Min menu

Pages

Wani kauye a Nigeria inda Maza da mata suke magana da yare mabanbanta

 Domin kallon bidiyon garin da kuma yan garin kalli kasa


Wani kauye a Nigeria inda Maza da mata suke magana da yare mabanbanta

A kauyen ubang wanda, inda mafiya yawan alummar gauyen manomane wanda yake a kudancin Nigeria inda Maza da mata ke magana da mabanbantan yaruka a tsakaninsu. A cewarsu wannan aladar tasu baiwa ce daga Allah, amma fa yayin da da yawa daga matasan garin ke tafiya zuwa wasu sassan kasa yayinda yaren yaren turanci ke kara samun gindin zama a garin, akwai barazanar cewa yaren ka iya bacewa daga doron kasa - 

Alummar kauyen sunce "jinsin guda biyu suna fahimtar junansu, Amma yayin magana kowa yana amfani yaren jinsin sa" ba'a san zahirin adadin kalmomin da suka banbanta tsakanin yarukan guda biyu ba.

Akwai kalmomin da yawa wadanda suke iri daya me tsakanin mazan da matan, sannan akwai wadansu wadanda suka banbanta wajen sauti da haruffa

Yayin da yaro yakai shekara Goma ake tsammanin sa da fara cikakken yaren Maza a wannan lokacin yaro da Kansa zai fahimci cewa ga irin kalmomin da zaike amfani dasu, babu bukatar wani ya fada masa irin kalmomin da zaina amfani dasu, yayin da yaro ya fara cikakkiyar magana irin ta Maza Hakan na nuna yaron ya Isa shekarun girma

Alummar kauyen ubong suna matukar alfahari da wannan banbancin yaren dake tsakaninsu suna kallona Hakan a matsayin wani abu na musamman. Akwai maganganu mabanbanta akan yadda wannan banbance banbance ya samo asali


Comments