Min menu

Pages

Makomar: Fabinho, Kane, Hojlund, Zaha, Henderson, Silva, Doucoure, Suarez

Musayar yan wasa a yau ranar Asabar makomar: Fabinho, Kane, Hojlund, Zaha, Henderson, Silva, Doucoure, Suarez 

Ga kanun labaran 

PSG ta sawa United Kai a cinikin Hojlund bayan makomar Mbappe bata da tabbas a kungiyar, duk da haka United na Kara kaimi a cinikin Dan wasan, Palace na saran Zaha zaici gaba da zama a kungiyar, Liverpool, At Madrid, PSG zasu fafata a cinikin Doucoure

Ga cikakken labarin 

Zakarun Jamus Bayern Munich na zawarcin dan wasan tsakiyar Liverpool da Brazil Fabinho, mai shekaru 29, idan yunkurinsa na komawa Al-Ittihad bai cimma ruwa ba. (Sky Germany- in German)


A halin da ake ciki, Bayern na shirin kai tayi na uku kan dan wasan gaban Tottenham da Ingila Harry Kane kuma tana da kwarin gwiwar siyan dan wasan mai shekaru 29. (Time - subscription required)


Ta ko yaya dan wasan bayan Ingila Kyle Walker, mai shekaru 33, yana sha'awar tattaunawa da Bayern Munich yayin da yake tunanin barin Manchester City a wannan bazarar. (Sky Sports)


Atalanta ba ta son yin watsi da tayin fam miliyan 86 kan dan wasan Denmark Rasmus Hojlund, mai shekaru 20, wanda Manchester United ke zawarcinsa. (Mail)


Paris St-Germain kuma tana sha'awar Hojlund kuma sun fara tattaunawa. (L'Equipe - in France)


Crystal Palace na da kwarin gwiwar dan wasan gaban Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekaru 30, zai rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya duk da sha'awar Al-Ettifaq da Lazio. (Telegraph - subscription required)


Dan wasan bayan Brazil na hagu Alex Telles, mai shekaru 30, ana kan hanyar kammala cinikinsa kan £4m daga Manchester United zuwa Al-Nassr. (Mirror)


Nottingham Forest na dab da daukar dan wasa Ola Aina, mai shekaru 26, bayan kwantiragin dan wasan Najeriya din ya kare a Torino. (Time - subscription required)


Lazio ta bi sahun Fulham a yunkurin dauko dan wasan Chelsea Callum Hudson-Odoi, mai shekaru 22. (Alfredo Pedulla - in Italian)


Dan wasan bayan Southampton na Ingila 'yan kasa da shekara 21, Tino Livramento, mai shekaru 20, yana dab da komawa Newcastle. (Chronicle live)


Liverpool, Paris St-Germain da Atletico Madrid suna zawarcin dan wasan tsakiyar Mali Cheick Doucoure, mai shekaru 23, amma Crystal Palace na bukatar fan miliyan 65 kan Dan wasan. (90min)


Liverpool na tattaunawa da Preston North End kan siyar da dan wasan ta dan kasar Ingila Layton Stewart mai shekaru 20. (Liverpool Echo)


Dan wasan tsakiyar Spain Thiago Alcantara, mai shekaru 32, yana tunanin barin Liverpool inda yake da zabi a Spain, Saudi Arabia da kuma Turkiyya. (Diario Sport - in Spanish)


Dan wasan baya na kasar Holland Ki-Jana Hoever, mai shekaru 21, da dan kasar Portugal Chiquinho, mai shekaru 23, suna kan hanyar zuwa Stoke a matsayin aro na kakar wasa ta bana daga Wolves. (Express and Star)


Dan wasan bayan Fiorentina dan kasar Brazil Igor, mai shekaru 25, na shirin kammala gwajin lafiya a Brighton ranar Litinin bayan kungiyoyin sun amince kan kudi fan miliyan 14.7 (€17m). (Fabrizio Romano)


An ki amincewa da tayin Monaco sau biyu kan dan wasan bayan Southampton dan Ghana Mohammed Salisu, mai shekaru 24, kuma watakila za su jira har zuwa watan Janairu lokacin da za su tattauna batun daukar sa kyauta a bazara mai zuwa. (Mail)


Kocin Gremio Renato Gaucho ya ce dan wasan gaban Uruguay Luis Suarez ya tattauna da shugaban kulob din na Brazil kan yiwuwar komawa Inter Miami, inda dan wasan mai shekaru 36 zai sake haduwa da tsohon abokin wasan Barcelona Lionel Messi. (Goal)


Manchester City na neman dan wasan tsakiyar na Portugal Bernardo Silva, mai shekaru 28, domin ya amsa masa sabon kwantiragin fan 300,000 a kowanna mako. (Mirror)


Atletico Madrid na shirin fafatawa da Chelsea wajen siyan dan wasan Montpellier dan kasar Faransa Elye Wahi, mai shekaru 20. (L'Equipe - in French)


Sai dai Wahi ya ce ba ya son ya je kungiyar 'yar uwar Chelsea ta Strasbourg a kamar aro idan Chelsea ta dauko shi. (Foot Mercato - in French)


Comments