Min menu

Pages

Kogi 7 mafi haɗari a Duniya, sun ci rayuka da dama, 3 daga cikinsu a Afirka su ke

Kogi 7 mafi haɗari a Duniya, sun ci rayuka da dama, 3 daga cikinsu a Afirka su ke





A Duniya akwai kyawawan wurare da yawa waɗanda ke da haɗari sosai, wasu ma su kai ga rasa rayuka.


Wasu koguna dake da matuƙar burgewa, sai ka ji kamar ka shiga cikinsu.  Abin ban mamaki game da waɗannan ruwayen masu kisa shi ne yawancinsu kamar ramukan ninkaya na yau da kullum su ke.


1. Frying Pan Lake, New Zealand:  Frying Pan Lake yana cikin Waimangu Volcanic Rift Valley na New Zealand. Wannan tafkin yana da zafi sosai, domin kuwa zafinsa yakai kusan digiri 45 zuwa 55 na ma’aunin celcius. Yana cikin wani yanki na wani dutse mai aman wuta da ake kira da Echo Crater. Fashewar da dutsen yayi ya haifar da mutuwar sama da mutane 100  a shekara ta 1886, don haka tafkin yana da mummunan tarihi.



2. Tafkin Kivu, Rwanda: Tafkin Kivu kyakkyawan tafki ne da ke da yanayi mai ban sha’awa da ban ƙaye, kuma matattarar masu yawon bude ido da mazauna gida. Duk da kyawunsa, tafkin Kivu babban bala’i ne da ke jiran faruwa. Tafkin yana da nisan mil 12 na carbon dioxide da nisan mil 16 na methane a ƙasa, wanda suna iya fashewa a ko wane lokaci, kuma a duk lokacin daya fashe to nan take zai ƙone duk wani abu daya taɓa nan take. yana iya fashe a zahiri a kowane lokaci.


 

3. Jacob’s Well, Texas: Jacob’s well wani kyakkyawan rami ne mai ban sha’awa da ke cikin Texas. Idan ka kalleshi ba zaka taɓa cewa yana da wani aibu ba saboda kyawunsa, amman a cikin shekara ɗaya wannan tafkin yayi sanadiyar mutuwar mutane har kimanin 8. Tafarkin Jacob's  well yana kama da wajen yin iyo sai kuma shi ba wajen yin iyo bane mutum yana shiga sai dai uwarsa ta haifi wani. 

 


4. Boiling Lake, Dominica: Saboda hatsarin tafkin yasa mahukunta suka hana yin iyo a cikin wannan tafkin domin kuwa ruwan yana da tsananin zafi ta yadda nan take yake dafa duk wani abu da ya faɗa cikinsa. Ance ruwan yana da launin toka-shuɗi wanda yawanci ke lulluɓe a cikin gajimare na tururi, Tafarkin Tafasa kenan kamar yadda muka yi masa laƙabi da Hausa.



5. Tafkin Natron, Tanzania: Tafkin Natron wani tafki ne a ƙasar Tanzania, wanda ruwan yake kalar ja, yana dauke da alkalinity wanda ya kai kusan 12, wanda yake zagwanyar da dabbobi, mutane har ma da duwatsu. Wannan tafkin yana da ɗanɗanon gishiri-gishiri. Yin cudanya da ruwan na iya kona fata.



6. Great Blue Hole Well: Kamar Jacob’s well, Great Blue Hole well, Babban rami ne mai dauke da shuɗi kala mai ban sha’awa. A Ƙarƙashin saman kyakkyawan ruwa mai launin shuɗi kuma wani zazzafan ruwane mai tsananin zafi. Babban abin da ya fi hatsari dake a wannan tafkin shi ne, masana kimiyya sun gano cewa yayin da suke gangara cikin ramin, akwai wani sinadari na hydrogen sulfide wanda ya mamaye ilahirin tafarkin gaba ɗaya, wanda babu iskar oxygen a ƙarƙashinsa wanda ita wannan iskar oxygen ɗin ta ce iskar a muke shaƙa yau da kullum.


7. Bermuda Triangle: Wani yankine da ake siffanta shi da kusurwowi guda uku a cikin tekun atlantika´a kasar amurka, kuma yana nan ne a daura da kudancin gabar tekun, wanda ya hada da wani bangare daga tsibirin bahama da puerto-rico, da wani yanki na jihar florida, da kuma shi kansa tsibirin bamuda wanda wannan wuri ya samo sunansa daga gareshi.

Jiragen ruwa da kuma na sama da dama sun halaka sun bace bat sakamakon kokarin ratsawa ta wannan wuri na bamuda. Wata mujalla da ake kira da suna “national geographic magazine’’ ta bayyana wannan yanki na bamuda a matsayin alamari mafigirma kuma mafi rikitarwa da aka kasa fahimtarsa a wannan zamani

Akwai jirage da dama da suka halaka a wannan wu, misali a ranar 8 ga watan janairun 1962 wani jirgin sama da ake kira da suna aerial tanker kirar kb50 ya bace bat sakamakon bi ta sararin samaniyar wannan wuri, an kuma nemeshi ko sama ko kasa har yau baaji duriyarsaba.

Misali masana ilimin sinadarin da ke janyo abu daga sama zuwa kasa suna ganin cewa a wannan yankin na bamuda akwai wani mayan karfe na musamman wanda yake da karfin fizgo duk wani abu da ya yi kokarin ratsa wannan wuri komai girmansa kuwa. Kuma dazarar ya zukoshi tun da yake a tsakiyar teku ne to shi kenan shifa halaka ta gabbata a gareshi, kuma ba za’a taba jin duriyarsa ba .

Su kuwa masana ilimin falaki , suna ganin cewa, wannan wuri na bamuda da ke a cikin teku,wata kafa ce ta zuwa sauran duniyoyi, sabodahaka duk abin da ya bi ta cikinsa wato kamar dai ya tafi wata Duniyar ne ba ta Dan-adam ba.

Su kuma masana ilimin falsafa a nasu raayin, wurin na bamuda wata katafariyar fadar shedan ce, inda duk abin da yayi kokarin tsallakata zai halaka.

Wannan al’amari dai ba wai magana ce ta hadari ko tsautsayi ba, magana ce ta bacewa bat a nemi abu ko sama ko kasa a rasa, sabadahaka kenan batun sanin kididdigar yawan mutanen da suka halaka ko kuma yawan dukiyoyin da aka rasa abu ne mawuyaci.

Sai dai kawai maganar dai a nan itace cewar, wannan wuri da ake kira da suna Bamuda triangle gaskiya ne akwai shi, amma har yanzu Duniya bata tabbatar da ainihin ko menene a wannan wuriba.

Comments

1 comment
Post a Comment

Post a Comment