Min menu

Pages

Waye ya kashe Ahmadu Bello Sardauna

 Waye ya kashe Ahmadu Bello Sardauna?Abubuwa sun faru masu matukar sosa zuciyar duk wani dan arewa a shekarar 1966 wanda har yau har gobe muke ganin abin..


Wannan abin yana zuciyar duk wani dan arewa wanda baza su manta dashi ba saboda kashe wasu manya da akai kuma ginshikai masu son ci gaban yankin Arewa a shekarar 1966.


An kashe Sardauna mutum mai son ci gaban yankin Arewa, mutumin da yayi ta fadi tashi ganin yan arewa sun zamto zakaran gwajin dafi a kasar Nigeria.


Mutum mai jajircewa dan ganin arewa  da yan arewa sun dogara da kansu da karatun boko koma babu zasu tsaya da kafafunsu.


Amma makiya arewa suka shiga suka fita ganin sai sunga bayansa shida Abubakar Tafawa Balewa..


Ance wanda ya kashe Sardauna wani manjo ne na soja, kuma yana daga cikin wanda Sardauna ya amincewa sunansa Chukwuma Nzeogwu.


Daga karshe dai aka gano cewa turawa ne suka dauki nauyin kisan ta boyayyiyar hanya.


Har yanzu Arewa na kukan rashin SardaunaComments