Min menu

Pages

 Tarihin kasar sudan



Kasar Sudan tana daya daga cikin kasashen dake Nahiyar Africa, inda take a yankin arewa maso gabashi.

Kasar  tana  iyaka da kasashe har guda tara. 

Wato Daga arewacin kasar tana iyaka da Misra wato Egypt, daga gabashi kuma Eritrea da Ethiopia, daga kudanci, Kenya da Uganda daga kudu maso gabas congo, da jamhoriyar Afirka ta Tsakiya, daga yammaci Chadi, daga arewa maso yammaci Libya.


Kasar sudan kasace wacce take bin addinin musulci domin mafiya yawan mutanen kasar musulmai ne.

Tutar kasar tanada launi guda hudu launin ja da fari a tsakiya sai kuma launin baki dake kasa a gefe guda kuma akwai launin Kore.

A bangaren yare Sudan tanada yare sama da dari biyar to amma amma wadanda suke kan gaba basu fi guda goma sha biyar ba, inda yaren larabci shine akan gaba sai kuma yaren dinka, hausa shine yare na uku da yafi yawa a kasar in aka dauke yare biyun da muka bayyana a farko, sai kuma yaren Nuba, four, mahas, danagla,zaghawa, Tigrinya, sai Fulani da kuma bargo, Tama, masalit, nuwair, sai kuma yaren shulukda.

Idan a bangaren dokar kasar ne kasar tanada yare guda biyu ne a matsayin official languages dinsu wato larabci sai kuma yaren English.

A bangaren yanki kasar ta sudan tanada yankuna har wajen guda ashirin da shida ne wanda babban birnin kasar yakasance sunansa Khartoum.

Sannan batun fadi ko kuma girman kasa Sudan tana daya daga cikin kasashe uku mafiya girma da kuma fadin kasa a Nahiyar Africa.

Akwai guraren shakatawa da kuma yawon bude ido da mutane kan ziyarta sune kamar haka 

Gidan tarihin kasar ta sudan

Duwatsun darfour 

Sai kuma birnin kasala.

Daga karshe an raba kasar ta sudan gida biyu akwai arewa sannan akwai sudan ta kudu.

Mu kasance tare daku a wani sabon shirin.

Comments