Min menu

Pages

Jerin Wasu Ƙasashen Duniya 6 da Rana Ba Ta Faɗuwa Na Tsawon Lokaci

 Jerin Wasu Ƙasashen Duniya 6 da Rana Ba Ta Faɗuwa Na Tsawon Lokaci

Akwai wasu kasashe shida a faɗin duniya da Allah ke ikonsa, inda rana ke shafe tsawon lokaci ba ta faɗi ba.


Kasar Sweden da Finland na daga cikin jerin waɗannan kasashe, inda kuma ake samun wasu lokuta da ake samun dare na tsawon lokaci.


Waɗannan ƙasashe na ganin iko na Ubangijin da ya halicci kowa, kuma a haka mutane ke rayuwa a wuraren


Sweden - Ƙasahen turawa, Finland da Sweden na daga cikin jerin ƙasashen duniya shida, waɗanda rana bata faɗuwa na tsawon wani lokaci.


Punch ta ruwaito cewa waɗannan kasashen na fuskantar zafin rana na tsawon watanni ba tare da ta faɗi ba kuma wasu na fuskantar duhun dare na yan kwanaki.


1. Sweden


Ƙasar Sweden dake yankin turawa, tana fuskantar rana ba tare da ta faɗuwa ba na tsawon watanni shida a kowace shekara.

Tun daga farkon watan Mayu, har zuwa ƙarshen watan Agusta, rana tana faɗuwa ne da tsakiyar dare kuma ta sake fitowa da ƙarfe 4:00 na asubahi.


2. Finland


A lokacin damina, a mafi yawancin yankuna ƙasar Finland rana bata faɗuwa kwata-kwata na tsawon kwanaki 73

Amma a lokacin hunturu ba'a ganin ko da ɗigon hasken rana a baki ɗaya sassan kasar.


3. Norway


Ana kwashe kwanaki 76 a ƙasar Norway ba tare da rana ta faɗi ba, kuma ana kiran ƙasar da ƙasar rana.

Tun daka watan Mayu zuwa ƙarshen watan Yuli, kasar na shan hasken rana ba tare da faɗuwa ba.


4. Nunavut, Canada


Birnin Nunavut dake arewa maso yammacin ƙasar Canada, na fama da hasken rana na tsawon watanni biyu ba tare duhun dare ya gitta ba.

Amma a lokacin damuna, birnin na fusakantar duhun dare na tsawon kwanaki 30.


5. Iceland


Bayan ƙaurin sunan da Iceland ta yi na ƙasar da babu sauro kwata-kwata. A lokacin sanyi ana dare ne kawai a ƙasar yayin da rana bata faɗuwa a watan Yuni.


6. Barrow, Alaska


Rana ba ta faɗuwa a wannan yankin tun daga ƙarshen watan Mayu har zuwa karshen daren watan Yuli.

Hakazalika daga farkon watan Nuwamba, rana bata fitowa sam har tsawon kwanaki 30 a jere, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Comments