dan kasar Belgium Jeremy Doku, mai shekaru 21, a matsayin wanda zai maye gurbin Riyad Mahrez, wanda ya koma kungiyar Al-Ahli ta Saudiyya a makon jiya. (Fabrizio Romano)


Har ila yau Manchester City na ganin dan wasan gaban Crystal Palace Michael Olise, mai shekaru  21, a matsayin zabin ta Wanda zai maye gurbin Mahrez, in da kocin Palace Roy Hodgson yayi ikirarin zai yi wahala taci gaba da rike dan wasan na Faransa na kasa da shekaru 21 a kulob din a bazara. (Athletic subscription required)


An yi watsi da tayin fan miliyan 85 da Bayern Munich ta kai kan dan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, inda Spurs ke son sama da fam miliyan 100 kan dan wasan mai shekaru 30. (Guardian)


Kane dai yana tsammanin zai ci gaba da zama a Tottenham a kakar wasa ta bana idan har kungiyar ba ta cimma matsaya da Bayern ba kafin wasan da kungiyar za ta buga da Brentford a gasar Premier, saboda yana ganin ba daidai ba ne ya bar kungiyar bayan an fara gasar. (Evening Standard)


Chelsea ta saka dan wasan tsakiyar Leeds United dan kasar Amurka Tyler Adams, mai shekaru 24, da kuma dan wasan Ajax na Mexico Edson Alvarez, mai shekaru 25, cikin jerin wadanda suke zawarcinsu. (Time - subscription required)


Dan wasan baya na Ingila na 'yan kasa da shekaru 21 Levi Colwill yana kusa da kulla sabuwar yarjejeniya a Chelsea ta hanyar sanya sakon bankwana ga Brighton a Instagram, inda dan wasan mai shekaru 20 ya shafe kakar wasa ta bara a matsayin aro. (TalkSPORT)


Liverpool na nazarin yarjejeniyar kawo dan wasan Fluminense dan kasar Brazil Andre, mai shekaru 22, zuwa kungiyar bayan da Southampton ta ki amincewa da tayi na biyu na dan wasan tsakiyarta dan kasar Belgium Romeo Lavia mai shekaru 19. (Sky Sports)


Dan wasan baya na kasar Ireland ta Arewa Jonny Evans, mai shekaru 35, yana shirin bai wa Manchester United kwantiragin shekara daya bayan ya koma kungiyar na kankanin lokaci a bazara. (Belfast Telegraph)


Nottingham Forest za ta saurari tayin sama da fam miliyan 40 kan dan wasan Wales Brennan Johnson, in da Tottenham, Brentford da Aston Villa na daga cikin kungiyoyin da ke son dauko dan wasan mai shekaru 22. (Football insider)


Dan wasan tsakiya na Manchester City dan kasar Portugal, Bernardo Silva ya "bude" kofar fa komawa Barcelona, ​​amma yanayin kudi na zakarun La Liga ya sa yunkurin siyan dan wasan mai shekaru 28 ba zai yiwu ba. (Sport in Spanish)


Paris St-Germain ta kulla yarjejeniya da dan wasan Barcelona dan kasar Faransa Ousmane Dembele, mai shekaru 26. (Fabrizio Romano)


West Ham ta kawo karshen zawarcin dan wasan tsakiyar Southampton da Ingila James Ward-Prowse, ganin cewa kudin da  da kungiyar ta Southampton ta yiwa dan wasan mai shekaru 28 ta yi yawa Dan wasan. (Sky Sports)


Dan wasan Manchester City dan kasar Portugal Carlos Borges, mai shekaru 19, yana dab da komawa Ajax a kan kudi Yuro miliyan 20 (£17m). (Athletic subscription required)


Everton za ta iya zawarcin dan wasan West Ham dan kasar Jamaica Michail Antonio bayan dan wasan mai shekaru 33 ya kasa samun damar komawa Saudiya. (Football insider)


Galatasaray na son dauko dan wasan Tottenham dan kasar Faransa Tanguy Ndombele kuma suna fatan kulla yarjejeniyar fan miliyan 11 kan dan wasan mai shekaru 26 (Mirror)


Leeds na tunanin zawarcin dan wasan bayan Manchester United Brandon Williams, mai shekaru 22, dan kasar Ingila. (Independent)

Comments