Min menu

Pages

Makomar: Raya, Mane, Kane, Lukaku, Olise, Amrabat, Van de Beek, Dembele, Todibo, Greenwood,Allan Saint-Maximin, Fred

 

Musayar yan wasa a yau ranar Aabar makomar: Raya, Mane, Kane, Lukaku, Olise, Amrabat, Van de Beek, Dembele, Todibo, Greenwood, Allan Saint-Maximin, Allan Saint-Maximin, Fred 

Ga kanun labaran 

Greenwood zai dawo taka Leda bayan tsawon lokacin, Munich ta fara tattaunawa da Raya, Chelsea nason sayar da Lukaku, United daf da kammala daukar Amrabat, Tottenham ta sake zama da wakilan Munich, PSG zata dau Dembele, kimanin manyan kungiyoyi biyar ne zasu fafata a zawarcin Todibo, Al-ittihad ta dau Allan Saint-Maximin

Ga cikakken labarin 

Bayern Munich ta fara tattaunawa da Brentford kan yarjejeniyar sayen golan Spain David Raya, mai shekaru 27, inda shi kuma mai tsaron ragar zakarun Jamus na Switzerland Yann Sommer, mai shekaru 34, ya tattauna batun komawa Inter Milan. (Sky Sports)


Bayern ta kuma amince da tayin Al-Nassr na dan wasan gaban Senegal Sadio Mane mai shekaru 31. (Fabrizio Romano)


Tottenham ta sake wani taro da mahukuntan Bayern ranar Litinin don tattaunawa kan yiwuwar siyar da dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekaru 30, bayan da aka soke tattaunawar da aka shirya yi ranar Juma'a. (Mail)


Tottenham za ta yi amfani da tattaunawarsu da Bayern kan Kane don tattaunawa kan sha'awarsu ta neman dan wasan gaban Faransa mai shekaru 18 a Jamus Mathys Tel. (Telegraph - subscription required)


Chelsea ta ki amincewa da tayin aro na Juventus inda takai tayi na sayen dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku, mai shekaru 30, saboda suna son sayar da shi na dindindin. (Tuttosport - in Italian)


Chelsea na zawarcin 'yan wasan tsakiya guda uku - ciki harda da dan wasan Crystal Palace na kasar Faransa Michael Olise, mai shekaru 21, da Rayan Cherki dan kasar Faransa mai shekaru 19 da haihuwa da kuma Mohammed Kudus na Ajax mai shekaru 22. (Football London)


Manchester United za ta iya zawarcin Dan wasan Fiorentina da dan wasan Morocco Sofyan Amrabat, mai shekaru 26, ko kuma wani dan wasan tsakiya na baya a karshen kasuwar saye da sayar da 'yan wasa idan kulob din ya samu isassun kudade daga sayar da 'yan wasan ta. (Guardian)


Real Sociedad na tattaunawa kan dauko Donny van de Beek a matsayin aro daga Manchester United tare da zabin siyan dan wasan tsakiyar Netherlands din, mai shekaru 26. (Marca - in Spanish)


Paris St-Germain na shirin kammala yarjejeniyar ba-zata don siyan dan wasan Faransa Ousmane Dembele daga Barcelona. Dan wasan mai shekaru 26 yana da fam miliyan 42.8 wanda zai kare ranar Litinin. (ESPN)


Newcastle United ta sayar da dan wasan Faransa Allan Saint-Maximin, mai shekaru 26, ga kungiyar Al-Ahli ta Saudi Pro League a kan fan miliyan 30. (Mail)


Manchester United a shirya take ta bar golan Ingila Dean Henderson, mai shekaru 26, ya koma Nottingham Forest a matsayin aro. (Manchester Evening News)


Real Madrid na tunanin zawarcin golan Getafe David Soria yayin da Crystal Palace da Forest suma ke zawarcin dan kasar Spain din mai shekaru 30. (AS- in Spanish)


Aston Villa ba za ta sayi dan wasan gefe na Sporting Lisbon na Portugal Pedro Goncalves, mai shekaru 25, saboda tayin £38.6m ya mata tsada in ya zama Dan wasan nafi tsada a kungiyar £30m a farashin da Sporting ta nema. (Record - in Portuguese)


Galatasaray na zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester United dan kasar Brazil Fred, mai shekaru 30, amma akwai tazara a kimarsa tsakanin kungiyoyin biyu. (Sky Sports)


Dan wasan gaba na Ingila Mason Greenwood, mai shekaru 21, zai iya samun makoma a Manchester United bayan da babban mai daukar nauyin kungiyar ya amince ya dawo taka leda. (Sun)


Nottingham Forest ta yi watsi da tayin fam miliyan 35 da Brentford ta yi wa dan wasan gaban Wales Brennan Johnson, mai shekaru 22. (Telegraph - subscription required)


Kociyan kungiyar Roberto de Zerbi ya ce Brighton za ta sayi wani babban dan wasa idan Moises Caicedo ya bar kungiyar a kakar wasa ta bana, inda tuni Chelsea ta ki amincewa da neman dan wasan tsakiyar Ecuador, mai shekaru 21. (Mail)


Newcastle United, West HamUnited, Aston Villa, Paris St-Germain da Napoli duk sun tuntubi Nice game da Jean-Clair Todibo amma dan wasan Faransan mai shekaru 23, baya gaggawar barin kungiyar. (Nice-Matin - in French)


Tyler Adams, mai shekara 24, yana da yarjejeniyar barin kungiyar ta kusan fam miliyan 20 a kwantiraginsa na Leeds United, in da Aston Villa da West Ham da dan wasan tsakiyar Amurka suka fuskanci juna. (Athletic subscription required)

Comments