Min menu

Pages

Makomar: Hojlund, Mbappe, Amrabat, Martinez, Kolo Muani, Kudus, Kane,Toure

Musayar yan wasa a yau ranar Talata makomar: Hojlund, Mbappe, Amrabat, Martinez, Kolo Muani, Kudus, Kane,Toure 

Ga kanun labaran 

United ta dau Amrabat da Hojlund, da yiyuwar Mbappe ya koma Madrid, PSG zata iya daukar Kane duk da zawarcin Munich

Ga cikakken labarin 

Manchester United za ta kai tayin Rasmus Hojlund ga kungiyar sa Atalanta a yunkurinta nason daukar dan wasan gaban Denmark in Rasmus Hojlund mai shekaru 20 a wannan makon. (Mail)


Manchester United ba za ta biya sama da fam miliyan 60 kan Hojlund ba, amma Atalanta na son fan miliyan 86. (Time - subscription required)


A wani bangaran Kuma Dan wasan Denmark din ya amince komawar kungiyar ta Manchester United kan yarjejeniyar shekaru Biyar (Fabrizio Romano)


Dan wasan Fiorentina dan kasar Morocco Sofyan Amrabat, mai shekaru 26, ya cimma yarjejeniyar komawa Manchester United kan kwantiragin shekaru biyar. (Nicolo Schira)


Inter Milan ta kai wa Aston Villa tayin Yuro miliyan 15 (£13m) kan golan Argentina Emiliano Martinez, mai shekaru 30, bayan Andre Onana ya koma Manchester United. (TyC Sports Argentina - in Spanish)


Manchester United na neman dan wasan Eintracht Frankfurt dan kasar Faransa Randal Kolo Muani mai shekaru 24, yayin da kociyan kungiyar Erik ten Hag ya Kara bayyana sha'awar sa ta daukar dan wasan gaban Ajax dan kasar Ghana Mohammed Kudus mai shekaru 22, wanda ake dangantashi da Chelsea. (Mirror)


Ten Hag kofarsa a buɗe take domin karbar tayin 'yan wasan sa na Manchester United da yawa domin samin kuɗi da ake buƙata don ƙaddamar da yunƙurin siyan dan wasan gaba. (Football Insider)


Ten Hag na neman karfafa zabin mai tsaron gida na Manchester United tare da daukar dan wasan Fenerbahce mai shekaru 25 Altay Bayindir dan kasar Turkiyya. (Goal)


Chelsea, Manchester United da Tottenham za su kasance cikin kungiyoyin dake zawarcin dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekaru 24, bayan da Paris St-Germain za ta samu fan miliyan 259 daga kungiyar Al-Hilal ta Saudi Arabiya a cinikin Mbappe.(Telegraph - subscription)


Al-Hilal na shirin bai wa Mbappe albashin da ya kai Yuro miliyan 200 (£172m) a shekara yayin da zai ba shi damar rike kashi 100 na hakkin hotonsa (Fabrizio Romano).


Idan Mbappe ya koma Al-Hilal zai iya zaman shekara guda kawai, inda PSG ta gamsu cewa shugaban Real Madrid Florentino Perez da dan wasan sun kulla yarjejeniya da shi don komawa gasar La Liga a badi. (Time subscription required)


Barcelona ta nisanta kanta daga zawarcin Mbappe duk da ikirarin cewa sun tattauna da PSG. (Marca - in Spanish)


Idan Mbappe ya koma Saudi Arabiya, PSG za ta biya fam miliyan 100 ga Tottenham kan dan wasan gaba Harry Kane, mai shekaru 29, duk da cewa har yanzu Bayern Munich na da kwarin gwiwa cewa kyaftin din Ingila zai zabi komawa kungiyar. (Football Insider)


Al-Hilal na dab da daukar dan wasan Fulham dan kasar Serbia Aleksandar Mitrovic, mai shekaru 28. (90min)


Dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson, mai shekaru 33, ya yi bankwana da takwarorinsa na Liverpool da ma'aikatansa kafin ya koma kulob din Al-Ettifaq na Saudiyya.(Mail)


Dan wasan gaban Amurka Folarin Balogun, mai shekaru 22, ya yi atisaye shi kadai a lokacin da kungiyar Arsenal ta ziyarci kasar Amurka, inda Inter Milan ta shirya tayin fan miliyan 35 kan dan wasan. (Mail)


Everton na dab da neman dan wasan Almeria na Mali El Bilal Toure, mai shekaru 21, duk da tana fuskantar hamayya da Atalanta.(football Insider)


West Ham ta kaiwa Southampton tayin£25m kan dan wasan tsakiyar Ingila James Ward-Prowse mai shekaru 28. (Telegraph - subscription required)


Yunkurin Chelsea na sayen dan wasan tsakiya na Ecuador Moises Caicedo, mai shekaru 21, daga Brighton ya ci tura saboda bukatar Brighton na shigar da dan wasan baya Levi Colwill mai shekaru 20 a cikin yarjejeniyar. (Guardian)


Tottenham da Nottingham Forest sun tuntubi Juventus kan dan wasan bayan Italiya Andrea Cambiaso, mai shekaru 23. (Tuttosport - in Italian)


Manchester United na shirin tsawaita kwantiragin dan wasan bayan Ingila Aaron Wan-Bissaka, mai shekaru 25, bayan da ta yanke shawarar kin zawarcin dan wasan Inter Milan dan kasar Netherlands Denzel Dumfries, mai shekaru 27. (Mirror)


Dan wasan tsakiya na Leicester City Hamza Choudhury, mai shekaru 25, yana son makomarsa ta daidaita kafin a fara kakar wasa ta bana, sakamakon zawarcin Southampton. (Mail)

Comments