Min menu

Pages

Wani itace mai zubar da jini kamar dan Adam

 Wani itace mai zubar da jini kamar dan AdamAssalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu hakika muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu muna godiya sosai da sosai.


A yau cikin shirin namu muna tafe muku ne da photo tare da bayanin wani itace wanda idan aka sare shi yake zubar da jini tamkar jinin jikin bil'adama.


Bincike ya nuna wannan itacen yana cikin wasu kasashe ne dake nahiyar Africa irinsu Zambia Africa ta kudu Angola, Tanzania, Congo, da sauran wasu sassa na kasar Namibia da Zimbabwe.


Sannan akwai irin wadannan bishiyoyin a wasu sassa na nahiyar Turai.


Shidai wannan itacen ana kiransa ne da suna BLOOD WOOD wanda kai tsaye aka dangantashi da jini.


Duk lokacin da aka sari jikinsa to ruwan da yake zubarwa tamkar jinin Dan adam yake.Comments