Min menu

Pages

Makomar: Hojlund, Lukaku, Dybala, Gallagher, Mbappe, Lavia, Fabinho, Sanches, Lukaku, Calvert-Lewin

Musayar yan wasa a yau ranar Alhamis makomar: Hojlund, Lukaku, Dybala, Gallagher, Mbappe, Lavia, Fabinho, Sanches, Lukaku, Calvert-Lewin

Ga kanun labaran 

Manchester United ta Kai tayi kan Hojlund, Mbappe ya amincewa da komawa Madrid, Juventus nason daukar Lukaku aro, Da'alama Chelsea baza ta dau Dybala ba, Chelsea bata son sayar da Calvert-Lewin

Ga cikakken labarin 

Manchester United ta kai tayin baka na Yuro miliyan 50 (£42.8m) da kuma Yuro miliyan 10 (£8.5m) a matsayin kari ga Atalanta kan dan wasan gaban Denmark Rasmus Hojlund mai shekaru 20. (Athletic subscription required)


Paris St-Germain, wacce ita ma ke zawarcin Hojlund, ta kai tayin karin albashi ga dan wasan wanda ya fison komawa Manchester United. (Gianluca di Marzio - In Italian)


Daraktan wasanni na Juventus, Cristiano Giuntoli, zai tafi Ingila domin tattaunawa da Chelsea kan aro dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku, mai shekaru 30. (Calciomercato, via Goal)


Lukaku ya ci gaba da zama a Landan yayin da sauran ‘yan wasan Chelsea ke rangadin tunkarar kakar wasa a Amurka. (Time subscription required)


Dan wasan Faransa da PSG Kylian Mbappe, mai shekaru 24, ba ya sha'awar ganawa da wakilan Al-Hilal kan yiwuwar komawa Saudiyya. (Sky Sports)


Majiyoyin da ke kusa da tattaunawar sun kara gamsuwa Mbappe ya amince da sharuddan komawa Real Madrid a shekara mai zuwa. (Telegraph - subscription required)


Da alama Chelsea za ta yi rashin nasara kan dan wasan gaban Argentina Paulo Dybala, kamar yadda rahotanni suka nuna dan wasan mai shekaru 29 ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya a Roma. (Tuttomercatoweb, via football transfer)


West Ham na iya rasa damar siyan dan wasan tsakiyar Ingila Conor Gallagher, mai shekaru 23, wanda ke son ci gaba da zama a Chelsea da kuma fafutukar neman gurbi karkashin sabon kociyan kungiyar Mauricio Pochettino. (Mail)


A halin da ake ciki, West Ham na ci gaba da tattaunawa da dan wasan tsakiya na Southampton da Ingila James Ward-Prowse, mai shekaru 28, tare da kulla yarjejeniya a yanzu. (Football Insider)


Al-Hilal na kan gaba a yunkurinta na sayen dan wasan tsakiya na Paris St-Germain da Italiya Marco Verratti, mai shekaru 30. (Fabrizio Romano)


Liverpool na shirin inganta tayin farko kan fam miliyan 37 kan dan wasan tsakiyar Southampton Romeo Lavia mai shekaru 19 dan kasar Belgium. (Athletic subscription required)


Liverpool da Saints sun kai kusan fam miliyan 15 a farashin Lavia. (Telegraph)


Ana sa ran Reds za ta karbi tayin fan miliyan 40 daga Al-Ittihad na dan wasan tsakiya na Brazil Fabinho, mai shekaru 29, bayan sun koma tattaunawa. (Time)


Dan wasan tsakiya na PSG da Portugal Renato Sanches, mai shekaru 25, ya kusa rattaba hannu kan yarjejeniyar aro na tsawon kakar wasa da kungiyar Roma ta Serie A. (L'Equipe - in French)


Fatan Aston Villa na sayen dan wasan tsakiya na Tottenham da Argentina Giovani Lo Celso ya kara kaimi saboda har yanzu Napoli ta gaza rufe yarjejeniya da dan wasan mai shekaru 27. (Birmingham Live)


Dan wasan bayan Ingila Rico Lewis, mai shekara 18, ya amince da kwantiragin shekaru biyar, wanda zai kasance da zabin na tsawon shekara guda, in da Manchester City, da dan wasan baya na kungiyar Nathan Ake, mai shekaru 28, shi ma ya kulla sabuwar yarjejeniya. (Mail)


Everton ba ta da sha'awar siyar da dan wasan Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekaru 26, wanda ake alakanta shi da komawa Roma. (Mail)

Comments