Min menu

Pages

Shugabannin Afrika da aka ba damar mulki har abada a kasashensu.

 Shugabannin Afrika da aka ba damar mulki har abada a kasashensu.


Daga cikin shugabannin nahiyar Afrika da suka kai wannan matsayi ko dai ta hanyar ayyana kansu ko kuma majalisar kasarsu ta yi dokar ɗaga likafarsu zuwa matsayin sun haɗar da.


1. Idi Amin Dada - Uganda




  A 1966 aka nada shi a matsayin shugaban kwamandan sojin Turawan mulkin mallaka na Burtaniya

  Idi Amin Dada tsohon shugaban Uganda ne, an haife shi a garin Koboko da ke arewa maso gabashin kasar a 1925.

  Ya yi karatunsa a kasar kuma ya zama soja cikin dakarun mulkin mallakar Burtaniya a 1945 wadanda ake kira King's African Rifles (KAR), ya kure duk wani mataki da bakar fata ya taba kai wa a rundunar sojin.

A 1966 aka nada shi a matsayin shugaban kwamandan sojin Turawan mulkin mallaka na Burtaniya.

   Ya zama shugaban kasar a 1971 bayan hambarar da gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban kasar na farko Milton Obote. Ya shugabanci kasar na tsawon shekara takwas.

   A 1979 rikici ya sanya shi ya gudu ya bar Uganda inda ya samu mafaka a Saudiyya ya kuma mutu a can a 2003.

   Ya bai wa kansa matsayin (Field Marshal) wato na kasancewa kan shugabanci na har abada a 1975, wanda kuma shi ne makura a tsarin sojin kasa Uganda, matsayin mallakar tauraro biyar.

   Turawan yamma na yi ma shi kallon dan kama karya wanda kuma ya durkusan da tattalin arzikin kasar ta Uganda.


2. Mohamed Hussein Tantawi - Masar



  Ana yi wa Mohamed Hussein Tantawi kallon wani rumbun bayanan tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak.

  An haifi Mohamed Tantawi a yankin Nubian da ke tsakanin Masar da Sudan a 1935, bayan kammala karatunsa ya shiga aikin soji a 1956 a Masar.

  Ya zama shugaban kasar Masar bayan hambarar da Shugaba Mubarak, ranar 11 ga watan Fabirairun 2011 ya zama shugaba, kuma ya sauka 30 Yuni 2012.

Ya yi karatun digirinsa na biyu a kwalejin horas da soji inda ya karanci kimiyyar soji, ya samu cikakken horo kan harkokin soji da yaki.

   Sama da shekara 50 ya halarci manyan yake-yaken Masar cikin har da na shekarar 1967 da na 1973 a Gabas Ta Tsakiya, kuma dukkansu ya fuskanci Isra'ila ne, anan ne kuma ya samu matsayin (Field Marsha).

   A 1991, biyo bayan mamayar da Iraki ta yi wa Kuwait, ya kasance a bangaren dakarun hadin gwiwa a yakin Gulf na farko. Ya karbi kyautar girmamawa daga Masar da Kuwait da kuma Saudiyya.

   A dai cikin shekarar ne aka naɗa shi ministan harkokin tsaron Masar.



3. Bokassa - na Jamhuriyar Dimokradiyyar Afrika ta Tsakiya



   An haifi Bokassa a yankin Bobangui, da ke M'Baka na kauyen Lobaye, ranar 22 ga watan Fabirairu 1921.

   Ya yi makaranta a Brazzaville, ya so ya zama fasto amma daga baya iyayensa suka ba shi shawarar shiga cikin dakarun Turawan mulkin mallaka na Faransa.

  Bayan ya kammala karatunsa a 1939 ya shiga cikin tawagar dakarun ya zama soja 1941 kuma ya yi yaƙi karkashin tutar dakarun a yakin da aka yi da dakarun Nazi.

  A Janairun 1962 Bokassa ya bar tawagar dakarun faransa ya koma ta cikin dakarun Jamhuriyar Dimokradiyyar Afrika Ta Tsakiya a matsayin babban kwamandan bataliya.

  Ya zama shugaban kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Afrika ta Tsakiya tsakanin shekarar 1966 zuwa shekarar 1976 a matsayin shugaban soji.

Sannan ya kuma ayyana kansa a matsayin sarkin sarakunan Jamhuriyar Dimokradiyyar Afrika ta Tsakiya 1976 zuwa 1979 ya kuma sauya sunan kasar zuwa Central African Empire.

  Kasashen duniya sun yi ta sukarsa saboda zargin hannu da wajen yi wa wasu yara 'yan makaranta 100 kisan kiyashi, wannan ya janyo dakarun faransa suka koreshi daga kan mulki.

  Ya tsallaka Côte d'Ivoire gudun hijira daga baya ya kuma koma faransa.

  Daga bayana ya koma Jamhuriyar Dimokradiyyar Afrika ta Tsakiya 1980, tabbatar masa da laifin da ake zarginsa da shi, aka kuma yanke masa hukuncin daurin rai da rai.A 1993 ne aka sake shi bayan sassauta hukuncin da aka yanke masa, ya mutu a watan Nuwambar 1996 sakamakon ciwon zuciya.

   A shekarar 2003 aka yi masa gafara saboda bikin cikar kasar shekara 50 da 'yancin kai.

Comments