Min menu

Pages

Yadda zaku raba screen din wayarku gida biyu.

 Yadda zaku raba screen din wayarku gida biyu.Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu?


Hakika muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu a koda yaushe muna godiya sosai da sosai.


A yau cikin shirin namu munzo muku ne da bayanin wani application wanda zai baku dama ku raba screen din wayarku gida biyu.


Wasu zasu cika da mamaki suce yaya mutum zai raba screen din wayarsa gida biyu alhalin da hankalin sa ba tabuwa yayi ba.


To bari kuji ba irin wannan rabawar nake nufi ba.


Wasu da yawa suna son yin aiki biyu da wayarsu lokaci guda, kuma basu san yadda ake yi ba, wannan yasa muka zo muku da wannan sabon application din wanda zaku iya amfani dashi wajen yin ayyuka biyu da waya daya kuma a lokaci guda.


Wannan App din zai baku damar da zaku bude bidiyo kuna kallo kuma a gefe kuna daukar photo ko yin shira a WhatsApp duk kuma a lokacin, ko kuma sauran abubuwa.


Dan haka duk mai bukatar son dauko wannan App din ya duba kasa gurinda aka rubuta danna nan domin saukarwa


                        Danna nan

Comments