Min menu

Pages

Dole maza su auri mata biyar ko su karasa rayuwarsu a gidan kurkuku

 An umarci maza su auri mata biyar ko su karasa rayuwarsu a gidan kurkuku a wannan kasar..Tuni gwamnatin kasar Swaziland ta bada umarnin duk wani na miji daya auri mata biyar ko kuma ya karasa sauran rayuwarsa a gidan kurkuku.


Wannan yana zuwa ne saboda tsananin yawan da mata sukai a kasar wanda yawansu ya nunka na maza da kaso mai tsoka wanda idan ba wannan dokar aka sanya ba wasu matan zasu gama rayuwarsu ne ba tare da sunyi aure ba.


Kasar Swaziland kasa ce dake nahiyar Africa wacce suke bin tsarin mulki sarakuna misali sarki shine yake kamar zama a matsayin shugaban kasa.


To sarki Mswati na uku shine yake kan ragamar mulkin a yanzu kuma shine ya yanke wannan hukuncin na tilastawa mazan dake kasar su auri mata har biyar.

Domin yace duk wata masifa da take afkuwa a kasa tana zuwa ne idan matan da suka balaga sukai yawa a kasa ba tare da sunyi aure ba.

Sarkin yayi alkawarin bayar da kudin aure ga duk mazan da za suyi auren, domin tallafawa.Comments