Min menu

Pages

Wani mutum ya musulunta saboda kallon shirin izzar so

 Wani mutum ya musulunta saboda kallon shirin izzar soShirin izzar so yayi sanadiyyar musuluntar wani matashi.

                          Izzar so 

A yanzu ne mai daukar nauyin shirin film din izzar so series wato lawan Ahmad wanda aka fi sani da umar Hashim ya fitar da sanarwar hakan a shafinsa na Facebook.


Kamar yadda jarumin ya wallafa photonsa tare Dana saurayin daya musuluntar yace wannan saurayin ya taso ne tun daga wata jiha mai nisa yazo gare su domin ya musulunta.


Ya taso ne tun daga jihar Cross rivers, kuma yace sanadin kallon shirin izzar so ne yaji yana sha'awar shiga addinin musuluncin saboda yadda yaga ake koyarwa.


Yanzu dai ya karbi addinin musuluncin inda aka canja masa suna daga John zuwa Umar.


Shirin izzar so dai ya samu karbuwa gurin al'umma saboda yadda ake koyar da abubuwa masu kyau a cikin shirin da kuma nuna karfin addu'a da mahimmancin yin gaskiya.


Izzar so episode 75 original bakori tv


Kamar yadda ake fitar da sanarwa cewar shirin izzar so zai fito ne wannan lahadi din da karfe takwas kamar yadda umar Hashim din ya sanar

Comments