Min menu

Pages

Yadda zaku gano wayarku ta hanyar yin tafi da hannunku.

 Yadda zaku gano wayarku ta hanyar yin tafi da hannunku.

Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu.


A yau cikin shirin namu munzo muku ne da wani application wanda zai birgeku sosai


Sauda yawa mutane sukan iya manta wayarsu a daki cikin duhu kuma babu fitila wannan zaisa suyi ta dube dube domin su gano inda wayar tasu take amma sai sunsha wahala kafin su sameta.

To wannan application din idan kuka dorashi akan wayarku zaku iya saitashi inda koda kun ajiye wayarku baku ganta ba da zarar kun tafa hannunku zatai kara ko kuma tayi haske.


Sannan wannan app din aikinsa bai zaya nan kadai ba zaku iya saitashi ta amfani da bakinku idan kukai fito to wayar zatai kara wannan zai baku damar sanin inda take.


Bayan haka zaku iya saita app din ta hanyar yin motsi da jikinku duk lokacinda kukai motsi to wayar zatai kara.


Sannan zaku iya saita app din ta duk wanda ya taba wayar a cikin taro ta fara jiniya tana kara wannan zai taimaka wajen kama barawo ko mai son daukar muku wayar.


Bayan haka akwai sauran abubuwa da wannan App din yake yi.

Dan haka duk mai son dauko wannan App din ya duba kasa gurinda aka rubuta danna nan                           Danna nan


Comments