Min menu

Pages

 Kasar Algeria



Aljeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka, wacce take a arewaci. 

Kasar Algeria babbar kasa ce idan aka zo maganar fadi da kuma girman kasa domin za'a iya sata a sahun farko cikin manyan ƙasashen dake Africa.

Algeria kasar musulmi ce kusan gaba daya domin musulmai sune suke da rinjaye sosai a cikin wannan kasar kuma kusan gaba dayansu larabawa ne.

Harshen da yan kasar suke amfani dashi shine larabci.

Kasar Algeria tana iyaka da wani babban kogi daga arewacinta, sannan kuma tana zagaye ne da wasu kasashe guda shida sune kamar haka.


daga yammaci Maroko da kuma wata hamada

daga kudu maso yammaci Murutaniya, da kuma kasar Mali.

daga kudu maso gabashi kuma kasar ta Algeria tana iyaka ne da kasar Nijar.

daga gabashi kuma kasar Libya

Tutar kasar Algeria launi biyu ne da ita kore da kuma fari sai kuma tambayi farin wata da tauraruwa a tsakiyar tutar.

Kasar tana da jahohi akalla arbain da takwas inda babban birnin kasar shine Algiers, akwai gine gine masu matukar kyau da daukar hankali a kasar.


Comments