Min menu

Pages

Kasashe 20 a Duniya da Suke Fama da Rashin nagartattun Shugabanni

 Kasashe 20 a Duniya da Suke Fama da Rashin nagartattun Shugabanni



Wani rahoto da wata ƙungiya ta saki ya nuna jerin kasashen duniya mafi rashin shugabannin kwarai a duniya.

A rahoto da kungiyar CGGI ta saki, kasar Venezeula ce kasa ta karshe cikin masu shugabannin kwarai a duniya.

Kasar Zimbabwe ce ta biyu sannan kuma kasar Najeriya ta uku. Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Singapore, Chandler Good Government Index, CGGI ta bayyana jerin kasashen da suka fi shugabannin kwarai a fadin duniya.

Rahoton da aka saki ranar 26 ga Afrilu, ya bayyana cewa an yi amfani da yawan karɓar cin hanci da rashawa wajen nuna irin nagartan shugabannin kasa.

CGGI ta saki rahotonta a shafinta na Tuwita. Diraktan CGGI, Wu Wei Neng, ya ce mulki na kwarai ne abinda zai iya kawo wa kasa nasara.

An bada maki ga kowace kasa ne bisa abubuwa guda 7:

Nagartan shugabannin da hangen nesa, dokokin kwarai, ma’aikatu na kwarai, gaskiya da rashin cin amana, janyo hankalin masu sa hannun jari.

Sauran sune mutuncin kasar a idon duniya, da kuma taimakon marasa karfi da tayar da su daga makaskancin hali.


Ga jerin kasashen:

1. Kasar Venezuela

2. Kasar Zimbabwe

3. Kasar Najeriya

4. Kasar Mozambique

5. Kasar Mali

6. Kasar Iran

7. Kasar Madagascar

8. Kasar Lebanon

9. Kasar Burkina Faso

10. Kasar Zambiya

11. Kasar Aljeriya

12. Kasar Habasha (Ethiopia)

13. Kasar Nepal

14. Kasar Pakistan

14. Kasar Malawi

16. Kasar Nicaragua

17. Kasar Guatemala

18. Kasar Ecuador

19. Kasar Cambodia

20. Kasar Tajikistan

Comments