Min menu

Pages

Shugabanni 10 da suka fi kowa ilimi a Nahiyar Africa

 Shugabanni 10 da suka fi kowa ilimi a Nahiyar Africa


Haƙika zancen nan da Hausawa ke cewa: “Masu neman ilimi shugabanni ne,” ya tabbata a kawukan wadannan shugabanni, domin ba kawai mulki suka yi fice a kai ba, sun kuma zama gangaran a bangarorin ilimi daban-daban.

Wadannan shugabanni guda 9, ga su nan mun tsara su gwargwadon ilimin kowannensu.


1. Sarki Mohammed Na 4 Dan Kasar Moroko

Shi Mohammed BI ya zama Sarkin kasar Moroko daga mahaifinsa a shekarar 1999. Ya yi makarantar Firamarensa ne da Sakandarensa a Kwalejin Royal.

Ya samu shaidar digirinsa na farko ne a shekarar 1981, daga nan ya je Jami’ar Agdal inda ya yi wani digirin a bangaren shari’a. Ya yi Satifiket akan sha’anin ilimi a bangaren siyasa. Sannan ya yi diploma akan abin da ya shafi dokokin al’umma.

Sarki Mohammed ya yi digirin digirginsa ne wato PhD a turance a bangaren shari’a daga jami’ar Faransa ta Nice Sophia Antipolis.


2. Dakta Peter Mutharika Na Kasar Malawi



Dakta Peter Mutharika shi ne shugaban kasar Malawi. Ya yi digirinsa na farko ne a bangaren shari’a a Jami’ar London. Sannan ya yi digirinsa na biyu wato LL.M da kuma digirinsa na uku wato PhD duk a bangaren shari’a daga Jami’ar Yale.

Shi kwararre ne a bangaren sanin dokokin tsarin mulki da kuma tattalin arziki na duniya.


3. Alassane Kuattara Na Kasar Kwadebuwa



Alassane Dramane Ouattara shi ne shugaban kasar Kwadebuwa tun daga shekarar 2010 har zuwa yau. Kuattara ya samu digirinsa na farko ne daga Kwalejin Kimiyya ta Dredel wacce yanzu ta koma Jami’ar Dredel dake Philadelphia a Pennsylbania .

Daga nan ya yi digirinsa na biyu da na uku a bangaren tattalin arziki daga Jami’ar Pennsylbania dake kasar Amurka.


4. Dakta Mulatu Teshome Na Kasar Ethiopia

Dakta Malatu Teshome. Ya kasance shi ne shugaban kasar Ethiopia tun daga ranar 7 ga watan Oktoba 2013 har ya zuwa ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 2018.

Teshome ya yi karatunsa ne a kasar Sin. Inda ya samu digirinsa na farko a bangaren falsafar siyasar tattalin arziki, kuma yi digirin digirgir dinsa a sashen sanin dokokin duniya a Jami’ar Peking.


5. Dakta Ameenah Gurib Ta Kasar Mauritius

Sunanta Dakta Ameenah Gurib-Fakim, mace ta farko da aka zaba ta zama shugabar kasar Mauritius. Ta shiga Ofis ne a ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2015 a matsayin shugabar kasa ta 6 ta kasar Mauritius din har ya zuwa 23 ga watan Maris din shekarar 2018.

Bayan ta kammala Firamarenta a makarantar Saint-Patrice ta koma Mahébourg Loreto Conbent. Sai dai ta samu shaidar Satifiket din Sakandaren ta ne a makarantar Loreto Conbent Kuatre Bornes. Daga nan ta tafi kasar Ingila inda ta yi digirinta na farko a bangaren sanin sinadarai a Jami’ar Surrey a shekarar 1983

Ta yi digirinta na uku ne wato PhD duk a wannan fannin a Jami’ar Edeter.


6. Ibrahim Boubacar Keita Na Kasar Mali



Bayan mun baro kasar Mauritius, yanzu haka mun dira a kasar Mali. Ibrahim Boubacar Keita shi ne shugaban kasar Mali tun daga ranar 4 ga watan Satumban 2013.

Shugaban kasar yana da digiri na biyu guda biyu a bangarorin tarihi da kuma siyasa daga Jami’ar Lycée Janson-de-Sailly dake birnin Paris da kuma Lycée Askia-Mohamed dake birnin Bamako.

Sannan kuma yana da wadansu digirin a bangaren kimiyyar siyasa da kuma dokokin duniya a Jami’ar Dakar da kuma makarantar Institut d’Histoire des Relations Internationales Contemporaines.


7. Robert Mugabe Na Kasar Zimbabuwe

An yi masa shaidar cewa tabbas Robert Mugabe jajirtaccen shugaban ne. Duk da wannan shaidar ta zama shugaba, hakazalika mutum ne mai ilimi wanda ya tattara ilmummuka daban-daban a kirjinsa. Ya yi Firaministan kasar daga shekarar 1980 zuwa 1987. Daga nan ne ya zama shugaban kasar daga shekarar 1987 zuwa 2017.

Yana da digirinsa na farko a bangaren shari’a, da bangaren kimiyya, da bangaren ilimi da tarbiyya, da bangaren sha’anin mulki da kuma bangaren fasaha.

Sannan ya yi digiri na biyu a bangaren shari’a wato LL.M da kuma bangaren kimiyya.


8. Faure Gnassingbe Na Kasar Togo

Faure Gnassingbe na kasar Togo shi ne ya zama na takwas a jerin shugabannin da suka fi kowa ilimi a tsakanin shugabannin Afrika.

Ya kasance shugaban kasar tun daga shekarar 2005 zuwa yau. Shi da ne ga tsohon shugaban kasar wato Gnassingbe Eyadema.

Gnassingbe ya kammala Sakandarensa ne a Lome kafin ya je ya yi digirinsa a bangaren sha’anin kudin da ksuwanci a birnin Paris. Daga nan ne ya yi digirinsa na biyu a bangaren sha’anin kasuwanci a Jami’ar George Washington dake kasar Amurka. Har wala yau ya sake wata digirin na biyu a bangaren ilimin sanin kasuwanci. Sannan ya yi wata digirin a bangaren kasuwanci.


9. Ellen Johnson Sirleaf Ta Kasar Liberiya

Ellen Johnson Sirleaf, tsohuwar shugabar kasar Liberiya ta kasance ta tara a wannan jerin. Ita ce mace ta farko a kasar Liberiya da aka zaba ta zama shugabar kasa. Kuma rahotanni sun bayyana cewa; ita ce mace ta farko a nahiyar Afrika da ta zama shugabar kasa.

Ta zama shugabar kasa ne a shekarar 2006, wacce ita ce ta kasance shugaban kasar Liberiya ta 24. A shekarar 2011 aka sake zabenta ta zama shugabar kasa har ya zuwa shekarar 2018.

Ta yi karatunta ne a Kwalejin Afrika ta yamma wato ‘College of West Africa’ da kuma Kwalejin Kasuwanci ta Madison, daga nan ta shiga Makarantar Sanin Tattalin Arziki a Boulder dake Colorado a shekarar 1970.

A takaice dai tana da digiri a bangaren sanin sha’anin mulki, digiri na biyu guda a wannan fannin na sanin mulki. Digirinta na farko ta yi ne a bangaren tattalin arziki. Sannan tana da wata digirin a bangaren tattalin kudi.


10. Paul Biya Na Kamaru

Paul Biya dan siyasan Kamaru ne wanda yake shugaban kasar Kamaru tun ranar 6 ga Nuwamba 1982. Dan asalin Kudancin Kamaru ne, Biya ya tashi chanzari a matsayin shugaban ofis a karkashin Shugaba Ahmadou Ahidjo a shekarun 1960, yana aiki a matsayin Sakatare-janar na Shugaban kasa daga 1968 zuwa 1975 da kuma sannan a matsayin Firayim Ministan Kamaru daga 1975 zuwa 1982. 

Paul Biya yayi Diploma a Cibiyar Nazarin Harkokin Kasuwanci a Paris

Sannan ya sake yin wata Diploma a Institut des Hautes Etudes d'Outre-Mer, sannan yaje yayi Bachelor a Arts in Law and Science Science, Jami'ar Faransa.


A takaice, wadannan sune shugabanni 10 da suka fi kowa ilimi a tsakanin shugabannin kasashen Afrika. Wadansu daga cikinsu tuni suka zama tsoffin shugabannin kasa, a yayin da damarsu har yanzu sune suke jagorancin kasar ta su.

Comments