Min menu

Pages

Makomar: Rice, Gundogan, Neymar, Kim, Neves, Xhaka, Caicedo, Balogun, Vinicius Jr, Navas, Mac Alliester, Sabitzer

Musayar yan wasa a yau ranar Talata makomar: Rice, Gundogan, Neymar, Kim, Neves, Xhaka, Caicedo, Balogun, Vinicius Jr, Navas, Mac Alliester, Sabitzer 

Ga kanun labaran

Bayern ta shiga neman Rice, inda kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ke kokarin komawa cinikin Neves yayin da yake daf da tafiya Barcelona, Xhaka yace makomar sa zata bayyana ƙarshen markon nan, Munich ta sanar da United farashin Sabitzer, Vinicius zaici gaba da zama a Madrid, United tayi magana da Wakilin Neymar, inda kungiyar ke daf da kammala cikin Kim PSG ke kokarin fadawa cinikin, Arsenal nason daukar Gundogan 

Ga cikakken labarin

Bayern Munich na ganin dan wasan West Ham dan kasar Ingila Declan Rice, mai shekaru 24, a matsayin wanda ya dace da 'yan wasan tsakiya a gare su, amma sun san Arsenal ma na kokarin dauko shi. (Sky Sport Germany)


Arsenal na zawarcin kyaftin din Manchester City kuma dan kasar Jamus Ilkay Gundogan mai shekaru 32. Dan wasan mai shekaru 32 kwantiraginsa zai kare a wannan bazarar. (Guardian)


Manchester United na tattaunawa da dan wasan Brazil Neymar, mai shekaru 31, daga Paris St-Germain. (L'Equipe - in France)


Manchester United na shirin kammala cinikin dan wasan Napoli na kasar Koriya ta Kudu Kim Min-jae, mai shekaru 26, wanda kuma PSG ke nema.(Sun)


Barcelona na son dauko dan wasan tsakiya na Portugal Ruben Neves, mai shekaru 26, daga Wolves a wannan bazarar, amma cinikin ya danganta da ko dan wasan Spain Ansu Fati, mai shekaru 20, zai bar Barca. (Athletic - subscription required)


Idan Arsenal ba ta sayi Declan Rice na West Ham ba, za ta sanya Dan wasan Wolves' Neves, da dan wasan tsakiya na Real Sociedad da Spain Martin Zubimendi, mai shekaru 24, da dan wasan tsakiyar Brighton na Ecuador Moises Caicedo, mai shekaru 21, a matsayin madadinsa. (Mail)


Dan wasan tsakiyar Switzerland Granit Xhaka, mai shekaru 30, ya ce za a yanke shawarar makomarsa ta Arsenal kafin wasansu na karshe na kakar wasa ta bana. Gunners na tattaunawa da Bayer Leverkusen kan kudi fan miliyan 13. (Standard)


AC Milan ta sanya dan wasan gaban Arsenal dan kasar Amurka Folarin Balogun, mai shekaru 21, a matsayin babban Dan wasan da take burin siya dan wasan bayan da ya taka rawar gani a matsayin aro a Reims a kakar wasa ta bana, amma suna fuskantar hamayya daga RB Leipzig. (Calciomercato - in Italian)


Dan wasan gaban Brazil Vinicius Jr, mai shekaru 22, ba shi da niyyar barin Real Madrid duk da cin zarafi na wariyar launin fata daga abokan hamayyarsa. (90min)


Liverpool ta shiga jerin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan bayan Crystal Palace Marc Guehi mai shekaru 22 a duniya. (Mail)


Liverpool na dab da kulla yarjejeniya da dan wasan Brighton da Argentina Alexis Mac Allister, mai shekaru 24. (Fabrizio Romano)


Ita ma Manchester City na son sayen Mac Allister wanda ya lashe kofin duniya. (Mirror)

Manchester United na son barin dan wasan gaban Faransa Anthony Martial mai shekaru 27 ya tafi. (Sun)


Bayern Munich ta shaida wa Manchester United cewa dole ne ta biya fam miliyan 22 don siyan dan wasan tsakiyar Austria Marcel Sabitzer, mai shekaru 29, Wanda yanzu yake zaman aro a kungiyar kan kwantiragin dindindin a wannan bazarar. (Sky Sport Germany)


Nottingham Forest na son ci gaba da rike golan Costa Rica Keylor Navas, mai shekaru 36, ​​da dan wasan baya na Brazil Renan Lodi, mai shekaru 24, wadanda ke zaman aro daga Paris St-Germain da Atletico Madrid gaba dayan su. (90min)


Nottingham Forest na sha'awar golan Monza na Italiya mai shekaru 25, Michele di Gregorio. (Calciomercato - in Italian)


Tottenham zata biya Feyenoord fiye da fam miliyan 6 domin mayar da Arne Slot sabon kocinta tare da nada mataimakansa biyu. (Mail) 

Comments